Chapter 155
Chapter 155
bayanansa na baya ba,sunan daya fada sai taji kunnenta kamar baiji mata dai dai ba "Widad" ya sake fada yana kallonta hankalinsa kwance idonsa yana dan lumshewa saboda baccin daya fara ji. Cikin zafin nama ta miqe ta zauna sosai, kaman zata bige yarinyar saboda yadda ta tashin da sauri "Kasan me kake cewa abbas?,da widad zaka tafi hajji?" Dubanta yayi "Me na fada da yake alamta ba cikin hayyacina nake ba?" Yadda yayi maganar cikin bagararwa kamar ba wani mummunan abu ya aikata mata ba,ta tsareshi da ido,wani yayyafin zafi yana sauka daga zuciyarta yana ratsa kowanne sashe na jikinta,tafasa sosai zuciyarta ta dinga yi,ta rasa wacce kalma ce ta dace dashi,saita kuka kawai.ya balle mata,ta miqe tana sauka daga kan gadon cikin hargagi masifa da daga murya ta fara sake masa maganganu marasa dadi,ya rufe ido yana jinta har zuwa sanda tace "Kuma duk munafukan da suke sake shirya wannan abun Allah ya tsine musu albarka idan basu fasa ba,ni dasu shege ka fasa" Wata gigiyacciyar tsawa ya daka mata,yana dubanta da idanunsa da suka fito waje "Shirmenki ya isheni haka,fita ki bani waje shashasha mara hankali,a gabana zaki tsaya kina furta tsinuwa munafukai da sauran shirmenki!,zaki fita ko sai na baki mamaki?" Hannu tasa tana son dauke yusra daga kan gadon,tsananin bacin rai yasa ya janye yarinyar gefe,saita koma ta tsaya tana cewa "Mamaki kuma na nawa?,aika gama bani mamaki,wallahi tallahi inda nasan haka kake da bazan taba aurenka ba,amma kaje na barka da Allah" ta juya da gudu tana kuka da qaqqarfan sauti ta fice a dakin. Hannunsa gaba daya qaiqayi yake,tabbas inda wani ne a waje yayi masa hakan yau sai ya gane shayi ruwa ne,bayason shaidan ya dinga tunzarashi ta sanadinta ya zama madoki,sai ya dinga ambatar Hasbunallahu wani'imal wakil. *********Karfe goma na safiya ta gama shiryawa,tun jiya cikin zumudi ta kwana,tayi zaune a parlor tana jiransa. Da sallama ya shigo falon,muryarsa tayi laushi sosai saboda baccin da bai samu ba isashe daren jiya,ya zama wani so cool yayi kyau cikin shigar qananun kayan da ba kasafai ya fiya sanyasu ba,yau din yayi amfani da sun glasses wanda zai hanaka gane ainihin qwayar idanunsa,sai ya qara masa wani mugu mugun kyau,har widad ta kasa dauke dubanta daga kansa. Duk da yadda ya sakaye qwayar idanunsa amma hakan bai hanata ganin canzawar mood dinsa ba "Oga zumudi..... let's go,banaso rana tayi mana sosai,inason na dawo gida na huta"ya fada yana duba agogon hannunsa. Tare suka jero zuwa harabar gidan yana riqe ds hand bag dinta tana gyara rolling na mayafinta tana masa shagwabar don Allah idan anzo yin allurar ya tsaya a wajen. Murmushi ya sake,ko yaushe tabararta na nasarar korar bacin rai ko damuwarsa,wannan ya sanya koda daga office wani abu ya bata ransa,tattara komai yake ya dawo gida,yana da yaqinin zai samu magani sa sassauci,koda batasan me yake damunsa din ba,koda batayi komai da nufin korar bacin ransa ba. Da kansa ya bude mata seat din motar ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata rigarta data fito sannan ya miqa mata hand bag dinta. Hadawa tayi da hannunsa ta riqe tana kallon qwayar idanunsa "Me?" Ya tambayeta ganin yadda ta bata fuska "Smile mana uncle,kayi kyau yau,amma kaqi kayimin dariya.....haba mana uncle" ya qarasa fada a shagwabe. Don dole bai shirya ba siririn murmushi ya kubce masa,ya duqa a tausashe yayi kissing goshinta sannan ya zagaya ya tayar da motar. Suman zaune hafsat dake kallonsu ta dakin solar dinsu dake daura da wajen tayi,taji jiri kamar yana dibanta,har sai data samu waje ta zauna ta wucin gadi,kafin kuma kuma ya qwace mata,ta jima zaune a wajen tana kukan,har sai dataji shigowar sale sannan ta miqe tana barin wajen don kada ya sameta a haka raini ya shiga tsakani,saidai tana jin zuciyarta ta tsike gaba daya,zuwa yanzun komai ta fanjama fanjam,don haka wayarta kawai ta dauka ta fara neman number ummanta ba tare data damu da kukan da yusra ke tsalawa ba, wadda ta tashi daga bacci tun dazun taji ba'a Kula da ita ba. Idanunta fal tsoro,ta waiwaya tana dubansa sanda zata shiga dakin da ake bada rigakafin tana kallonsa "Please uncle,don Allah ka rakani" "Muje" ya fada yana maida wayarsa aljihun wandonsa suka shiga dakin a tare. Yadda taga suna gaisawa da likitar ya tabbatar mata akwai sabo tsakaninsu,tadan kalleshi,abbas din badai miskilanci ba,ya sansu amma ya maze mata,suka hada ido ta masa sing na zan rama,ya dage mata girarsa daya kawai. Fitsarinta suka fara buqata,tayi ta kawo mata aka bada gwaji. Gyara zaman glass din fuskarta likitar tayi sannan ta dago kai tana duban abbas din "Sir,bakasan madam nada juna biyu bane?" Sosai ya kalli likitan,sai ya zare gilashin idanunsa "Juna biyu?,Kina nufin,she's pregnant?" "Yes sir.....alamu ma sun nuna kamar yafi wata biyu" "Ya salam ya Allah"ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki,kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare daya samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad. *H A F S A T* Kamar zata zauce sanda taketa kiran ummanta ba tare data daga ba,muryar umman kawai takeson ji ta isar mata da saqon abubuwan da takeso a gabatar mata akan widad din,tana jin idan bata d'ai d'aita rayuwar yarinyar,ta gigita mata rayuwa ba tabbas mata ta rako duniya,indai bata dauki mataki mafi muni a kanta ba bata cika hafsatu ba,yarinyar tayi mata abubuwa masu.muni dake da yawan gaske,ba zata yaba qyaleta ba itama,ta rabata da abu mafi soyuwa a wajenta,halittar da duk duniya ba wadda take qauna sama da ita ABBAS dinta. Sai data yi mata kira biyar a jere,ana shidan ta dauka,kafin hafsat din tace komai ta rigata "Yauwa,nima ke naketa nema ai,ina hanyar dawowa daga gun aiki ne......,akwai gagarumar matsala hafsatu,akwai matsala" kalmomin umman nata da kuma tashin hankalin dake cikin nata kwanyar suka hadu suka kusa fasa mata kwanya,saita sulale ta zauna sosai a wajen tana jiran jin gagarumar matsalar dake tunkarosu din. *A L H A M D U L I L L A H* *_Masu karatu..... bakuji komai ba,baku karanta komai ba,kawai abinda zance daku shine......kuyi jumirin bibiyata,muje zuwa bayan hutun azumi,in sha Allah ina tafe da kashi na biyu na labarin A RUBUCE TAKE k'addarata,nima ba haka naso ba,amma yanayin yadda labarin ya dauko tunda farko,bazai taba qayatarwa ya bada ma'ana ba sai an cimma gacinsa,zanyi qoqari da ikon Alalh bayan sallar pages din sunfi wadan nan da muka gama tsaho in sha Alllah,fata na Allah ya bamu aron rai da lpy_* ina muku fatan ALKHAIRI AREWABOOKS FOLLOWERS dina,wadanda baku gajiya da bibiyata, alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke,ayi ibada da bukukuwan sallah lafiya,na barku lafiya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155