Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,187 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana dariya tare da cewa "Haba Besty daga wasa sai duka kin mance ni amarya ce zan had'a ki da my sweet darling fah" D'an murmishi Suhaima tayi kawai ta d'auki phone d'in Jiddah tana kallon pic's d'in ciki, da haka har suka k'arasa gidan su Jiddah amman daga waje tayi parking bata shiga cikin gidan ba, Wow! abin da Suhaima tace kenan ganin irin unguwar su Jiddah ta manyan masu kud'i ce ganin gidan su Jiddah kuwa sai da gaban Suhaima da na Yaya Aliyu ya fad'i. Anya basu yi gangancin sake wa da Jiddah ba irin wannan k'aton gidan daga ni Iyayen ta ba k'aramin masu kud'i bane, lokaci d'aya jikin su yayi sanyi sosai, nan Jiddah ta k'arasa wajen Yaya Aliyu suka yi sallama bayan ta tabbatar mishi da jibi da yamma yazo d'aukan Suhaima idan yazo ya kirawo ta a waya daga haka suka yi sallama ya buga machine d'in shi ya tafi jiki a sanyaye yana dana sanin sakewa da Jiddah da suka yi har haka, kada a wulak'anta mishi k'anwa ko kuma su bud'e mata ido da rayuwa amman da ya tuna irin tarbiyyar Jiddah sai ya d'an ji sanyi cikin zuciyar shi but still jikin shi a sanyay dakyar yake tuk'a machine d'in yana addu'a cikin zuciyar shi Allah ya tsare mishi Suhaima har taje ta dawo lafiya... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Dis page is dedicated to Ayusher Ilias my Namecy Biebie dee tawa My Zeee yabour Asy khaleel, kirkin ku daban ne ina yin ku sosai sister's Allah ya bar zumunci a tsakanin mu ❣ PAGE 32-33 Bayan tafiyar Yaya Aliyu ne Jiddah ta shigo motar tayi mata key maimakon su shiga gidan sai Suhaima taga ta juya sun bar unguwar gaba d'aya, cikin tsokana Jiddah tace "Baki ji tsoro ba kada na siyar da ke naga baki tambaye mu ina zamu je ba " D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Na yarda da ke ne sosai Jiddah nasan son da kike min bazai sa ki cutar da ni ba " "Haka ne tawan Allah ya bar mu tare har 'ya'ya da jikoki, waiii ya kaga Suhaima da jikoki suna cewa goggo Suhaima " Dariya kawai suka yi adaidai lokacin Jiddah ta k'araso inda zasu je wani katafaren shagon yin gyaran jiki, saloon, manicure and pedicure da kuma make-up sai lalle, parking Jiddah ta samu tayi suka fito zuwa cikin shagon sosai wajen ya burge Suhaima, matar wajen tana ganin Jiddah ta fara washe baki da alama ta saba zuwa wajen. Babu 6ata lokaci Jiddah ta fad'a wa matar abin da za'a yi wa Suhaima, aikuwa nan suka shigar da Suhaima wani room suka farayi mata gyaran jiki na dilka sosai suka tsaya suka gyara Suhaima sun san zasu samu kudi masu tsoka, bayan an gama gyaran jikin aka yi mata gyaran su farce sannan aka dawo kan lalle daga k'arshe kuma aka gyara mata gashi wanda basu sanya mata relaxer ba cos gashin Suhaima yana da tsantsi irin na asalin fulani sai suka wanke mata kan da kalolin shampoos and conditioner different color's, sannan suka busar mata da dogon gashin ta da hand dryer tukunna suka gyara mata in style. Kyan da Suhaima tayi 6ata lokaci ne wajen fad'ar shi tayi kyau sosai tamkar ba ita ba, har wasu kayan Jiddah ta bata ta sanya wata milk d'in gown mai adon light green sai veil light green shima nan ta sanya kayan aka yi mata light make up sosai tayi kyau, rolling d'in veil d'in suka yi mata akanta ba k'aramin had'uwa tayi ba idan kaga Suhaima ka d'auka irin mai kud'in nan ce ba daga k'auye ta fito ba. Ita kanta Jiddah bata zata haka Suhaima take ba sai yanzu hankalin ta ya kwanta tasan dai ba lalle iyayen ta su gane daga inda Suhaima ta fito ba, kuma ba laifi kan Suhaima a waye yake bata da dahun kai, nan Jiddah ta biya kud'in suka fito daga shagon kai tsaye gida suka nufa. Horn Jiddah tayi gateman ya bud'e mata kofa ta shigo ciki a parking lot tayi parking tukunna suka fito daga motar, sakin baki da hanci Suhaima tayi ganin irin girman gidan su Jiddah gashi part part ne sosai gidan ya birge Suhaima amman bata kuma aha'awar zaman irin cikin gidan nan don tasan dole a samu masu wulak'anta mutane, ta6o ta Jiddah tayi tana murmishi tace "Alhamdulillah yau Allah ya nufa Suhaima zata zo gidan mu, ina cikin farinciki yau sosai, Suhaima ga gidan mu nan kina ciki yau anan aka haife ni na girma, daman na fad'a miki gidan mu muna da yawa don kakan mu da iyayen mu duk a ciki muke zaune " Gid'a kai Suhaima tayi tana k'ak'alo murmishin yak'e kafin tace "Masha Allah wannan gidan naku yayi kyau sosai Jiddah " Kamo hannun Suhaima tayi tare da cewa "Thank U my dear " D'auko bag d'in Suhaima tayi suka nufi wani part, duk taku d'aya da Suhaima take sai gabanta ya fad'i sosai gaba d'aya a tsorace take kamar wadda za'a sace haka take jin ta. Suna shiga cikin k'aton parlourn wani sanyin Ac da k'amshin turare ya bugi hancin Suhaima ko'ina tsab dashi duk da mutanen da suke zazzaune cikin parlourn kuwa, kusan gaba d'aya mutanen kallon Jiddah da Suhaima suke. Tuni Suhaima ta fara tsarguwa da kallon, wata matashiyar budurwa ce kamar sa'ar Jiddah ta taso da gudu ta rungume Jiddah tana cewa "Ga amarya ga amarya nan ta dawo, ina kika shige muna ta neman ki? " D'an murmishi Jiddah tayi tare da cewa "Na d'an fita ne wani wajen " Kallon budurwar tayi tare da cewa "Zahra meet my friend Suhaima Omar, Suhaima meet my sister Zahra 'yar gidan K'anin Abban mu ce " Cikin murmishi Suhaima tace "Ina yini? " Wani banzan kallo da Zahra tayi wa Suhaima sai da ta kusan zubewa a k'asa saboda rawar da jikin ta ya fara, wani banzan tsaki Zahra ta saki tare da hararar Jiddah tace "Kefa tsiyata kwashe kwashe ne dake ina kuma kika samo wannan villagers girl d'in? " Dumm gaban Suhaima da Jiddah ya fad'i, duk gyaran da ta kashe kudi tayiwa Suhaima don kada su gane daga inda ta fito sai da Zahra ta gane, wannan maganar a cikin zuciyar ta Jiddah tayi bayan ta gama k'arewa Suhaima kallo inda taga ita bata hango makusa ba sai ma kyan da Suhaima tayi, amman sai ta dake ta harari Zahra tare da cewa "Ni fah bana son iskanci Zahra wannan fa friend d'ina ce tare muka yi schl itace fa Suhaiman da nake baku labari" Wata shegiyar dariya Zahra ta saki tare da nuna Suhaima da d'an yatsa tace "Dis villagers girl ce kuka yi schl tare kin ma raina min hankali nafa sanki da kwashe kwashe " Haushi ne ya turnik'e Jiddah a fusace taja hannun Suhaima wanda idanun ta sun ciko da kwalla taf suka nufi hanyar da zata kai Jiddah part d'in Umman ta yayin da Zahra da sauran mutane wanda suka karkata hankalin su da

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});