Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 99

Chapter 99

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,191 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

toilet tayi wanka, d'aure da towel ta fito d'an k'arami, had'a ido tayi da Sabeer wanda yake zaune kusa da gadon Na'eem da Shaheed yana lilasu a hankali murmishi suka sakarwa junan su cike da so, wani mayataccen kallo Sabeer yake bin ta dashi wanda tun safe ta kula da irin wannan kallon nashi, ita tsoron ma zuwa kusa dashi take hannun shi ya mik'a mata bata yi musu ba ta mik'a nata ya rik'e shi tare da janyo ta jikin shi ya fara shinshina wuyan ta zuwa bayan ta hura mata iskar bakin shi yayi cikin kunnen ta wanda ya haddasawa Suhaima kasala cikin muryar rad'a yace "Baby nah ki bani wannan damar please ina son kasance wa dake nayi missing d'in ki da lot " Duk da ta gane nufin shi amman da taji abin da yace sai da taji fad'uwar gaba amman ya zata yi tunda hakk'in shi ne wanda ya rataya kan wuyanta, don haka k'ara shigewa jikin shi tayi kawai tana cusa face nata a chest d'in shi. "Bari naje nayi wanka koh? " Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira, tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tarar da ita har ta shirya cikin wata gown ta bacci iyakar rabin cinyarta (da yake Sabeer ya sanya Jiddah d'ebo mata kayan ta ba tare da wani ya gane ba) ta gyara gashin ta sai tashin kamshi take, kallonta yake kamar yau ya fara ganin ta. Agurguje ya shirya ya taho wajen ta ya rungume ta cikin jikin shi yana faman aika mata da zafafan sak'onnin shi cikin wani irin salo mai wuyar fassara, wannan daren sun raya shi sosai cikin wani irin kaunar junan su anan Sabeer ya gama tabbatar wa Suhaima itace rayuwar shi haka ita ma a 6angaren ta gwarzon nata shine jin dad'in rayuwar ta suna addu'a da fatan Allah ya barsu har karshen rayuwar su. Rayuwar su suke cike da jin dad'i da kwanciyar hankali suna kula da yaran su sosai da haka har Na'eem da Shaheed suka tasamma shekara d'aya yaran sunyi wani irin girma gashi suna wata goma suka iya tafiya gudun su suke ko'ina zuwa lokacin Aunty Aliyah tana d'auke da tsohon ciki itama, zumunci Jiddah da Suhaima kuwa kullum k'aruwa yake idan bata zo ba to za suyi waya junan su, tsakanin Suhaima da Sabeer kuwa kullum soyayyar su k'ara k'arfi take kula suke bawa junan su sosai, Daddy kuwa a weekend yake zuwa ganin jikokin shi. Suna watanni goma sha bakwai Suhaima ta yaye su, yayin da Aunty Aliyah kuma ta haihu aka samu mace sunan Umman su Suhaima aka sanya mata wato Fatima suna kiran ta da Ameerah, Yah Aliyu ma karatun shi ya d'auki zafi yana daf da had'a degree d'in shi a Buk. Wani zuwa weekend da Daddy yayi yace yana son Na'eem da Shaheed su bishi suyi mishi kwana 2 sunyi matuk'ar shak'uwa da Daddy sosai, a tsorace Sabeer ya barwa Daddy yaran shi don yana jin tsoron kada Mumy ta kashe musu yara, tsaf Daddy ya karance shi girgiza kai kawai yayi yana murmishi bai ga laifin shi ba yana da gaskiyar shi baisan yanzu yanda Mumy ta koma ba ne duk wannan ji da kan babu shi. ********** Duk wani jin dad'i gashi nan akwai shi sai dai babu kwanciyar hankali, duk tayi bak'i ta rame Dr Faridah kenan wato Mumy abin duniya yayi mata yawa wajen shekara 2 bata sanya tilon d'anta a idon ba tayi neman tayi binciken duk a banza tayi kok'arin tambayar Daddy akan inda d'anta yake but yace shima neman shi yake k'arshe ma rufe ta da fad'a yayi ai duk laifin ta ne gashi ta salwantar mishi da rayuwar d'an shi ba'a san inda yake ba. Ta 6angaren Dr Ahmad d'an fillo dasu Hajjah Hauwaa suma suna cikin wannan tsantsar tashin hankalin na rasa sanin inda Sabeer sunyi binciken iyakar iyawar su amman basu ji d'uriyar inda yake amman Dr Ahmad d'an fillo yaso d'ago Daddy yasan inda Sabeer yake ganin yanda hankalin shi yake kwance bai d'aga hankalin shi sosai ba akan 6atan Sabeer amman sai Daddy ya nuna mishi ba haka, tun daga lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya kwanta rashin lafiya saboda 6atan Sabeer d'an lelen shi yayi kuka sosai yana mai nadamar da tun lokacin yayi magana matar shi ta dawo gare shi tun da dalilin ta suka neme shi suka rasa, Haka ma Mumy ta kwanta ciwo a tsaitsaye ko hospital bata iya zuwa jinin ta hau sosai damuwa biyu ce ta had'e mata rashin tilon d'anta da kuma juya mata baya da mijinta yayi duk a dalilin Suhaima, wadda zuwa wannan lokacin tayi nadamar abin da ta aikata yafi sau ba adadi tayi kukan sosai da bata aikata hakan ba da tuni d'anta na kusa da ita har da jikokin ta ma, har tana fatan ta d'an samu sauk'i ta nemi garin su Suhaima taje ta nemi yafiyar ta ko zata samu sassauci cikin zuciyar ta da rayuwarta gaba d'aya. Tun safe yau jikin ta ya rikice ga Daddy baya nan yafita tana kwance a falo wajen 4 na yamma ne jefi jefi tana kallon tv tana kallon African Tv suna wa'azi na marigayi sheik Ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya jik'an shi da rahma Amin), lokaci zuwa lokaci gaban ta na fad'uwa. Sallama Daddy yayi ya shigo palourn hannun shi rik'e da Na'eem da Shaheed suna d'an tsalle tsallen su, wata zabura Mumy tayi ganin wasu kyawawan yara masu matuk'ar kama da junan su kuma abin da ya k'ara hargitsa ta ganin yanda suke matuk'ar kama da Daddy da kuma Sabeer, nan take wani tunani ya d'arsu cikin zuciyar ta ko Daddy aure ya sake bata sani ba matar ta haifa mishi yara. Da d'an gudun su suka k'arasa inda take tare da rungume mata k'afafun ta, sakin baki kawa tayi tana kallon su wani irin sanyi taji jikinta yayi ta zame ta zauna lokaci d'aya wani mugun son yaran ya ratsa mata cikin zuciyar ta da zuciya d'aya ta d'ago su zuwa jikin ta cikin murmishi take cewa "Ya sunan ku yara nah?" Na'eem da yafi surutu cikin muryar shi wadda bata kware ba yace "Ni sunan Na'eym wannan kuma Sha'eed" Ya k'arasa fad'i yana Shaheed da d'an yatsan shi, "Masha Allah sunan masu dad'i Allah ya albarkaci rayuwar ku " "Amin " Daddy ya amsa cikin zuciyar shi, d'agowa tayi ta kalli Daddy tare da cewa "Daddy yaushe ka sami yara masu kama da kai bansani ba? " Murmishi yayi yana tafiya Stairs yana cewa "Bana wa bane aron su aka bani na kwana 2 " Cikin d'okin murya tace "Da gaske kake Daddy?" "Ban ta6a yi miki wannan wasan ba gaskiyar kenan " Washe baki tayi duk yanda jikinta babu dad'i amma sai taji lokaci d'aya kamar an cire mata ciwon cikin farinciki take cewa "Nagode Thank U very much Daddy naji dad'in ganin yaran ji nake kamar my Son nake gani Allah ya biyaka " Ta k'arasa maganar hawaye na fita daga eyes nata sosai Daddy yaji wani mugun tausayin ta lokaci yayi da Dr Faridah ya kamata tasan ainahin inda d'anta yake yana gama wannan tunanin ya wuce stairs

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});