Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,175 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

to my Sadeey SaNaz *PAGE 71-72* Sai bayan mangarib su Sabeer suka k'arasa gida, yana shiga part d'in su ya hango Mumy kusa da dining table tana shirya abincin dare fuskarta d'auke da damuwa wanda mutum kallo d'aya zai mata ya karanci hakan. Yana zuwa ya rungume ta tare da bata peck a cheek d'in ta cikin farinciki yace "Mumy yau ina cikin farinciki sosai na kusan mallakar Suhaima ki tayani murna " Wani abu ne ya tokare mak'oshin Mumy wanda ya sanya ta d'an jimawa kafin ta bud'e bakinta tace "Son nasan ka gaji da yawa kaje kayi wanka da sallah tukunna " Ta k'arasa maganar cikin murmishin yak'en da yafi mata kuka ciwo, da yake Sabeer na cikin farinciki shi ya hanashi fahimtar yanayin Mumy, don haka kawai sai ya wuce up stairs. Bin bayanshi da kallo Mumy tayi kafin ta zauna saman kujerar dining table ta zabga uban tagumi, duk wannan abin da suke Daddy yana kofar shigowa parlourn yana kallon su. Ganin Mumy ta zauna ta zuba tagumi ya sanya shi k'arasa wa cikin parlourn hannun shi ya sanya ya janye tagumin da tayi kafin yace "Haba sweetie nah me yasa kike son shiga tsakanin farincikin d'anki, kinsani Suhaima itace farincikin Sabeer yana sonta rabuwa da ita ba k'aramin wani hali zai shiga ba, a matsayin ki na uwa kina mishi addu'ar fatan Alkhairi a wannan auren nashi, ni kaina da fari ban yarda ba da hakan ba, zama nayi tare da yin nazari kafin na amince mishi sannan da naje yau naga gidan da Son yake neman aure sai naji hankalina ya sake kwanciya da wannan auren don kuwa gidan gidan mutunci ne sosai, ina son ki kwantar da hankali kada wani ciwo ya shige ki matar mutum kabarin shi Allah yayi Suhaima ce zata kasance matar d'anki don haka kawai ki bisu da fatan alkhairi " Yana gama fad'in haka ya tashi ya wuce side d'in shi don kada a kirawo sallahr ishsha bai yi ko mangarib ba, Mumy tasan Daddy gaskiya ya fad'a mata but zuciyar ta tak'i amincewa da hakan. Bayan Sabeer yayi wanka tare da yin sallahr mangarib da ishsha ne, ya zauna saman sofa yana kok'arin kiran Suhaima hannun shi d'aya kuma yana rik'e da cup aciki fresh milk ce don baya jin zai iya cin abincin dare cikin shi a k'oshe yake ji Babyn shi ta cika mishi ciki. Lumshe idanun shi yayi jin sanyayyar murya Suhaima tana tambayar shi sun je gida lafiya, sake gyara kishingid'a yayi tare da cewa "Alhamdullilah Baby mun isa gida lafiya yanzu kin ganni a d'aki ni d'aya duk nagaji " "Ayyah sannu " Cewar Suhaima cikin tausayin shi. "Da munyi aure Baby nasan da ban da matsala zaki min tausa har na warware bama iya tausa ba har irin wanka da....... " Bata bari ya k'arasa maganar ba da sauri cikin jin kunya tace "Kaiii Sabeer baka jin kunyar fad'in wannan maganar? " "Keee Baby bana jin kunya indai da ke zanyi irin wannan maganar" Ya fad'i hakan cikin kwaikwayar maganar ta, dariya suka d'an yi kafin yace "Baby ina son ki da yawa kada ki wahalar da rayuwa, kada kiyi amfani da son da nake miki ki wahalar dani please " Ya k'arasa maganar kamar zai fashe mata da kuka, wani tausayin shine ya rufe Suhaima tare da wani irin son da yake k'ara shiga cikin zuciyar ta. "Sabeer don me zan wahalar da rayuwa bana fatan na kasance daga irin wadannan mutanen masu amfani da son da ake musu suke wulak'anta mai son su, ina maka son da bazan jure ganin ka cikin wahala ba balle ni na wahalar da kai, daga lokacin da ka zama mijina zan kasance mai yi maka biyayya dai dai iyawata" Wata ajiyar zuciya ya sauke wadda har sai da Suhaima ta jiyo shi kafin yace "Naji dad'in abin da kika ce Baby nah thank U very much" "Uhmmm " Abin da tace kenan, d'an murmishi yayi yana cewa "Baby ya neh koh bacci ya fara zuwa ne? " "A'a me kagani? " "Just naji kin ce uhmm" "Ba komai " "Okay bari na barki ki huta gud night and sweet dreams " "Same 2 U" A haka suka yi sallama kowa ya ajiye waya. Soyayya mai zafi suke nuna wa junan su tsakanin Sabeer da Babyn shi, duk wata kulawa wanda ya kamata suna bawa junan su, soyayya mai tsafta suke nunawa junan su, yayin da Daddy ya matsantawa Mumy da dole ita zata had'a lefen Sabeer saboda da fari da yayi mata maganar k'in amincewa tayi sai da yayi da gaske sannan ta yarda dakyar, ta 6angaren su Suhaima ma Yaya Aliyu da Aunty Aliya sai shirye shirye suke yi sosai na hidimar biki. Sabeer sai da ya nunawa Aliyu kada ya sha wahalar yi mata kayan d'aki zuwa kitchen don shi tuni ya gama shirya musu gidan su shi da Babyn shi, amman sam Yah Aliyu yak'i yarda ya kafe sai yayi dole tasa Sabeer hak'ura tunda baisan dalilin shi ba. *** **** *** *_After 2 week's_* "Hello Suhaima kina jina? " "Ehh Jiddah ina sauraren ki " "Yawwa Babyn Yah Sabeer gobe ina son zuwa zamu tattauna akan maganar bikin fah" Cikin rashin fahimta Suhaima tace "Kamar wanne shiri? " Hararar ta Jiddah tayi duk da tasan ba gani zata yi ba tun da a waya suke magana tace "Har kinsa na harare ki wallahi, da kin d'auka zamu yi biki lami ne kamar bikin Yah Sabeer da Besty na ai dole mu kwashi shoki " Dariya Suhaima ta tuntsire da ita kafin tace "Kinyi nauyin zaki kwaso shokin a haka? " "Dallah malama ina ruwan ki sai fah anyi duk wani zagaye zagayen ki yarinya " Suhaima na dariya tace "Toh sarkin masifa naji na yarda " "Yawwa ko kefa, kin ga zan d'auko mai gyaran jikin da zata yi miki ke dai kawai sai nazo don my dear ya dawo gud night " "Okay Allah ya kaimu " "Amin kiyi min d'an wake don Allah " "Zanyi miki kodan Babyn mu " Dariya suka yi kafin su yi sallama, sauke numfashi Suhaima tayi tare da gyara kwanciyar ta, wayar ta ne ya sake k'ara nan ta d'auka da sauri ganin Sabeer ne, hirar su ta soyayya suka sha sosai kafin su yi sallama, addu'ar bacci Suhaima tayi babu dad'e wa bacci mai dad'i ya d'auke ta.......... _Fan's kuyi hak'uri da page's d'in nan don ban samu damar yin editing ba dafatan za'a yi min afuwa duk inda aka ga error typing_ Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/17, 8:53 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 73-74* Washe gari kuwa tun safe bayan ta gama had'a breakfast ta karya nan ta gyara d'akin ta tsaf da tsakar gidan zuwa wankin toilet da wanke wanke sannan ta fara yiwa Jiddah d'an waken da take buk'ata, wanda ta hada filawa da garin rogo kad'an a ciki. Bayan ta gama yin d'an waken ta ne ta daka mata yaji mai dad'i wanda yasha citta da garlic sannan ta yanka cucumber, tomatoes and onion, tana kammala wa ta wuce wanka, bayan ta

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});