Chapter 54
Chapter 54
cike da shagwa6a, dariya Jiddah tayi kan tace "Toh naji dake da mijin ki bansan wanda yafi wani shagwa6a ba gidan ku da kallo kuwa duk an tara shagwa6a66u" "Yanzu dai tafiya zanyi don my dear yana hanya shi da driven da ya kawo ni, yace ya gaji da yi mishi mitar da nake yak'i zuwa su gaisa da Bestyna shine yau yace zai zo " Murmishi Suhaima tayi kan tace "Allah ya kawo su lafiya" "Amin " Fita Jiddah tayi bata dad'e ba sai gata da Aunty Aliya wadda ta saki baki tana kallon yanda Suhaima ta koma tamkar ba ita ba. Hannu tasa tana shafa hannun Suhaima tace "Wannan da fita kika yi da ita Jiddah da nace wankan inji kika yi mata " Dariya suka yi dukkanin su jin abin da Aunty Aliya ta fad'i. "Aunty kema kiyi don Allah " Cewar Jiddah, rik'e baki tayi tana cewa "A haba wannan ai na irin kune " "Kaiii Aunty aikuwa ya kamata kiyi " Cewar Suhaima. "Suhaima ki had'a mata tayi itama kafin Yah Aliyu ya dawo yaga yanda zata canja idan na dawo zan kar6i tukwicin kyauta ta " Suna nan zaune suna hira har mijin Jiddah yazo, shigowa har gidan yayi suka gaisa da Aunty Aliya da Suhaima bayan an ta6a hira ne suka yi musu sallama suka tafi har k'ofar gida Suhaima ta rako su sannan ta dawo gida bayan sun tafi. Bayan Suhaima ta dawo gida ne ta had'a wa Aunty Aliya itama tayi kamar yanda Jiddah tayi mata, sosai tayi kyau ba laifi bayan angama ne Suhaima tayi wa Aunty Aliya simple make-up tayi kyau kamar ba ita ba sai da Suhaima ta d'auke ta a pic's. Suna zaune tsakar gida suna hira sai ga Yah Aliyu ya dawo nan sauran sallamar mak'alewa tayi a fatar bakin shi ganin yanda matar shi ta koma kamar ba ita ba, kallon ta kawai yake yi don ya mance da wata Suhaima dake zuba mishi sannu da zuwa, duk kunya ta d'an kama Aliyah ganin kallon da yake mata. Yayin da Suhaima ta tattara ta arce d'akin ta don kada taga abin da yafi k'arfin idon ta, dariya k'asa k'asa take don kuwa Yah Aliyu ya bata dariya, phone nata ta d'auko data ta kunna sai gashi Jiddah ta turo mata pic's d'in da ta d'auke ta d'azu, zubawa pics d'in ido tayi ita kanta tasan tayi kyau. *_11:30pm_* Sabeer ne kwance kan bed yana zuba murmishi gama yin wayar shi kenan da Suhaima, duba wajen pic's nashi yayi sam bashi da pic's d'in Babyn shi yana shirin kiranta ne yaji alamar shigowar sak'o a WhatsApp d'in shi don haka ya duba sai yaga Jiddah ce ta turo mishi da wasu pic's guda 5 daga k'asa ta sanya "Yah Sabeer kada ka nunawa Besty na turo maka pic's d'in nan don inason kaga yanda Babyn ka ta zama kuma ka bani tukwici idan ba haka ba na daina turo maka " ta k'arasa da sanya d'an aljanin murgud'a baki, sannan ta kuma cewa "Asha kallo lafiya angon Besty " ta sanya aljanin dariya da gwalo. Tun kafin ya bud'e yake murmishin abin da Jiddah ta rubuta, sakin baki, hanci da ido Sabeer yayi yana ganin pic's d'in sai da ya sake murza eye's nashi kafin ya dad'a zubawa pics d'in ido, wannan anya Baby nace?, ya fad'i haka cikin zuciyar shi kafin maganar ta samu matsugunun tunani a brain nashi tuni ya gama hashasho Babyn shi ce. "Wow! Gaskiya Baby nah kin had'u ashe zan more woo" Ya fad'i hakan yana cigaba da kallon ta tuni ya tafi mafarkin ido biyu, baisan adadin lokacin da ya dauka yana kallon pics d'in ba, sai da yaji Jiddah ta turo mishi da text d'in taji shiru bata ga tukwicin ta ba. Cikin rawar jiki ya fara typing da cewa "Me kike so k'anwata ta kaina? " "Yah Sabeer komai ma " "Car or Money wanne kike so fad'i?" "Yah Sabeer Mota nake sooo" "Angama sister gobe za'a kawo miki key " Wani ihun murna Jiddah ta saki har phone nata na fad'uwa k'asa don tasan kyautar Sabeer baya k'arama, nan tayi mishi godiya tare da addu'ar Allah ya bashi Suhaima, na takaice muku Sabeer ranar har dasu mafarkin Suhaima suna tare don da asuba sai da Sabeer yayi wanka sannan ya iya yin sallah..... lol. *_Washe gari_* Sabeer ne ya fito daga bedroom d'in shi yana taka staircase anutse ya kusan k'arasa wa palour ne ya hango Mummy da Daddy zaune ga kayan bag's na akwatinan lefe nan barbaje a palourn tun daga kan akwatunan mutum zaisan basu da wani tsada ko kalar kyau basu dashi gashi guda 6 ne gaba d'aya kayan ciki kuwa ko arzik'in kyau basu dashi. K'arasa wa yayi cikin palourn yana kallon kayan a wulak'anci yace "Daddy Mumy kayan wane ne wannan?" "Nima jira nake ta sanar dashi bansan na wane ne ba nafi kyautata zaton ko gate man ne zaiyi aure ta bashi kyautar su " Cewar Daddy kenan, duk sun zubawa Mumy ido suna sauraren abin da zata ce dasu......... *_Ya kuka ji wannan page d'in Fans dafatan ya k'ayatar ku, inason ganin comment's, yau nayi abin kirki koh?_*😜 Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/25, 8:09 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 75-76* Ganin Mumy tayi shiru tak'i magana yasa Sabeer yin magana cikin k'aguwa yace "Mumy ke fah muke jira ki fad'a mana ki zo ki bani abinci yunwa nake ji " Hankalin Mumy kwance ta bud'e baki tace "Lefen da Daddy yace na had'a ne sune na gama had'a wa " Cikin son sanin na waye Sabeer yace "Na wane kodai gaskiyar Daddy ne gateman ne zai yi aure?" Yayin da Daddy kuma ya saki baki yana kallon Mumy zuwa yanzu ya tabbatar lefen Sabeer ne da yace ta had'a shine ta had'a mishi wulak'antaccen kayan nan da ko wani talakan mai zuciyar nema idan ya sanya kanshi sai ya had'a wanda yafi shi had'uwa, ranshi ne ya soma 6aci yama kasa magana sai kallon mamaki da yake bin ta dashi,yana jiran yaji me Sabeer zaice kafin shima ya d'ora hukuncin da zaiyi don sosai wannan karon Mumy ta 6ata mishi rai, yana cikin wannan tunanin ne yaji muryar ta tana cewa Sabeer. "Lefen auren ka ne da wannan talakar yarinyar 'yar k'auye don nasan sun fi dacewa da ita kuma zata kar6a su cikin murna don basu saba ganin irin su ba" Wata 'yar dariyar ban yarda ba Sabeer yayi kan yace " are you serious Mumy maganar ki nasan da wasa ne ai? " "Sabeer kadaina sanya wasa cikin maganar nan da gaske nake duk abin da nace " Wata dariyar Sabeer yayi wadda tafi kuka ciwo yace "Yayi kyau Mumy " Ya fad'i hakan yana barin parlourn cikin 6acin rai da taiaicin abin da Mumy tayi na niyyar wulak'anta shi yake hawa staircase d'in da sassarfa, bedroom nashi ya nufa yana shiga ciki ya bud'e tafkeken wardrobe nashi ya fara watso kayan ciki yana barbaza su a ko'ina, shi Mumy take neman wulak'antawa saboda kawai yana son d'iyar talakawa wadda ta rayu a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104