Chapter 11
Chapter 11
rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru. Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama "Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?" Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta "Bari kawai hauwa'u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi" "Wa fa?" Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece "Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun" baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen "Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba'a yi wasa ba gaba sai abinda tace za'a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta" fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan "Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan" "To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba" shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba. A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai "Banason wannan maganar,ku qyaleni haka" yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar. Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma'aruf,ma'aruf dai,ma'aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma'aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba "Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma'aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma'aruf,jika ne shi cikin gidan,d'an mace ne)tamkar 'ya take a waje na". Ci gaba tayi da sabgoginta abinta,ta.maida kanta ga islamiyyar da take zuwa,don tunda aka koma hutu boko bata koma ba,alhaji yace ya isa hakanan,su maida hankalinsu ga islamiyya,ita dasu Aafiya,yayin da zancan bada ita ga ma'aruf ya fara yawo cikin gidan. Zancan ya zowa anty madina ta bakin mijinta uncle mulhim,ta jinjina lamarin sosai "Tirqashi" ta fadi,saboda tasan irin rashin jituwar dake tsakaninsu,duk sanda widad ta shigo tana binta da kallo yadda take sabgoginta da alama batasan abinda yake faruwa ba,tana tausayinta itama,tana yarinyarta amma sai abubuwa ke zuwar mata kamar wata babba?. Bata tashi sani ba sai wata rana suna dawowa daga islamiyya,a hanyarsu ta zuwa gida sun biyo ta wani layi,tun daga nesa suka hangi ma'aruf din yana tahowa shi da wani abokinsa,kunnensa maqale da earpiece suna hira kadan kadan da abokin nasa,kafin su qaraso Aafiya tasa hannu tadan bugi widad,wai tanason mata nuni dashi,saidai ko daya ita widad din bata ma fahimci me take nufi ba har suka qaraso dab dasu. Aafiya ce ta gaisheshi tana rusunawa,ya amsa mata suka wuce,widad kam da idanu ta bisu har suka wuce din,sai taja tsaki "Yanzun ya kusa zama angonki ma ba zaku fara magana ba widad?" Wani kallo tayi mata cikin quruciya da sakalci "Waye angon nawa?,ni ba wanda zan aura na gaya miki ina wajen ummu na,tare zamuyita zama" "Tabdijan,ni kuwa ana cewa aure za'a yimin zan yarda,bakiga kayan lefen da aka kawowa su anty ramziyya ba?,ga kayan girki da gadajen da aka siya musu masu yawa fa,ke don har yanzu bakije gidajensu ba,baki gani ba gwanin sha'awa,su dafa abinda sukeso,suyi kwanxiyarsu a gadonsu,ba duka ba aike ba fada,ke.....hmmmmm" Aafiya ta fada da alama abun yana burgeta,fuskar widad ta dan sauya zuwa fara'a "Su ai sun girmemu,ko auren za'ayi mana ba za'a yi mana irin nasu ba" kama baki Aafiya tayi tana fidda ido gami da kallonta "Inji wa?,wallahi momma tace qila ma mu samu abinda yafi nasu" "Allah?" "Wallahi" sai widad din tayi shuru tana jinjina kai,hadi da tuna yawan kayan da aka fitarwa kowacce cikinsu ramziyya daga gidan aka sa amota zuwa jeren gidanta. Sam ta manta ma da wani zancan ma'aruf,har suka isa gida suna zancan kayan auren,a harabar gidan suka rabu kowa ya shige sassansu. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 07 Bata fahimci zancan da gasken gaske bane sai da ummu ta fara hadata da walid qaramin dan anty madina yana rakata kaiwa ma'aruf din abincinsa,ta maida wannan aikin na kullum kullum a kanta,a nan ne hankalinta ya fara tashi,duk a qoqarin ummu na kawo kusanci da fahimtar juna a tsakaninsu. Tun ranar farko kamar tasan manufar yin hakan bata shiga dakin ba,daga bakin qofa ta tura masa ta juyo tayi tafiyarta,hakance taci gaba da kasancewa,duk sanda aka aiketan turawa take daga qofa ta wuce abinta sassan anty madina ko sassan wani daga cikin kawunnanta. *_RABON ZA'AYI_* Sun tafi tiryan tiryan da walid kai abincin,tana ta qunci da dacin rai,amma ba zata iya qin zuwa ba,har sun kusa da qofar dakin taji akwai alamun baqo,sai ta koma da baya tana duban walid "Muje na aje masa akan motarsa,yazo ya dauka" yaron yana biye da ita har gaban motar ma'aruf,ta dora masa abincin sannan suka koma sassan ummu,ta fito ne suna kallon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155