Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 152

Chapter 152

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,310 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sanda ta karba saqon ta hannun sale,ya rasa wa zai bawa aiken kudin amfanin gidanta sai salen?,bata sake shiga rudu ba sai dataga kowanne kudi ya fadi na meye,babu ko qarin sile akan abinda ya saba bata,gashi buqatar kudin take da gaske saboda fara adashin asara data yi,ko cikin satin ummanta tace lallai lallai ta tanadi kudi,saboda ba zasu taba bari sakaci ya shigo cikin aikin da aka fara ba,wannan ya sanya ta sake qullatar widad din qwarai,a duniya idan aka bata bindiga akace ta kashe mutum daya widad din zata fara harbewa. Yadda ya dauke mata wuta abin ya fara damunta,gashi tana fuskantar EDD dinta yana sake matsowa,wata zuciyar tana ta kirashi wata tana ta shareshi,a haka kwanakin suka fara tafiya, dole daga bisani ta karya billent ta kirashi,ta kuma maida komai ba komai ba,don lallai tana buqatar kudi. *B a y a n wa t a u k u* Bayan watanni uku hafsat din ta sauka,ta sake samun baby girl,zagayowar kwanaki hudu abbas ya dauki excuse don zuwa ganin baby,dole widad ta soma shirin binsa itama,don rabonta da bauchi tun wancan lokacin da suka samu sabani da hafsat,duk sanda zaije weekend tabar binsa,saidai yaje yayi kwanaki biyu ya dawo Kaduna,hakan yafi mata kwanciyar hankali,har ya zamana koda wasa batason taji ya ambaci xuwa bauchi da ita,yanzu zataji hankalinta ya tashi. Ta shirya tsaf tayi sabbin dinkunanta,gyaran gashi zuwa lalle suka wuce bauchi,ranar ta shiga sassan hafsat din,wanda rabonta dashi har ta manta. Ba wani mutane bane sosai, kasancewar ita din dama bata mutane bace,mai zuwa mata sha'ani sai wanda ya dubi Allah,anty ummee ce sai wasu baqi mata biyu sai 'yar yayarta data dauko saboda aikace aikacen gidan,sai hajiya habiba. Ciki ciki hafsat din ta amsa mata barkan data mata,itama sai bata saka kanta can ba,ta zauna daga hannun kujera,anty ummee ta miqa mata baby da aka gama yiwa wanka tana qarewa widad din kallo tsafff tana kaduwa da yadda taga ta sauya,ta karbeta tana jin sha'awar yarinyar har cikin zuciyarta,kasancewarta mai son yara sosai. "Uhmmm.....ko a bar miki ita ne?,naga kin kasa daina kallonta" hajiya habiba ta fada tana wani munafukin murmushi tana kallon widad,sai ta saki murmushi kafin tace komai hafsat ta rigata,taja wani mugun tsaki tana gyara zamanta "Ki daina irin wannan wasan hajiya habiba......haihuwa wasa ce da zaka dauki yaro danka ka baiwa yaro,wanda ko ciwon kansa bai sani ba?,tab..... garinsu da nisa ai,idan fitsari banza ne kaza tayi mana" tsaf ya fahimci abinda hafsat din take nufi,don haka ta miqe tsam ta miqawa anty ummee babyn tana cewa "Allah ya rayata" ta fice a nutse a falon ta wuce sassanta,don saukarsu kenan ta fara shigowa nan din. Tare hajiya habiba da anty ummee suka dauke kai daga kallon widad bayan ta bace musu,suka maida kan hafsat data fara qananun motoci tana sakin tsaki kamar ta tsinke harshenta "Banso kika sanya baki ba,kallon me juna biyu nakewa yarinyar,naso na bugar mana cikinta muji akwai ko babu" hajiya habiba ta fada tana duban hafsat "Ai banza ce,nima kallon da nakeyi yarinyar kenan tunda ta shigo,kamar me yaron ciki,canzawar tayi yawa,ni tsorata ma nayi dana ganta wallahi,ta zama wata babbar mace?" Anty ummee ta fadi tana kama bakinta. "Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe,ni kuwa ina me zan zauna na barta tayi ciki?,haba don Allah,bazai yiwu ba" hafsat ta fada tana girgiza kai,cikin zuciyarta tana jin wani irin zafi kamar ma ance cikinne,tana qiyasta yadda zata cakuda 'ya'yanta da 'ya'yan wata matar?,ba zaiyuwu ba,ba zata iya ba,barin widad din ta samu ciki harta haihu shine babban kuskuren da zata tafka "Idan ba mataki kika dauka ba sanda zai narka mata cikin sani kikayi?,kina nan kina bacci saidai ki tashi ki ganshi" hajiya habiba ta fada tana miqewa tsaye gami da daukar jakarta "Bafa wannan maganar hajiya,matakin nasa aka dauka,shi yasa nake cika miki baki" "To yanzu naji magana.....hmmm aikin hadu da alaqaqai ciwon zamani mai wuyar magani" "Ko tunata banason yi wallahi hajiya,ban taba kawowa yarinyar nan zata shiga rayuwata tayimin karen tsaye har haka ba" hafsat din ta fada yana sauke idanunta a sassan widad din tana jin ranta yana mata ciwo. Duk da jego take amma hakan bai sanyata ta barwa widad din kwananta ba,haka take diban jiki tabar masu tayata zama ta wuce sassansa ta kwana,ko daya widad din bata bari taga damuwarta ba,saita shiga sabgar gabanta kawai. Da kansa yace me take buqata na taron suna,tace zata kirasa idan ya fita,saita dauki waya sukayi magana da anty madina "Kiyi komai naki ta yadda ba ruwanki da abincin taronta,wanda ya shigo miki ki bashi,wanda ma baizo na ya hutasheki" da suka gama wayan saita kira hajjaa ita kuma ta gaya mata yadda suke komai na taron suna,ta yiwa abbas din waya ta gaya masa,ya ajjiye mata komai,da taimakon hajja takai aikin abincinta,masa da sinasir sai soyayyiyar shinkafa (fried rice). Ana gobe suna ta yiwa uncle muhsin waya ya bar nujood tazo suka kwana tare,washegari aka tashi da suna. Kwalliya ta dinga yi sosai,tana canza shiga cikin kayan da abbas din ya dinka musu,duk da na hafsat din ya dara nata,da kadan da kadan saiga mutane sun cika sashen nata, don duk wanda ya shigo din ga abinci nan zaici ya qoshi,sashen mai jego kuwa babu bayani,don kudinta ta adana,ta sada mutane da wata irin jallop din shinkafa data hadu da taqadiriyar dahuwa mara tsaro,dukka lemon roban da yasa aka jibge ta debesu,ta musanya da zobo dan dauri. Daga qarshe dai sassan widad sai ya zamana kaman a nan akayi haihuwar,duk wanda ya shigo din kuwa saiya qoshi da abinci me kyau,hafsat na daga sassanta amma labarin abinda ke faruwa a sassan widad din tuni yaje mata,ta cika tayi fam,musamman matan abokan abbas din da suka yada zango a can bayan sun mata barka,don ba wadda ta zauna a cikinsu,saboda ba wani kyakkyawan mu'amala bace tsakaninsu,tsananin kirkin abbas din ne ma ya sanya suka kasa qin zuwa,dama kuma idan ka gansu a gidan to saifa irin hakan ta kama. Kasa zaune bare tsaye hafsat din tayi,da yammar ta canza kaya na biyu shima bisa takurawar anty ummee "Kiyita zama,suttura iya sutura an miki amma kin jibgesu,ga kishiyarki can kowa fadin shigar ta yakeyi,keda ake taron don ke amma kamar saboda ita akeyi" sannan ne ta sake saka wata atamfar. Sanda ta fito falon tayi baqi ta hangi fitowar widad din ta window din falon nata da aka dauke curtains dinsa,ta yima matan abokan nasa rakiya,tana sanye da shadda 'yar mali,baqa ce da aka yiwa adon mustard yellow,zo kaga baqar shadda jikin farar mace,an tsara mata wani mugun dinkin bubu,ido kawai ta runtse hafsat din tana dauke kanta daga wajen tana jin Zuciyarta kamar zata fashe. Kwana biyu da suna suka koma inda suka fito,tabar hafsat din da tarin ciwo a zuciyar ta,da kuma K'ULLACI hadi da ALWASHI iri daban daban akan widad din. Duka duka sati uku da komawarsu bauchi tafiyarsu ta taso,zasu tashi ta kano,don haka suka shirya zuwa bauchin yayi sallama da hajiyansa,ya kuma sallami gida sannan su wuce kanon. Kamar ko yaushe,cikin tsoro da wani mugun bacin rai da qunci ta sauka a sassan nata,yau din tana jin tsanar gidan sosai fiye da ko yaushe,cikin qafafunta takejin kamar ba lallausan carfet

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});