Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,182 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

k'auye. "Why Mumy why shi talakan ba mutum bane, ba Allah ne yayi shi ba yaso ganin shi haka a rayuwa ba, Mumy kada k'ureni muzo muna yin abin da kowa zai yi nadama " Wani 'yar k'arar takaici ya saki yana sanya hannun shi cikin sumar kanshi wadda tasha gyara yana hargitsawa, can kuma kamar wanda aka mintsina ya mik'e zumbur ya fara cire kayan jikin shi ya canja da wasu jeans black da T-shirt maroon colour mai k'aramin hannu ya d'auko phone da car key's ya fito daga d'akin. Yana saukowa daga upstairs yaji muryar Daddy yana yiwa Mumy fad'a sosai akan abin da ta aikata, suna ganin sai kuma suka dawo da hankalin su nan, cikin damuwa Mumy ta fara cewa "Son ina zuwa baka ce min yunwa kake ji ba, ga breakfast fah na had'a maka favourite foods naka? " "Bana buk'atar su " Sabeer ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba ya k'arasa wajen Daddy yana cewa "Daddy zan fita " Rik'o hannun shi Daddy yayi tare da cewa "Ina zaka Son? " "Daddy zan je na nemi mai had'a min lefe wanda nasan baza su so na kunyata a rayuwata ba " "Da kyau Son but da ka nemi Jiddah da Yusrah (Yayar Jiddah wadda take bi itama dai bata da tsaurarawa sosai akan abu wanda ya danganci talaka tana da aure har da yara 2), nasan zasu fitar da kai kunya baza su so kansu ba da yawa, kamar wasu mutanen da basu d'auki talaka a mutum mai mahimmanci ba, wanda kuma agaba zai iyayi mishi wani abin alkhairi mutum ya dawo yana jin kunyar aikata abin da yayi" Mumy ta cika tayi fam sai huci take don tasan da ita yake don tuni ta tsargu. Sai lokacin hankalin Sabeer ya d'an kwanta don dama shi baisan wurin da zai je ba kawai ya fito da niyyar barin gidan ko yaji sanyi cikin ranshi. "Yanzu Daddy wanne k'asa zasu je? " "Ina tunanin su je dubai su had'a acan idan ma bai wadatar ba sai a dad'a neman wata k'asan, yanzu zan kirawo mazajen su na rok'i wannan alfamar a wajen su, ka kwantar da hankalin ka Son " Rungume shi Sabeer yayi cikin jin dad'i yace "Nagode Daddy nah hak'ik'a kai uba ne na gari wanda yake faranta ran d'an shi koda yaushe Allah ya barmin kai " "Amin Son nima ina alfahari da kai " Yana gama fad'in haka yaja hannun Sabeer suka fita daga side d'in, suka bar Mumy da baki a sake tana mai bin su da kallo cikin mamakin gasa mata maganar da suka yi sannan suka fitar mata da waje ko sallama babu gashi ba wanda yayi breakfast a cikin su, kuma saboda su ta shiga kitchen ta tsara girki shine suka watsa mata k'asa a ido, zubewa tayi kan kujera tana faman kallon kayan da ta sanya house girl d'inta ta had'a su, da yake er aikin dattijuwa ce kuma er k'auye ce sosai sai tace ta had'a mata lefe kamar yanda suke had'awa a k'auyen su, amman irin wanda mai kud'in k'auye zai iya had'awa amman sai tace mata akwatina 6 zata siya shine fah ta had'o kayan, ko lokacin da ta gansu sai da taci dariya ta more saboda abubuwan da aka zuba aciki. D'an ta6e baki tayi kan tace "Ni ban ga wulak'anci anan ba nasan da gudu zasu kar6a suna murna tun da basu saba ganin kayan lefe masu yawa irin wannan ba" Ta k'arasa fad'i tana kwanciya kan kujera wata tsanar Suhaima na k'ara shiga cikin zuciyar ta,tun kafin taga yarinya take jin tsanar ta kuma tabbas sai tayi nadamar auren d'anta don bazata barta tayi rayuwa cikin jin dad'i ba, (kun ji tunanin Mumy fah sai kace itace mai tsarawa mutum rayuwar shi). Tun da Sabeer da Daddy suka bar gidan basu dawo ba sai wurin 11 na dare suka shigo part d'in, tun after sallahr ishsha suke cikin gidan ba tare da Mumy ta sani ba don ko dinner a Muh'd part d'in Hajjah suka yi, Mumy kuwa batasan sun dawo gidan ba don haka ta k'ule iyakar k'uluwa akan abin da Sabeer da Daddy suka yi mata don ko abincin dare da kanta ta shiga kitchen ta 6ata lokaci sosai wajen shirya musu abinci, tun tana zuba idanun ganin su har ta hak'ura ta kwanta kan kujera 3 siter tana sak'a da warwara ina mijin ta da d'anta suka yi. Tana cikin wannan tunanin ne taji shigowar su palon don haka ta mik'e tana kallon su cikin mamaki yanda suke ta zuba fara'a abin su Daddy ya rik'o kafad'ar Sabeer tamkar wani abokin shi. Kanta ne ya k'ara d'aurewa ganin zasu shige upstairs basu kulata ba, yanda ma suka nuna ko alamun sun san da ita a palon basu yi ba, kasa jurewa tayi don haka tace "Hala baku kula da ni ba, ina kuka zauna har wajen 11pm baku dawo gida ba? " Tsayawa suka yi tare da juyowa suka had'a ido lokaci d'aya suka had'e fuska sannan Daddy yace "Ina ruwan ki da inda muka je wannan ba matsalar ki bace? " Gaban Mumy ne ya fad'i kaddai ace adalilin Suhaima mijinta da d'anta su juya mata baya, ganin har sun fara taka staircase ya sanya ta katse tunanin ta da sauri tace "Ga abinci nan fah na girka muku " "Mun koshi Mumy wata k'awar Daddy ta bamu abinci mai dad'i mun ci don haka ki bawa masu aiki su ci " Cewar Sabeer kenan wanda sauran kad'an dariya ta kubce musu shi da Daddy don haka da sauri suka fad'a bedroom na Sabeer suka rufe suna kyalkyala dariya, har da rufe baki da hannun su saboda kada Mumy ta jiyo sautin dariyar tasu. "Son ka razana Mumyn ka da yawa fah kada wani abu ya samu mata ta ina jin tsoro " "Haba Daddy daga wannan maganar sai wani abu ya faru da ita? " "Eh mana Sabeer kasan yanda Mumyn ka take da kishi kuwa ni bama zan jure ganin ta cikin damuwa ba bari naje na rarrashi abata " Daddy ya k'arasa fad'a yana kokarin fita a d'akin, da sauri Sabeer ya rik'o hannun shi tare da cewa "Nooo Daddy kyale Mumyn nan, nima kaina bana son ganin ta cikin damuwa but Mum batason ganin farincikina i swear" "Kada kace haka Son nasan nan gaba zata so Suhaima " "Anya kuwa Daddy, na fahimci Mum ta gama tsanar Suhaima " "Kada kace haka Son addu'a zaka cigaba da ni " Gid'a kai Sabeer yayi kafin kuma su zauna suna hira akan tafiyar da su Jiddah da Yusrah zasu yi nan da gobe da yamma jirgin su zai tashi zuwa dubai, kafin daga bisani Daddy ya wuce side d'in shi don dare ya d'an yi. Mumy kuwa tun lokacin da maganar Sabeer tayi mata dirar mikiya cikin kunnen ta, ta gama firgicewa kusan suman tsaye tayi tsabar kad'uwa da jin abin da Sabeer ya fad'a mata, wato dalilin da ya sanya su yin dare a waje kenan, aikuwa ba 'yar iskar da zata shigo gidan nan matsayin matar Hussein wallahi duk wadda tayi gigin shigowa kuwa sai tayi dana

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});