Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,179 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wasu abubuwan na fannin boko, ga kuma kwalliya da gayu da take koya mata, saboda Jiddah tana son duk ranar da Suhaima zata gidan su ya kasance ta iya komai na wayewa yanda 'yan uwan ta basu su kyamace mata ko su raina saboda sanin halin su da tayi, sosai Suhaima ta mayar da hankalin ta tana karatu babu wasa, Aliyu ne mai kaita ya kuma d'auko ta daga makaranta yana alfahari da 'yar k'anwar tashi. *** *** *** AFTER SIX YEARS "Suhaima! Suhaima!! Suhaima!!! " Naga wata matashiyar kyakkyawar yarinya chocolate colour tana tsaye a tsakar gida tana kwallawa Suhaima kira, nima gaba d'aya na baza ido na hango fitowar Suhaima don na kwana biyu ban lek'o gidan ba daukan rahoto lol. Wata kyakkyawar yarinya na hango tana fitowa daga d'aki da gudu jikin ta sanye da wata gown ash colour mai touch d'in red a jiki, gashin ta a sake ya kwanta a gadon bayan ta hannun ta na rik'e da veil na gown d'in shima red colour. Da gudu ta k'araso wajen matashiyar yarinyar nan mai kiran ta, tana zuwa ta rungume ta tana dariya ita ma d'ayar dariya take, kafin kuma ta d'an ture ta tana 6ata fuska tace "Ni ai nayi fushi Jiddah da ke ace ranar graduation d'ina ki k'i zuwa koh" Wadda aka kirawo da Jiddah ta langa6e kai tare da cewa "I'm so sorry friend kinsan a time d'in na tafi raka Ammi na london yin check off, nima kaina ban ji dad'in hakan ba please forgive me " Wani kyakkyawan mirmishi Suhaima ta saki wanda ya fallasa dimple d'in ta sannan ta rik'o hannun Jiddah tace "Tsokanar ki nake besty kinsan Yayah Aliyu ya fad'a min " "Yawwa tawan har naji dad'i " Sake rungume juna suka yi suna dariya, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna tsaye suna kallon su sai murmishi suke su ma. A dai dai lokacin kuma driver d'in da ya kawo Jiddah ya fara shigo da kaya yana ajiye wa, sakin juna suka yi sannan a lokacin idanun Jiddah suka sauka akan Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tace "Auuu Yaya Aliyu da Aunty Aliyah daman kuna nan, ai ni ban kula da ku ba " "Daman ina zaki kula damu hankalin ki yana wajen Suhaima " Cewar Aunty Aliyah tana rik'e ha6a, Yaya Aliyu kuwa ban da murmishi babu abin da yake. Langa6e kai tayi cikin shagwa6a ta had'e hannayen ta biyu waje d'aya tare da cewa "Afuwan Babban Yaya da Aunty na bazan k'ara ba " Dariya suka sake yi kafin Suhaima ta rik'e hannun Jiddah taja ta zuwa cikin wata rumfa wanda aka ajiye wasu kujeru na sak'i, zama ake akan su don hutawa, gaba d'ayan su suka zauna ana hira cikin farinciki da annushuwa, kafin daga bisani Jiddah ta d'auko wani kwali ta bud'e sai ga chocolate cake ya bayyana, nan ta ajiye shi saman table d'in da yake ajiye inda suke zaune, sannan ta tashi da sauri ta nufi kitchen. Bata jima ba ta fito hannun ta rik'e da ashana, su dai bin ta da ido kawai suke, tana zuwa ta kunna ashanar ta sanya wutar jikin d'an candle d'in da yake tsakiyar cake d'in wanda ake sanyawa a jikin cake, kamo hannun Suhaima tayi sannan tace "Are you ready? " Gid'a kanta Suhaima tayi fuskar d'auke da murmishi, babu 6ata lokaci suka hure wutar a tare sannan suka yanka cake d'in kowacce ta bawa 'yar uwar ta a baki, sannan Suhaima ta bawa Aliyu ita kuma Jiddah ta bawa Aunty Aliyah. "Happy graduation sister " Rungume Jiddah tayi tare da cewa "thank you so much dear" "Haba never mind 'yar uwa" Daga nan Yaya Aliyu ya fita Aunty Aliyah kuma ta wuce kitchen, sannan Suhaima da Jiddah suka kwashe kayan da ta kawo wa Suhaima suka wuce cikin d'akin Suhaima, kan bed suka zube suna hira don sun jima basu had'u ba. Yinin ranar hira sosai suke har Jiddah na bawa Suhaima labarin an kawo kud'in ta an sanya rana nan da two month's biki su Abban ta suka sanya, da yake kuma Jiddah har ta shiga University tana level 2, mass com take karanta bata da ra'ayin sai ta gama schl zata yi aure, ta fison tana cikin karatun tayi idan yaso zata k'arasa a gidan ta da yake iyayen ta irin basu da shiga hak'ik'in yaran su a kan abin da suke so suna yi musu, sai dai idan abu bai yi musu wannan ne kuma akwai tashin hankali. Suhaima ta taya murna sosai tare da yi mata fatan alkhairi tare da alk'awarin zuwa gidan su biki, d'an hararar ta tayi tare da cewa "Ba daga baki ba fad'ar Allah yasa ki zo " Dariya ce ta tahowa Suhaima da sauri ta sanya hannu ta rufe bakin tana cewa "Ni na isa ace bikin besty guda ban je ba, da ban yiwa kaina adalci ba " "Kada ki zo d'in yarinya kiga yanda ake rashin mutunci " "Ah Ah ma basai kinyi rashin m ba zan zo ba " Daga nan kuma ta fara kok'arin tafiya gida ganin yamma tayi, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sun taya Jiddah murna sosai na auren da zata yi sannan sun yi mata alk'awarin zuwa idan lokacin yayi, sannan tayi musu sallama ta tafi, har wajen mota Suhaima ta rako ta suka sake yin sallama sannan ta shiga motar ta rufe driver yaja motar suka tafi suna d'aga wa junan su hannu, sai da motar ta k'ule Suhaima ta daina hango ta tukunna ta sauke hannun ta tare da sauke numfashi ta wuce cikin gidan su zuciyar ta fal farinciki yau Jiddah tazo don rabon da tazo anyi wajen one month's. *** *** **** Wata hamshak'iyar mata na hango tana rik'e handle d'in kofar wani d'aki tana bud'e wa tare da shiga ciki, kallo d'aya zaka yiwa matar kasan ta jik'u da naira, d'akin duhu dulum da ta shiga ciki. Da yake ta lak'anci wajen makunnar bulbs na bedroom d'in sai ta k'arasa ta kunna nan take haske ya gauraye cikin d'akin, wow nice room na furta lokacin da naga had'uwar d'akin, komai na d'akin blue and white ne hatta fentin bangon d'akin gashi k'ato ne room d'in sosai. Kai tsaye matar wajen tafkeken Italian bed d'in ta nufa, inda one and only lovely son nata yake sleeping hankalin shi kwance, ya lullu6e hatta kanshi da lallausan blanket wanda ya kasance shima blue ne and kwalliyar flower's white ajikin shi. Zama tayi gefen bed d'in tare da sanya hannun ta tana bud'e blanket d'in, har tayi nasarar bud'e face d'in, tubarkallah masha Allah nace a time d'in da na hango beautiful face d'in shi, bacci yake amman fuskar shi a sake tamkar wanda yake murmishi. A hankali ta sanya hannun ta tana bubbuga shi a nutse tana cewa "Hey son wake up " Sai da ta fad'i hakan sau biyu ana ukun ne ya fara bud'e lumshashshun eye's nashi wanda dogayen eyelashes ya rufe su, ya kallo Mummyn tashi cikin muryar shagwa6a yace "Why Mummy da zaki tashe ni a bacci, shiyasa sam ban so na dawo nigeria ba coz yanzu za'a fara sawa mutum headache "

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});