Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,186 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana zaro ido tare da cewa "Innallilahi Aliyu mai ya cije haka " Zaunar da Sabeer yayi saman kujera kafin yace "Cizon sauro ne wallahi" "Allah sarki sannu Sabeer Allah ya baka lafiya " D'an murmishin yak'e yayi mata yana d'aga kanshi alamar amsawa, tun lokacin da Aunty Aliyah ta fara magana Suhaima ta d'ora idanun ta kan Sabeer ta k'ura mishi ido cikin wani yanayi wanda ni kaina na kasa tantancewa, sai da suka had'a ido tukunna ta janye nata idon daga kallon shi ta sunkuyar da kanta. "Suhaima zo ki samo ruwan d'umi a kitchen yayi brush dashi " Tashi tayi ta d'auki buta ta d'ebo ruwan d'umin ta kawo maimakon ta sirka shi sai kawai ta dire a gaban shi a haka gaba d'aya jinta take wata iri kamar ba ita ba. "Wash Allah! " Taji muryar Sabeer ya fad'a da sauri ta kallo inda yake sai taga yana yarfe hannun shi tare da yatsina fuska ga hannun yayi ja sai lokacin hankalin ta ya dawo jikinta ta mance bata surka ruwan da na sanyi ba. "Suhaima baki da hankali da zaki kawo mishi ruwan zafi ba tare da kin surka ba" Fad'in Yaya Aliyu kenan yana hararar ta bayan sun had'a ido. "Laaa Yaya na mance ne Allah kayi hak'uri " Da sauri ta mik'e ta d'auki butar ta nufi wajen da suke ajiye ruwa ta surka ta kawo mishi tukunna ta koma ta zauna, duk inda tayi idanun Sabeer suna kanta suna shawagi gaba d'aya ta kasa sakewa. A haka ya lalla6a yayi brush sannan ya dawo saman tabarmar zama yayi kusa da Suhaima sai ya jingina da bango, sannu Aunty Aliya da Yaya Aliyu suka yi mishi ya amsa muryar shi can k'asa, koko ne mai kauri yasha gasara Aliyu ya mik'a wa Sabeer hannun shi yasa ya kar6a tare da kaiwa baki ya kur6a. Ba shiri ya furzo dashi waje sai a jikin Suhaima ya 6ata mata jiki don duk ya tsatstsalu a jikin ta har da saman fuskarta, sannu suka k'ara yi mishi yayin da Suhaima ta cukune fuska takaici da 6acin rai fal zuciyar ta har a saman fuskar ta ya nuna. "Am sorry please " Ya fad'i cikin sanyin murya fuskar shi d'auke da damuwa dagani kasan ba'a son ranshi yayi mata ba. "Je ki canja kayan ki wanke fuskar ki" Fad'in Aliyu kenan ganin irin yanda Suhaima take jifan Sabeer da kallon tsiwa. A fusace kuwa ta mik'e ta wuce d'akin ta bata dad'e ba ta fito d'aure da zanin wanka tare da hijab a jikinta ruwan wanka ta had'a tare da wucewa toilet. Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta ji yake tamkar ya tashi ya rungume ta cikin jikin shi ya rarrashi ta ya nuna mata hakan da ya faru ba'a son ranshi ba ne tsautsayi ne amman babu damar yin haka. "Me zaka ci a dafa maka tunda baka son kokon? " Fad'in Aunty Aliya kenan "Aunty idan na samu ruwan tea ma ya isheni don bana sha'awar cin komai" "Haba haba ruwan tea me zai maka ka fad'in abin da kake so kawai nan kamar gida ne " "Kin ga wuce kitchen mu je " Cewar Aliyu nan suka tashi suka tafi kitchen suna shiga Aliyu ya fita bai dad'e ba ya dawo, cikin mintuna kad'an Aunty Aliya ta dafawa Sabeer tea da yasha kayan kamshi citta da kaninfari sannan aka soya kwai suka kawo mishi. "Sannu da kok'ari Auntyn mu" D'an murmishi kawai tayi. A lokacin Suhaima ta fito daga toilet da harara tabi Sabeer kafin ta wuce d'akin ta. Nan suka karya har suka gama Suhaima bata fito ba nan Aliyu ya tafi siyowa Sabeer paracetamol, yayin da Aunty Aliyah ta wuce d'akin ta. Sabeer yana kok'arin mik'ewa don wuce wa d'aki ya kwanta Suhaima ta fito kallon shi tayi tare da cewa "Malam ba lallai ba dole idan baza ka iya zaman nan ba ka tarkata ka koma inda ka fito tunda babu wanda ya gayyace ka anan don bazai yiwu kana had'a mutane da wahala ba " Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan gaba d'aya, nan tsaye take Sabeer yaji wani zazza6in yana neman rufe shi dakyar ya iya kai kanshi d'aki ya zube akan katifa yana wani irin numfashi...... Kuyi hak'uri da ni fan's, kun ji ni kwana 2 shiru abubuwa ne sai a slow but insha Allah zan nayi kok'ari wajen typing. Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/22, 8:55 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz Dis page is dedicated to Faridah Bashir (Ummu Safwan) marubuciyar Tambarin sarautah, wannan shafin naki ne kyauta Allah ya raya mana Safwan ya k'ara zumunci Amin ❣ PAGE 55-56 Yana cikin wannan haline Aliyu ya shigo d'akin hannun shi rik'e da paracetamol da ruwa a cup na roba, ganin halin da Sabeer yake ciki ne yasa Aliyu ajiye maganin a gefe ya k'arasa wajen shi da sauri ya rik'o shi tare da cewa "Sabeer jikin ne? " Jan wani numfashi yayi wanda ya sanya Aliyu mugun tsorata, a hankali kuma ya sauke numfashin nashi tare da zaunawa saman katifar ya jingina bayan shi da bango kallon Aliyu yayi da idanun shi jawur dasu wanda yake afkin yi mishi sannu fuskarshi da tarin damuwa yace "Kada ka tashin hankalin ka bani maganin nasha " "Kodai zamu je asibitin nan na kusa damu su duba ka " Cewar Aliyu d'an murmishin yak'e yayi kafin yace "Basai mun je ba naji zazza6in ya sauka yanzu sauran ciwon kai bacci zanyi yanzu " Sannu Aliyu ya k'ara yi mishi kafin ya fita ya bashi gurin dob ya samu damar yin bacci, tunani kawai Sabeer ya fad'a na yanda Suhaima take wulak'anta shi ina laifin shi anan don kawai yace yana sonta da wannan tunanin bacci mai nauyi ya d'auki Sabeer. Tunda Sabeer ya farka daga baccin yaji da sauk'i ciwon kan ya ragu, tun daga lokacin Sabeer yake kok'arin koyan cin abincin su yana kuma bin Aliyu gona duk da baya kok'arin yin aiki idan sun je zai zauna yana kallon yanda yake yi ko kuma ya dunga zagaye gonar ko kuma Ashiru wanda ya taimake shi ya kawo shi gidan su Suhaima da yamma wani lokacin zai zo su tattaka zuwa cikin k'auyen, gashi yana kiran iyayen shi su gaisa sannan Aliyu, Aliyah da Babaa Lantana da Baba Adamu suna kok'ari wajen janshi a jiki ya sake dasu tamkar 'yan uwan na jini. Sai dai ta 6angaren Suhaima ne har yanzu babu wani cigaba don har yanzu tak'i bawa Sabeer fuskar da zai bayyana mata yanda yake sonta. Aunty Aliya kuma tayi nauyi sosai sai ya kasance duk wani aiki na cikin gidan Suhaima ke yi, yayin da Aliyu wani lokacin yake taimaka mata idan ayyukan sunyi mata yawa. Suhaima ce zaune saman kujera tana yankan salad tana sauraron freedom redio cikin shirin su na duniyar mu a yau wanda Usman Usman yake gabatar wa tana son shirin sosai batason ya wuce ta, Sabeer ne yayi sallama ya shigo gidan tun kafin ta amsa mishi, haushi ya turnik'e ta don haka sai ta fara gunguni tana cewa "Mutum sai kawai ya

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});