Chapter 154
Chapter 154
sanyi ya bude ya miqa mata,tana tsaka da sha ya nema gefanta ya zauna yana murza agogon hannunsa "Banajin tafiyar nan zata yiwu......" "......don Allah uncle" tayi saurin katsar numfashinsa,tunda taji zasuje ayi mata vaccination na tafiyarsu wadda duka duka saura kwanaki biyar ta matsu suje din,ido ya lumshe yana dariya "Bance wai an fasa ba,nima inason zuwa naga hajiyata,bazata yiwu ya mota ba,bari na duba mana rocket ko zamu samu koda evening flight ne" ido ta rufe tana dariya,kunya kuma tana kamata na yadda tayi saurin yanke masa hanzari "Kayi haquri uncle"daga kansa yayi daga danna wayar ya kalleta yana murmushi,bai taba zaton bada haquri abu bane mai sauqi wajen diya mace ga mijinta ba sai daya zauna da widad,kalmar haquri kalma ce mai matuqar tsada da wahalar furtawa a wajen hafsat,tsahon shekaru bakwai,adadin lokuttan da ta taba buda baki ta bashi haquri tsaf zai iya qidayesu da yatsun hannunsa. Kafin su fita daga gidan zuwa airport ta qarfafa jikinta,duk don wai ya sake yadda ba wani ciwo take ba,ya kuma janye maganarsa na suna sauka yau din gobe zai kaita a dubata. Sau uku tana kiransa wayarsa a kashe,ta qagu su iso tayi ido hudu da widad din kamar yadda ummanta tace ta fara tsaiwa ta tabbatar da gaske da cikin?,ta duba idan taga wani canji tattare da ita,idan akwai alamunsa to zasu bincika su dauki matakin da duk hafsat din taso. Tana parlor tana shayar da baby yusra,su nawwara sunata sabgarsu cikin falon,sassan dai kamar ko yaushe sauqi sai wajen Allah,duk da ta dauko diyar anty ummee ta tayata zama har zuwa sanda zatayi arba'in,to amma itama yarinyar aikij ya mata yawa,abinda taga zata iya shi takeyi. Ko kusa ko alama bataji alamun shigowarsu ba,don mota ya dauko daga airport,ba kamar yadda ya saba ba,idan flight zai biyo yana kiran umar yazo ya dauka motarsa dake nan ya daukoshi ya kawoshi gida. Yusra ta cire daga shayarwar da takeyi,idanunta a kansa sanda yaran suketa rige rigen isa wajenshi. Mummunan kishi ya kama zuciyarta,duk sanda zaizo mata weekend sai taga ya canza,sai taga ya qara fresh ya qara murmurewa fatarsa tayi wani lumaui,komai nasa fes kamar wanda akewa wankan inji. Qarasowa yayi ya duqa yana shirin karbar yusra,dai dai sanda take masa sannu da zuwa,ya amsa yana dan dauke numfashinsa hadi da daukan yarinyar yana kallonta,tausayinta yana cika zuciyarsa,ba alamun qamshi jikinta bare na mahaifiyarta,yadan ja kumatunta yana mata wasa duk da ba gane komai takeyi ba,yayin da hankalin hafsat ke kansa,tanason jin tare suka zo?. Amsarta ta fito kuwa sanda mimi ke tambayarsa ina anty widad?,yauma batazo ba?. Murmushi ya sake,qauna ce sosai da shaquwa me yawa tsakaninsu da widad din,tamkar ma itace ga haifeta ba hafsat din ba "Tazo,muje ku gaisa" sai ya sanyasu a gaba suka fice,suka bar hafsat da lissafin yadda zata shiga ta ganta din,don yarinyar ya canza hali,wani irin canji da tafi zaton akwai masu zugata na gasken gaske daga gefe,tasan tsaf daga halinta ba zasu hadu ba sai ranar da zata koma Kaduna. Ya sameta harta cire kayan jikinta,ta saka wata black rmless gown A shape,tabi lafiyayyar farar fatarta ta.kwanta,ya bita da kallo tsigar jikinsa na zubawa,yana jin wani abu mara dadi na masa yawo a rai,yasan yau da gobe duka zaiyi missing dinta,saidai yasan zasu hade a kano,kuma tabbas zaya fanshe kafin su tashi. Bakinta har kunne ta karba yusra tana mata wasa,ita da mimi da nawwara duka sun zagaye yarinyar,tana mata waqa suna mata amshi,sai ya koma gefe ya harde hannayensa yana kallonsu murmushi yana qwace masa,yana hasashen yaranta kamar haka. Daga kai tayi suka hada ido,sai ya kashe mata ido daya yana mata murmushi,ta maida masa martani,Allah ya zuba mata son yara,baisan wanne irin son yara gareta ba,abinda ko uwarsu data haifesu bata damu da yi musu ba amma ita saita bata lokaci tana wasa dasu hadi da kula dasu. Anan yabar mata duka yaran ya wuce sashensa, pampers din yusran da widad din taga ya cika da kashi ta cire mata cikin jin tausayin yarinyar "Tun dazu da take kuka na cewabmommy kashi tayi sai tace ba yanzu zata cire mata ba" duban mimi widad tayi cikin mamaki,itadai ta sani,yayyenta da matan gidansu duk sanda yaro yayi bayan gida cire masa shi sukeyi,takanji sunce yana cin jikin yaro sai wajen yayi ja ya zama ciwo. Wanka tayi mata da ruwa mai dumi sosai,ta shafeta da farar powder ta goyata ta fara gyaran sashennata,tana aikin yarannna biye da ita,yau daya nishadinsu ya canza,sashen ba aiki sosai don ba datti bane sai qura,nan da nan ta gama ta cikashi da wannan qamshin da ya zamewa gurin jiki. Ko kafin ta gama ma yarinyar tayi barci,saita kwantar da ita tayo wankan itama ta sauya kaya ta zura hijab ta tayar da sallah. Tana idarwa hafsat tana sallama,ta shigo idanunta akan widad din kamar zata cinyeta,bata lura ba don zuciyar a wanke take,ta gaidata ba yabo ba fallasa,ta amsa tana sake qare mata kallo. Tabbas tayi qiba,ta kuma yi fari sosai fiye da farinta nada,amma kuma sanda ta miqe zata dauko mata yusra dake bacci bataga tudun komai a tare da ita ba,wannan shi ya saka mata shakka a ranta,ta debi yaran suka baro sashen tana lalubar number ummanta. Bayani tayi mata na canjin data gani din daga wajenta,sannan ta dora mata da "ta danyi watanni umma da wannan canjin,idan ciki ne ya kamata zuwa yanzu ya fito,amma banga alamar komai tare da ita ba" shuru ta danyi tana nazari,ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ba'a nan take ba hafsatu wai an dannewa bodari kai,zanyi magana dashi,kome meye yake akwai su basa rasa ganinsa". Yana zaune daga bakin gadonsa,hannunsa dauke da tab,yana bibiyar statement na wasu masu laifi dake tsare a hannunsu,hafsat na daga gefe tana lallaba yusra tayi bacci fuskarta aa hade ranta a bace,tunda abbas din ya gaya mata kafin ta iso gadon tayi wanka take kumbure kumbure harta gama ta maida kayan jikinta ta dawo gadon,yayi haka na bawai don yana da bauqatarta ba,kawai ya fuskanci idan ba wanna titsiyen ya fara yi mata ba haka zata ci gaba da tafiya,sau daya ya kalleta bai sake dubanta ba,baisan me yasa har abada take sha'awa shigo masa bedroom da kayan data wuni dasu cikin gida ba,baisan sau nawa zai kwatanta mata bayason hakan ba,a yanzun da yake ganin sauyi daga wajen widad,sai abun ya daina bata ransa,tunda at least yana samun sassauci idan ita din taqiyi masa yadda yakeso,sai mamaki kawai da take bashi,sau tari tafi ganewa ta kwana da tufafinta,atamfa ko shaddar da tasha kwaramniyar yini guda da ita. Dakin shuru kamar ba kowa har ya gama aikinsa,koda ba aikin yake ba haka zaman yake dama,ita bata iya hira da miji ba,shi kuma dama tun asali miskili ne,yayin da take kallon miskilancinsa a matsayin zallar wulaqanci ne kawai (bata iya tsaiwa ta karanci ya yake). Tab din ya ajjiye a bedside drawer yana jan duvet dinsa zuwa qugunsa yana kallonta "Kiyi qoqari gobe da sassafe ki rubuta duk abinda kuke da buqata na kamar wata biyu haka,idan Allah ya kaimu ranar alhamis zamu wuce hajji ni da widad". Kamar wadda wuta taja ta kalleshi da sauri "Kai da wa?" Ta sake tambayarsa ba tare data bi takan sauran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155