Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 86

Chapter 86

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,173 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tukunna " Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin. Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin. Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su. "Lek'en me kike har kina yin tuntu6e " Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen don d'auko abin karyar ta tana cewa "Ni babu abin da nake kallo fah Aunty " Murmishi kawai Aunty Aliyah tayi, fitowa tayi daga kitchen ta zauna kusa da ita tana kok'arin zuba kunun tsamiya a cup tace "Aunty ina Yaya ne? " "Ya tafi makaranta yana da lecture d'in safe gashi zasu yi test ma " Suhaima tana bud'e wani k'aramin flaks wanda kosai yake ciki tace "Ayyah Allah ya taimaki Yayana " "Amin " Cewar Aliyah tana murmishi, kafin kuma tayi bismillah ta fara cin abincin cikin nutsuwa bayan ta gama ta wanke hannun ta tana kok'arin d'auke kayan da ta karya dasu don ta kaisu kitchen Aunty Aliyah tace "Bar wannan aikin Suhaima ki rik'e min Ameer don kuwa sauri nake son yi " Shagwa6e fuska Suhaima tayi kan ta ce "Kaiii Aunty nima fah na iya wannan saurin gashi ke kadai kika had'a abin kari " "Ni na isa na fad'i hakan ke dai zo ki rik'e min shi idan ba haka ba yana wannan rarrafen nashi zai hanani saurin aiki " D'aukan Ameer tayi tana cillashi tare da cafe shi tana dariyar shima Ameer d'in dariyar yake mata da 'yan hak'oran shi, tana cikin haka ne taji tsayuwar mutum akanta da sauri ta d'ago kanta ido 4 tayi da Sabeer wanda yake tsaye ya hard'e hannun shi yana kallon ta cike da so da tarin sha'awarta don sosai ta birgeshi ji yake kamar ya kamota ya gudu da ita, d'auke kanta Suhaima tayi daga barin kallon shi ta cigaba da yiwa Ameer wasa amman jikinta ya bata har yanzu bai tafi ba kallonta yake lokaci d'aya taji wata kasala ta lullu6e ta har takai ta kasa d'aga Ameer sama sai kawai wasan da take mishi. Fitowar Aunty Aliyah daga kitchen ne ya sanya shi katse kallonta, kallon shi Aliyah tayi kafin ta girgiza kanta ganin lokaci d'aya ya rame gashi kayan shi sunyi datti sosai tace "Sabeer kana buk'atar wani abun ne? " Cikin dashashshiyar muryar shi wadda mura tayi mishi mugun kamu yace "Auntyn mu wanka nake son yi sannan ina son bak'in tea da lemon tsami aciki " "To amman wannan murar taka ko chemist zaka je kada ta ssukar maka da zazza6i " Cikin murmishin yak'e yace "A'a basai naje ba zata warke " "Anya kuwa Sabeer za'a yi haka kada fa ta baka matsala? " "Auntyn mu kada ki damu zata warke nagode da kulawar ki, wadda ya kamata ta nuna damuwa akan ciwon bata damu ba sai ke don haka ki share zancen zuwa chemist " Da sauri Suhaima ta d'ago kanta ta kalli shi har zata yi magana kuma sai kawai ta d'auke kanta tana murgud'a baki, duk abin da take yi akan idanun Sabeer, yayin da Aunty Aliyah tace "Yanzu sai kayi wankan zaka sha tea d'in? " "Eh " Ya fad'i a takaice "Ka shiga d'akin Suhaima akwai toilet aciki sai kayi wankan ka aciki " Daga Suhaima har Sabeer da sauri suka d'aga kansu tare da kallon Aliyah, gid'a kanta tayi sanann tace "Kada ka damu kaje kayi " "Aunty amman...... " Cewar Suhaima sai dai bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba taja bakin ta tayi shiru ta had'e fuska. "Aunty nayi kawai a wannan toilet d'in " "A'a bazai yiwu ba, Suhaima kije ki had'a mishi ruwa nace idan har na isa na sanyaki abu kiyi " Tashi Suhaima tayi tana 6a66ata rai zata wuce d'aki taji tana cewa "Dawo ki d'ebi ruwan zafi tun da garin da d'an sanyi gashi yana fama da mura ". Kitchen ta shiga ta d'ebo ruwan zafi ta wuce d'akin ta tana cika tana batsewa don me Aunty Aliyah zata ce yayi wanka a d'akin ta, ko ta mance da irin yanda ya koreta daga gidan shi ne. "Auntyn mu 6atawa Baby nah rai fah? " Ya fad'i hakan bayan wucewar Suhaima. "Kyaleta Sabeer sakkowar Suhaima daga fushin da take da kai shi zai sanya Yayan ta ya huci daga d'aukan zafin da yayi maka, kai dai kayi kok'arin shawo kan Suhaima " Gid'a kanshi yayi kan ya wuce zuwa zaure ya d'auko bag d'in kayan shi ya wuce d'akin Suhaima, yayin da Aunty Aliyah ta cigaba da aikinta bayan ta goya Ameer. Yana shiga cikin d'akin wani k'amshi ne ya fara mishi sallama mai dad'i har sai da ya lumshe eyes nashi, tsayawa yayi yana kallon d'akin cike da sha'awar shi yayi mishi kyau duk da ba wasu kaya ne masu tsada ba sosai amman yanayin yanda aka tsara d'akin ne ya birge shi, daga gado, wardrobe sai dressing mirror k'asan kuma carpet ne sai kayan kallo gashi d'akin babba ne sai labulaye masu kyan tsari gadon nan an gyarashi sosai tamkar ba'a ta6a kwanciya akan shi ba. Yana nan tsaye Suhaima ta fito daga toilet d'in ba tare da ta kalli inda yake ba ta fara kok'arin fita daga d'akin, hannun ta ya rik'o cikin sanyin murya yace "Baby nah kiyi hak'uri please ki daina fushi da ni " Bata ko kalle shi ba ta fara zame hannunta daga nashi sannan ta fice daga d'akin, da kallo ya bita kafin kuma ya nufi hanyar da ta fito ya shige toilet d'in. Suhaima tana tsaye kusa da Aunty Aliyah tana mata mitar yanda ta sanya Sabeer shigar mata d'aki, yayin da Aunty Aliyah take murmishi kawai yaro yaro ne idan ban da haka yaci ace ta yafewa Sabeer don ita kanta Suhaima ya kamata ta baiwa Sabeer shaidar yanda yake nuna mata so da kulawa abu ne ya gifta a tsakanin su wanda mak'iyan su da basa son su gansu tare suka yi amfani da abin da Sabeer yafi so suka had'a makirci shi kuma laifin shi d'aya da ya biyewa zuciyar shi ya yanke hukunci cikin fushi sai dai kuma yayi kok'arin controlling din zuciyar shi tun da bai sake ta ba. Sallamar da suka ji anyi ne ya sanya Suhaima da Aliyah zabura gaban su ya hau fad'uwa lokaci d'aya kafin su ankare ya shigo gidan, kallon su ya tsaya yi cikin mamaki ganin yanda suka zuba mishi ido kallo d'aya yayi musu yasan basu da gaskiya. Tsarguwar da suka

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});