Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,177 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya fara gajiya ga wani uban tsoro da ya mamaye zuciyat shi ganin babu gidaje sosai, amman suna dad'a gaba sai ya cika da mamaki da yaga sun shiga wata unguwa duk gidaje sosai ba kamar inda suka baro ba. A k'ofar wani gida yaga sun tsaya saurayin yace "Ga gidan nan " "Yawwa sannu thank U so much " Nan ya shigar mishi da trolley d'in cikin zaure ya ajiye, laluba aljihun shi Sabeer yayi na jeans ya zaro 1k ya mik'a mishi tare da cewa "Gashi abokina na gode sosai but ka kar6a don Allah " Hannu biyu saurayin yasa ya kar6a tare da zuba godiya har zai wuce da sauri Sabeer yace "Hmm jimana abokina ya sunan ka? " D'an murmishi yayi tare da cewa "Sunana Ashiru kuma ga gidan mu nan " Ya k'arasa fad'i yana nunawa Sabeer gidan su wanda gida d'aya ne tsakanin su da na Suhaima. "Ni kuma Sabeer " "Sunan ka mai dad'i irin na 'yan birni " Dariya ya bawa Sabeer wanda ya sanya sai da ya d'an yi murmishin dariya saboda ya kula zai yi abin dariya, daganan ya wuce ya tafi Sabeer kuwa babu neman isowa ya kutsa kai cikin gidan tamkar irin gidan nan nasu. Suhaima tana zaune kan wani dutse tana alwala ta sallahr mangarib, ga Aunty Aliya kuma tana kok'arin sauke miyar abincin dare kenan daga saman murhu suka yi wata sanyayyar murya tayi musu sallama. Amsawa Aunty Aliya tayi yayin da Suhaima ta tsinci kanta da bugawar zuciya na lokaci d'aya, kafin su ankare sunga mutum a filin tsakar gida a tsorace Aunty Aliya ta kalle shi yayin da Suhaima ta kusan zubewa a k'asa saboda tsabar kid'ima da tsorata na wanda ta gani a k'auyen su kuma cikin gidan su. "Malam lafiya wa kake nema " D'an murmishi yayi tare da d'auke idanun shi daga kallon Suhaima ya dawo dasu kan Aunty Aliya yace "Nazo neman Suhaima ne sunana Sabeer " "Suhaima kuma? " Aunty Aliya ta furta hakan tana kallon Sabeer kafin ta jiyo da kanta zuwa kallon Suhaima wadda jikin ta yake rawa na tsorata. "Eh Suhaima nake nazo nema, idan babu damuwa zanyi sallah sai nayi miki bayanin ko ni waye? " Aunty Aliya sai tsoron nata ya ragu don kallon da tayi wa Suhaima ta karance ta tsaf alamar tasan shi amman tayi mamaki sosai na yanda Suhaima ta iya 6oye mata abu, don haka sai tace "Toh ai babu damuwa " Nan ta je inda suke ajiye botocin gidan ta d'auko babbar butar Yaya Aliyu da bata rabo da ruwa aciki ta ajiyewa Sabeer a gaban shi, d'an murmishi yayi tare da cewa "Na gode " Murmishin yak'e Aunty Aliya tayi, tana nan tsaye ya ajiye jakar laptop d'in shi dake rataye a kafad'ar shi saman wani dutse sannan ya tsugunna yayi alwala, abin sallah Aunty Aliya ta bashi sabida masallacin da nisa daga gidan ba lalle ya gane ba yana bak'o, kar6a yayi ya shimfid'a ya fara sallahr har zuwa yanzu Suhaima na tsaye tamkar wadda aka dasa a wajen ko kwakkwaran motsi bata yi, ganin haka ya sanya Aunty Aliya janyo hannun Suhaima suka wuce d'akin ta. Cikin tsoro tace "Suhaima wane ne wannan? " Suhaima itama a tsorace tace "Na shiga uku Aunty yanzu sai da Sabeer ya biyo ni " "Ki fad'a min wane shi kafin Yayan ku ya dawo daga masallaci " Murya na rawa ta bud'e baki zata yi magana suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gida, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa...... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/10, 5:16 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 51-52 Murya na rawa ta bud'e baki zata yiwa Aunty Aliya bayani suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gidan, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa gaban su sai dukan uku uku yake na tsoron yanda Aliyu zai saurare su na shigowar wani kai tsaye gidan. A haka ma a tsakar gida kallon kallo aka tsaya yi da Aliyu da Sabeer wanda idar da sallahr mangarib d'in shi kenan, da fara'a Aliyu ya shigo gidan anman had'a idon da suka yi da Sabeer ya sanya fara'ar fuskar shi ta d'auke lokaci daya ya 6ata fuska gefe d'aya na cikin zuciyar shi yana mamakin wannan wane ya shigo mishi gida haka kai tsaye haka har yana sallah. Sabeer ganin Aliyu ya d'aure fuska sosai yasa shi tsorata gaban shi ya fad'i kada ya kore shi daga gidan, murya na rawa yace "Sannun ka ina yini? " Cewar Sabeer kanshi a k'asa don ya fara tsarguwa da wannan kallon da Aliyu yake mishi, tamkar bayason amsawa yace "Lafiya k'alau " D'an matsawa yayi kusa da k'ofar d'akin Aliyah yana mamakin da har yanzu babu wanda ya fito ya amsa mishi sallama tsakanin ta da Suhaima tunda ba haka suke mishi ba matuk'ar suna gidan kuwa. "Aliyah, Suhaima kuna ina? " Muk'ut Suhaima da Aliyah suka had'iye yawu lokaci d'aya, idanun ta saman fuskar Suhaima tace "Gamu a d'aki mun yi sallah ne " Alhalin babu wanda yayi yunk'urin yin sallahr har gwara Suhaima tayi alwala. "Ku fito ina son ganin ku " "Toh gamu nan " Fad'in Aliyah cikin dakiya don ita tafi ma Suhaima jarumtar amsawa, sun d'an d'auki mintuna biyu sannan suka yi shahadar fitowa gaba d'ayan su. Yaya Aliyu yana zaune saman tabarma kusa da k'ofar d'akin Aliyah, yayi da Sabeer yake zaune saman abin sallah a tak'ure hankalin shi a matuk'ar tashe saboda uban cizon da sauro yake galla mishi a hannu da k'afar shi ga kukan shi da ya dameshi cikin kunnuwan shi ga zafi don sai had'a gumi yake. Fitowa suka yi tare da zama kusa da Yaya Aliyu sai da ya kalle su na 'yan mintuna kafin yace "Na shigo gida sai na tarar da wani abin mamaki dana gani, shin wane? Kuma me ya kawo shi cikin gidana ba tare da yarda ta ba? " K'uwwww cikin Suhaima da Aliyah ya fitar da wannan sautin ganin yanda Aliyu ya d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya, basu ta6a ganin shi cikin wannan had'e fuskar ba sai yau don haka suka tsorata. "Ku nake saurare ku yi min bayani " Fad'in Aliyu kenan ganin sunyi shiru kansu a sunkuye. Aliyah ce tayi k'arfin halin cewa "Uhm da....daman yanzu mu... muke son kiraka a... a waya mu fad'a maka, ya dai... dai ce sunan shi... shi Sabeer " Kallon baku da hankali yayi musu da sauri Aliyah ta sunkuyar da kanta ganin irin kallon da Aliyu yake jefan ta dashi, idan ba wannan kallon yayi musu me zaiyi taya ya kawai bakasan mutum ba ka barshi ya shigo cikin gidan ka kai tsaye namiji ma ba mace ba a yanda zamanin yanzu abubuwa suka ta6ar6are. Bai k'ara bi takansu ba ya juya wajen Sabeer da lokacin hankalin shi ya gama tashi saboda cizon sauro tamkar zai fashe da kuka ko yayi ta ihu ko yaji dad'i, Suhaima tana ankare dashi cikin zuciyar ta tace "Allah ya k'ara da uban wani iyayi ne

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});