Chapter 4
Chapter 4
yiwa Aliyu saboda yanda take jin jikin nata, yayin da Suhaima take kuka sosai, saboda ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki, da gudu Aliyu ya fice daga gidan har yana cin tuntu6e da dutse, yana saurin k'arasa wa gidan Babaa lantana mak'ociyar su, domin neman taimakon ta......... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI* 💝 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive Writer's Forum Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 5-6 Da gudu Aliyu ya shiga cikin gidan Babaa Lantana yana kuka sosai, Babaa Lantana mak'obciyar su fatima ce, mutunci sosai suke yi, tana tsananin tausayin Fatima da yaran ta, ita da mijin ta shi yasa wani lokacin suke taimka musu da abin da Allah ya hore musu, don su ma ba wani kud'i suke dashi ba sai rufin asirin Allah, suna da yarinya d'aya mai suna Aliyah ta d'an girmi Suhaima da kusan shekara hud'u, ita kad'ai Allah ya basu rayayyiya cikin duk yaran da take haihuwa suke mutu. A madafa Aliyu ya tarar da Babaa Lantana tana sauke abinci daga kan murhu, d'ago kanta tayi da sauri ganin yanda aka shigo mata gida kai tsaye babu sallama, mamaki ne ya kamata ganin Aliyu ne ya shigo yana kuka, cikin mamaki tace "Aliyu lafiya, mai ya faru kake kuka? " Cikin rawar murya da hakin gudun da yayi yace "Babaa Lantana ki taimaka mana, Inna ce bata da lafiya gashi ji...... ' Kafin ya k'arasa maganar da yake yi ne, tuni Babaa Lantana ta d'auko fallen zanin ta na atampa a saman igiyar shanya ta lullu6a shi a kanta, ta fita da sauri shima Aliyu ya bi bayan ta, har suna rige rigen shiga gidan. Cikin d'akin suka shige da sauri inda Fatima da Suhaima suke, Fatima sai murk'uk'usun azabar ciwo take tana hawaye, yayin da Suhaima take zabga kuka da k'arfi don ganin halin da Innar su take, da sauri Babaa Lantana da Aliyu suka k'arasa inda take, ganin halin da take ciki ne ya sanya Babaa Lantana cewa "Subhanallah Fatima 6ari ne sannu Allah ya baki lafiya " Kallon Aliyu tayi tace "Aliyu kama hannun Suhaima ku fita tsakar gida " Girgiza kai Aliyu da Suhaima suka yi lokaci d'aya, kafin Aliyu ya iya cewa "Babaa Lantana kiyi hak'uri ki bar mu a wurin Innar mu " Itama girgiza kai tayi tare da cewa "A'a Aliyu kayi hak'uri ku je waje " Dakyar Babaa Lantana ta shawo kan Aliyu ya kama hannun Suhaima suka fita waje, suna waiwaiyar Innar su, da batasan halin da take ciki don ta fara fita a hayyacin ta. Bayan fitar su ne Babaa Lantana ta fara yiwa Fatima dabarin su irin na zamanin da, ganin abin yana kok'arin gagarar ta ne ya sanya ta fito waje inda Aliyu suke raku6e waje d'aya, kallon su tayi wani tausayin su ne ya kamata dakyar ta iya cewa "Aliyu kayi sauri kaje ka kirawo Ladi ungozoma " Gid'a kanshi yayi sannan ya fita da gudu, ita kuma Babaa Lantana ta koma cikin d'akin wajen Fatima, ta bar Suhaima anan zaune tana kuka. Babu dad'e wa Aliyu ya dawo Ladi ungozoma tana bin shi a baya, d'akin da Fatima take ciki ya iya nuna mata da d'an yatsan shi, Ladi ungozoma kuwa wadda ke d'auke da k'aramin buhu a hannun ta na kayan aikin ungomanci irin na zamanin da, ta shige cikin d'akin. Duk yanda suka yi kok'ari wajen kada cikin Fatima ya zube, sai da cikin ya zube sai dai jini yak'i tsayawa sai zuba yake, nan dai ungozoma ta bayar da maganin da za'a jik'a mata ta sha, sannan Babaa Lantana ta biya ta kud'in ta, ta had'a kayan nata ta tafi. Babaa Lantana sai da ta gyara jikin Fatima tsaf da d'akin, sannan ta kirawo Aliyu da Suhaima don su zo wajen ta, sannan ta tafi gida don d'ebowa Fatima abinci don ba k'aramin gala6aita tayi ba sosai, tun da ba wani abincin kirki take samu ta ci ba, da sannu Allah zai saka ita da yaran ta a wajen Umaru, tabbas yaci amana bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ya azabtar da su, duk don son rai irin shi nashi. Suna shiga d'akin wajen Fatima suka nufa, zama suka yi a gefen ta gaba d'aya sun zuba mata suna kallon ta tamkar yau suka fara ganin ta. Kallo d'aya mutum zai mata yasan bata da ishashshan jini a cikin jikin ta, saboda yanda tayi wani fari sosai, gashi ta rame sosai dakyar take iya motsi ma, kallon yaran nata tayu tana daga kwance, wani tausayin sune ya kamata, a hankali wasu hawaye suka shiga zubowa daga idanun ta, bud'e bakin ta tayi wanda ya bushe saman le6en yayi fari tace "Aliyu ga Suhaima nan koda na mutu ka rik'e ta cikin amana, ina horan ka da ka tsaya tsayin daka ku nemi ilimi, don zama da jahilci bashi da amfani, sannan kada ku ce zaku ji haushin mahaifin ku, ku cigaba da yi mishi biyayya koda ya dawo wajen ku, ku kasance cikin yi mishi addu'a Allah yasa ya gane gaskiya, yasan 'ya'ya rahma ne, komai runtsi ina son ka kasance da Suhaima kada ka guje ta, duk laifin da tayi maka kayi hak'uri kai babba ne " D'an dakatawa tayi ta had'iyi yawu sannan ta d'an yamutsa fuska saboda jin yanda marar ta take wani murd'awa wa, cikin kuka Aliyu ya kamo hannun ta yace "A'a Inna baza ki mutu ba, zamu rayu tare da junan mu, don Allah ki daina wannan maganar Inna, hankali na yana tashi wani tunani yana d'arsuwa a zuciya ta sannan gaba na yana fad'uwa " Wani d'an murmishi Fatima tayi tare da cewa "Kayi hak'uri d'ana ni kaina bansan dalilin yi maka wad'annan maganganun ba, ina son duk lokacin da mahaifin ku ya dawo ku sanar dashi na yafe mishi duk abin da yayi min, nima kuma ya yafe ni idan nayi mishi wani laifin a zaman mu, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya raya min ku ya baku ilimi mai amfani ya kuma kare min ku a duk inda kuke 'ya'yana, ku rik'e Babaa Lantana da Baba Adamu a mataayin iyayen ku, don mutanen kirki ne kuma zasu rik'e ku tamkar Aliya 'yar su, duk abin da suka baku shawara kuyi amfani da ita don nasan baza su baku mummunan shawara ba Allah yayi muku albarka " Fatima ta k'arasa fad'in haka tana hawaye sosai, nana Aliyu da Suhaima suka sake fashe wa da kuka sosai, ana cikin Babaa Lantana ta shigo d'akin turus taja ta tsaya ganin su da tayi suna kuka, jikin ta ne yayi sanyi sannn wasu hawaye na tausayin su ya zubo mata, wayance wa tayi tare da fakar idon su don kada su ganta ta goge nata hawayen sannan ta k'arasa inda suke tace "Haba Fatima taya zaki na saka su a gaba kina kuka suna yi, ke da zaki rarrashe su ki kwantar musu da hankali " Murmishin yak'e kawai Fatima tayi, nan Babaa Lantana ta rarrashe su dakyar suka yi shiru, sannan ta basu abincin suka fara ci hannu baka hannu kwarya. Sannan ta d'ago Fatima a hankali ta kara mata kofin madarar shanu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104