Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,192 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'ora hannun ta tayi dukka biyun a saman kanta tace "Wayyo Allahna na shiga uku ni Suhaima yau nice a waje har k'arfe goma sha d'aya da rabi innalillahi " Lokaci d'aya hawaye suka fara zubo mata ga wani mugun tsoro da sanyi da take ji, tafiya ta fara yi ta nufi k'ofar hall d'in taga duk yawan mutanen nan wayam sai wasu d'ai d'aiku wanda batasan fuskar su ba, tuni Suhaima ta samu waje d'aya ta raku6e ta fara rasgar kuka kamar wadda akai mata dukan tsiya. Kuka sosai take har da majina ta rasa mafita don duk a rud'e take ta kasa dai daita nutsuwar ta balle ta sami mafita gashi phone d'in Jiddah a hannun ta wa zata kirawo acikin familyn ta mutanen da basu yi maraba da zuwan ta cikin su ba matsayin bak'unta na kwanaki biyu, balle ta samu damar kiran wani daga ciki ya taimaka mata, gashi idan ma ta kirawo Yaya Aliyu d'aga musu hankali kafin ma yazo ma koma mai ne ya cinye ta kuma bata yi wa Jiddah adalci ba idan ta fad'a mishi yanzu ya zata yi wayyo Allah na, sake rushe wa da kuka Suhaima tayi sosai tana nan a raku6e taji an dafa mata kafad'a tare da cewa "Hey what are you doing here? " Wata irin firgita Suhaima tayi tare da jiyowa a tsorace had'a ido tayi da wannan guy d'in na d'azu yana tsaye daf da ita ya hard'e hannun shi a kirji, wani k'ugi cikin ta yayi wanda tana tunanin ma Sabeer yaji k'arar da cikin nata yayi matse k'afafun ta ta fara yi saboda daf take da sakin fitsari a tsaye jikin ta kuwa sai rawa yake wanda ya sanya wayar Jiddah ta fad'i a k'asa da bag d'in ta. Kallon ta Sabeer yake up and down yana sakin wani murmishi wani sanyin dad'i ne yake ratsa cikin zuciyar shi da gangar jikin shi, sauran kad'an dariya ta kubce mishi ganin yanda take matse k'afa tamkar wanda yake jin fitsari ya matse shi irin sosai d'in nan har k'arar da jikin ta yayi sai da yaji sautin. Ganin murmishin da yake ba k'aramin sake rud'ar da Suhaima yayi ba aikuwa fakar idon shi tayi ta tattara gown d'in ta da hannun ta kafin Sabeer ya ankara yaga Suhaima ta zura da gudu tayi hanyar fita daga gate, ba shiri shima ya d'auki phone d'in da bag nata da suka fad'i ya bita da gudu shima. Suhaima da ta bud'e kofar gate d'in zata fita da sauri ta dawo baya jin wani irin sanyi da ya busa ta gashi wajen duhu babu wadaccen haske sosai a wurin nan ta tsaya waje d'aya tana rawar jiki, da haka Sabeer ya cimmata tana tsaye sai ruwan hawaye da yake tsere saman kyakkyawar face d'in ta, ganin Sabeer a kusa da ita da sauri Suhaima ta bud'e baki tace "Don girman Allah kayi hak'uri da abin da nayi maka tsautsayi ni bazan sake ba har abada kayi hak'uri kada kayi min komai bansan kowa anan ba " Sosai ta bashi tausayi ganin irin rud'ewar da tayi cikin sanyin murya yace "Hey calm down babe babu abin da zan miki just I'll help you" Kamo hannun ta yayi ganin har yanzu bata daina rawar jiki ba kuma a rud'e take, jan hannun ta yake har cikin mota ya zaunar da ita tukunna ya zagayo seat d'in driver ya zauna kallon ta ya tsayayi na tsayin wasu minutes, kallon yake cikin wani irin yanayi ita kuwa kanta a sunkuye batasan abin da yake ba tsoro ne fal a tattare da ita addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada ya cutar da ni, kafin yayi wa motar key suka bar wajen sun d'an yi nisa suna tafiya tukunna ya jiyo ya kalle ta still har yanzu kanta a sunkuye. D'an girgiza kai yayi tare da sakin dan murmishi yace "Ina zamu je, i mean ina ne gidan da zan kai ki? " D'an satar kallon shi tayi ta fad'a duniyar tunani ita da take bak'uwa a garin yau ne zuwan ta na farko ina zata gane gidan, don haka sai tayi shiru kawai. Ganin haka yasa Sabeer yace "Ina jiran ki fah kinsan dare yayi fah idan baki da wajen zuwa kuma sai mu wuce guest house d'ina mu d'an huta zuwa gobe " Wani zaro ido Suhaima tayi tamkar idanun ta zasu firfirto wani tsoro da nadamar shiga motar shi ya dirar mata lokaci d'aya ashe d'an iska ma ta shiga motar shi yau na shiga tara ba uku ba, dariya sauran kad'an ta kubce wa Sabeer ganin yanda Suhaima ta koma. "Don Allah kasan gidan su amaryar Jiddah? " Suhaima ta fad'a cikin rawar murya, da mamaki ya kalle ta kafin yace "Oh nan zaki je kenan? " Da sauri Suhaima ta d'aga kanta alamar eh, mamaki ne sosai ya kama shi ta yanda akayi Suhaima tazo gidan tun da yasan halin 'yan gidan su da basa huld'a da talaka sai mai kud'i d'an uwan su. Kuyi hak'uri da wannan fan's mu had'u a next page muji ya zata kasance. Ga Sabeer da Suhaima sun had'u shin komai zai faru kuma?... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 38-39 Babu wanda ya sake magana a cikin su kowannen su da tunanin da yake cikin zuciyar shi, amman Suhaima har yanzu hankalin tashe yake ganin har yanzu basu zo gidan ba ta sadaukar sace ta ma yayi tuni wasu sababbin waye sun cigaba da zuba saman fuskar ta, d'an kallon ta Sabeer yayi kad'an yana girgiza kai cike da mamakin ta ko wahalar kuka bata yi. Da haka suka k'arasa gidan Suhaima tana ganin an shiga cikin gidan ta tabbatar shine sai da ta saki ajiyar zuciya na kwanciyar hankali kafin ta sanya hannun ta saman face nata da niyyar goge hawaye sai taga an mik'a mata tissue kar6a tayi ta goge tukunna ta fara kok'arin bud'e kofar motar, kamar ance ta jiyo ta kalli side d'in su Jiddah aikuwa ta hango Jiddah tana tafiya cikin sauri tana goge fuska, da sauri Suhaima ta k'arasa fita kamar abin arzik'i ta rufe kofar motar sai ta zuro kanta ta jikin window da yake ya sauke glass d'in. Sabeer har zai yi wuce zuwa parking lot sai yaga ta zuro kanta sai ya tsaya ya d'auka godiya zata yi mishi sai hasashen shi yasha banban da na Suhaima don cikin tsiwa ta fara cewa "Uhm Malam ka d'auka godiya zan maka da ka zuba ido kana kallona har da bud'e kunnuwa don jin abin da zance, to ban gode ba kuma hak'urin da na baka d'azu in mistake ne, me yasa ma ka tausaya min ka d'auko ni da ka barni acan ma da nafi jin dad'i... " Da sauri Suhaima ta fitar da kanta tare da zurawa da gudu zuwa inda ta hango Jiddah a tsaye sai safa da marwa take, sakamakon wata cafka da Sabeer ya kawo mata ganin ta gudu ne yasa shi dunk'ule hannun shi ya naushi d'aya hannun kafin ya jingina kanshi jikin

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});