Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,313 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a dadi ba,wadanda suka jima suna addu'ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi. Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa. Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan 'yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa'a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi. ************ Daga can tsakiyar 'yan jaridar dake dauke da nau'ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din 'yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa "Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed". Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar "Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al'amari?,don dama jama'a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?" Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama'ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa "Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami'an tsaro musamman na 'yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu'a,fatan nasara" ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi. Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu. Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin. Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito. Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar "Kuna lafiya keda yaran?" Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi "Lafiya qalau muke" ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne "Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours" "Tooo....basai Friday ko Saturday ba?" Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba? "Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan" "Okay to,a taho mana da tsaraba" "Yayi.....me zan samu?" Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba "Kamar me kenan?" Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa. "In so samu ne tuwo nakeso" tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba "Xan qoqarta" ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba "Alright,saina qaraso" ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba. Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha'i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida. Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala'alla ma idan ka taki mummunar sa'a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa hancinka. Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta. Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa. Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi'un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko. "Muje ku rakani na shirya" ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara "Agwagwa sarkin wanka" tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});