Chapter 109
Chapter 109
zauna a wajen. "Kici gaba da kukan,karki bude baki ki fadi abinda ya kawoki,mahmudu kawai nake jira ya dawo,ai jibi yacemin zai dawo,yana hanya" cewar ummu bayan tayi qwafa,da alama ranta ya baci wannan karon akan widad din,a tausashe anty madina tace "A'ah,ai baza'ayi haka ba,ki bita a hankali ummu don Allah" "Yo madina meye ban mata ba?,indai ba so take na tsugunna tahau gadon bayana kuma na goyata ba,shine kawai abinda ya rage". A nan suka sanyata gaba da tambaya harda latifa amma ta kasa cewa komai,har ummu ta qulu ta tashi ta barsu,daga baya suma hakanan kowa ya haqura ya qyaleta. A ranar duk wanda ya shigo gaida ummun cikin yaranta maza kawunnan widad din sai ya kirata ya tambayeta,amma ta kasa cewa komai sai kuka,haka washegari akayita fama taqi magana,tace duka su qyaleta, mahmudu ne dai dai da ita,a goben kuma ko jibi zai dawo,abinda ya sake ruda cikin widad din,amma batajin zata iya ce musu ga dalili. Yaran gidan nata shigowa murnar zuwanta amma ta kasa sakewa,haka su Aafiya,saidai suyita hirarsu tana kallonsu,don ita a cikin damuwa take,tana tsoron gamuwarta da babanta,amma kuma tayaya zatace musu ga abinda yayi mata daya sanyata guduwa?. Abbas kuwa umnu ce tasa muhsin ya gaya masa basai yazo ba,yayi zamansa,abinda ya bashi mamaki yadda yakejin damuwa sosai a ransa,har ya taba kuzarinsa,ya kira number dinta kuma sau babu adadi amma kullum wayartata a kashe take,inda don ta tashi ce da tuni ya tsufa a kano,kwana ukun kacal amma yana jin kamar wasu kwanaki ne masu dimbin yawa,hafsat ta lura da hakan,duk da kusan ba wani sabgar juna suke shiga ba,ta kuma ji qishi qishin zancan tafiyar widad din kano,duk da bata da tabbacin meye ya kaita,amma ko babu komai taji dadin hakan har qasan ranta,tunda dai tasan ba lafiya bace ta kawo hakan,fatanta ma ta tafi kenan,kada ta sake dawowa har abada. Abu daya ne ya tsaye mata a rai,damuwar data fuskanci abbas din kamar ya shiga,ta rasa gane ma'anar hakan,ya fara son yarinyar kenan?, tambayar data yiwa kanta kenan,sai kuma ta qaryata kanta da kanta,ta yaya abbas din zai fara son diyar cikinsa?,banda kyau babu wani abu data ga yarinyar tana dashi,samun kanta tayi da duqufa addu'ar kada Allah ya bata ikon dawowa. **********Dukkaninsu suna falon ummu,mahaifinta da ya kasance babba da kuma qannensa gaba daya,ummu da widad na gefe,yayin da widad din tayi kamar ta shige cikin ummun "Tunda taqi cewa komai yaaya,me zai hana a sake kiran abbas din aji" girgiza kai alhaji mahmud mahaifin widad yayi cikin takaici "Ya riga yace min babu komai,kuma tunda yace din babu,ita dai tana kwaso wadan nan siraran qafafuwan nata tazo,ita zata bude baki tayi mana bayani ko na tashi na babballata a wajen nan na zubar" ya fada cikin tsananin fushin da tun dazu idanun ummu yasa yake cinyewa. Duka kallo sai ya koma kanta,cikin hargagi kamar zai kai mata duka yace "Zaki bude baki kiyi magana ko saikin daku?" Kamar an rufto mata duniya haka taji,ga wani mugun tsoron yadda abban nata ya juye da yake ratsata,tayi qas da kanta tana hawaye, abinda ya tunzura alhj mahmud,ba wanda ya ankara sai gani sukayi ya isa kanta da wayar tv daya ciro ya fara sauke mata ita. Kuka ta saki sosai,don zata iya cewa wannan shine karon farko da aka taba mata irin wannan dukan kaf rayuwarta,kafin a samu a qwaceta kuwa ta daku yadda ya kamata,latifa ta karbota tana boyeta cikin hijabinta ta fice da ita daga sassan ummun cikin jimami da alhini. Kai tsaye sassan anty madina tayi da ita,tana kwance a falo ta miqe tana salati "Dukanta dama yaaya yakeyi dana jiyo muryarta daga nan?" Anty madina ta fada kamar zatayi kuka "Wallahi,taqi ta fadi komai ne,shi kuma ransa ya baci" rungumeta anty madina tayi tana lallashinta "Inda kin fada widad ai magani za'a yi miki na koma meye da yake damunki" a nan hannunta latifa ta barta "Kada kice musu tana wajena please" anty madina tace da latifa ta juya ta fice,ita kuma ta jata zuwa bedroom dinta. Shuru ne ya ratsa falon bayan fita da widad din,zuciyar ummu duka ba dadi,dukan da mahmud yayi mata saita dinga jin kamar ita aka daka,amma kuma babu wani sauran abinda za'a yiwa widad din "Inajin ruqiyya zan sanya azo gida ayi mata" ummu ta fada cikin karyewar murya,kai kawu maisara ya gyada "Eh to,ya kamata a bincika ta wannan fannin ma,saboda suna iya sakata yin hakan,kuma ba kasafai hankali yake kaiwa can din ba,sai abu ya ta'azzara sannan ba fata ake ba" Miqewa abban yayi "Ai magana ta qare,gobe in sha Allah zanzo na dauketa da kaina muje,idanma sune sayi bayani" "Da kanka yaaya,ka bari wasu cikinmu su kaita" "Gwara ayi komai a gabana sa'idu don qaniyarta" har dariya taso subucewa ummu,mahmud din badai zafi ba,duk cikin yaranta ya fisu zafi,musamman al'amarin aure,baya wasa dashi. A hankali anty madeena ta turo qofar dakin "Kinyi bacci ne widad?" Widad dake zaune qasan carfet tana duba wasu litattafai data gani a dakin anty madinan ta amsa "Ban kwanta ba maman walidi" "Au na dauka mai gidan ya koya miki baccin wuri" ta fada tana duban fuskarta "Uhmmm" kawai ta fada tana maida kallonta ga littafin,maganar da anty madinan tayi saita tuna da abbas din,yana da kirki matuqa,yana da tausayi,tanajin dadin hira dashi amma duka ya bata wannan ta sanadin abinda yayi mata. Kaya ta zuba cikin cupboard sannan ta dawo gefen widad din ta zauna tana kallonta "Ki shirya gobe inji yaaya abba(haka matan gidan suke kiran babanta),gobe da safe zaku gidan mai ruqiyyar cire aljanu" a tsorace ta kalli anty madina idanunta a waje "Aljanu kuma?" Kai ta gyada cikin nuna halin ko in kula "Eh,haka abbansu walid ya gaya min" tuni hawaye suka cika idanun widad,ta narke sosai tana kallon antyn "Don Allah anty kice kada su kaini wallahi ni ba aljanu bane dani" "To menene widad?,tundi kinqi gayawa kowa aka sani ko sune?,ai gwara aje can din,qila su zasuyi magana" yadda taga ta rude tana roqonta taji a ranta zasu samu bakin,sai ta gyara zamanta tana dubanta "Kinga daga ni sai ke,ki gayamin me yasa kika taho kinji" "Ni bana sonshi anty madina" baki anty madinan ta riqe tana kallonta cikin mamaki,lallai wani halin sai widad din,amma a yadda ta fadi maganar ta fuskanci akwai wani abu,don haka ta hadiye mamakinta tace da ita "Bakya sonshi?,to me yasa bakya sonshi?" "Dan iska ne" ta amsa mata kai tsaye hawaye na sauka a idonta. Dariya ce taso qwacewa anty madeena,to amma tanaso su qarqare qarshen zancan "Dan iska kamar yaya weedad?,me yayi miki na iskancin?" Kallon anty madeena tayi,idanunta kamar zasu fado,kunya da nauyinta takeji,amma.indai bataso a kaita wajen mai aljannu dole tayi bayani "Tattabani yakeyi" ta qarasa fada muryarta tana rawa. Zuwa wannan gabar dole dariya ta kufcewa anty madina,yayin da sautin dariyar ya sanya widad cikin rudu,ta dauka zataga ta saki salati tana tafa hannaye,kota rufeta da fada ko da duka ma akan ta bari ana tabata din,sai kawai taga tana dariya. Kusan minti biyu sannan anty madeena tayi shuru tana nazari,ba shakka kuskure nasu ne,duk yadda akayi ummu bata zaunar da widad ta gaya mata meye gundarin aure ba,suma kuma bata jin wata a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155