Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 40

Chapter 40

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,186 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shigowa mutane gida kai tsaye tun kafin a amsa mishi sallamar a bashi izinin shigowa sai kace a gidan arna " D'an murmishi yayi yana girgiza kai don yaji ta tsaf sai kawai ya tashi ya koma zaure sannan yayi sallama mamaki sosai Suhaima taji da taji ya koma sai da ta d'an jima kafin ta amsa mishi sallamar sannan ya shigo yaja kujera ya zauna lokacin har ta gama yankan salad d'in. Shiru taji bai yi magana ba sai ta d'an d'ago kad'an ta kalleshi duk ya rame yayi d'an bak'i kad'an kamar ba Sabeer ba, gani tayi zai kallo inda take ya sanya ta kauda idonta da sauri zata tashi kenan taji muryar shi cikin sanyi yace "Baby taimaka min da abinci I'm very hungry wallahi please " Yi tayi kamar bata ji shi ba ta wuce kitchen kafin ta fito ta wanke salad d'in duk yana kallon ta don tayi mishi kyau cikin wata gown ta atampha duk da basu kamata ba d'inkin amman sun zauna cif a jikin ji yake kamar ya sanyata cikin jikin shi ya dunga fad'a mata irin son da yake mata ko ya samu sassaucin da yake ciki. Ya fad'a dogon tunani yana yi yaji kamshin turaren Suhaima a kanshi da sauri ya d'ago kanshi ya kalle ta tana tsaye hannun ta d'auke da plate na abinci tana mik'a mishi, hannun shi ya sanya ya kar6a hadda ta6o mata 'yan yatsun ta saboda tsokana yak'i kar6ar plate d'in aikuwa wani irin shock Suhaima taji ajikinta wanda bata ta6a jin irin shi ba da sauri ta saki plate d'in nan yayi saurin tarewa yana sakin murmishi ganin irin yanayin da ta shiga ajiye abincin yayi yana kallon shi shinkafa da wake ne sai salad da mai da yaji gefe d'aya a saman abincin ga kifi nan an sanya sosai abincin ya bashi sha'awa. "Uhm sauran ruwa Baby " Ya fad'i hakan a lokacin da Suhaima take kok'arin shiga d'akin ta ta huta don ta gaji tun safe take aiki, haushi ne yake kamata tun lokacin da Sabeer ya koyi ce mata Baby kuma ko a gaban su Yaya Aliyu haka yake fad'a mata, komawa tayi kitchen ta samu jug k'arami mai murfi ta d'ebo mishi na randa mai sanyi ta kawo ta dangwarar mishi a gaban shi. "Sannun ki Baby nah Allah ya bani ke " Ko kallon shi bata yi ba ta juya ta wuce d'aki sai kawai taji zuciyar ta tak'i aminta ta furta ba Amin ba daga addu'ar da Sabeer yayi. Cikin kwanciyar hankali ya fara cin abincin yayi mishi dad'i sai dai ko rabi bai ci ba ya ture shi saboda yayi mishi yawa yasan da gayya ta zubo mishi da yawa, yana nan zaune ya fara jiyo muryar Aliyah k'asa k'asa tana kiran Suhaima daman yinin yau a d'aki ta yini bata jin dad'in jikinta. Jin wannan kiran yasan Suhaima bazata ji ba ya sanya shi tashi ya nufi d'akin Suhaima ya shiga ba tare da neman izinin ta ba tana kwance saman bed tayi kwanciyar ringingine tana duba littafin addu'o'i. Tsayawa kallonta kawai ya tsaya yi don wannan kwanciyar ba k'aramin sanya shi a wani yanayi na daban, Suhaima ji take kamar ana kallon ta sai ta kawar da littafin daga saitin fuskar ta fuska a d'aure tace "Malam lafiya zaka shigo min d'aki ba neman izinin? " D'an sosa kai yayi kafin yace "Aunty Aliyah tana kiran ki " Yana gama fad'in haka ya fita, d'an tsaki taja kafin ta mik'e ta fita d'akin Aliyah ta shiga sai ta tarar da ita cikin wani hali don nak'uda ce ganga ganga ta taho mata da sauri ta k'arasa inda take durk'ushe ta rik'o ta tana kuka. Sabeer zai fita kenan yaji kukan Suhaima nan ya fara kiran sunan ta hankalin tashe gashi bashi da damar shiga d'akin, nan Aliyah dakyar ta fad'awa Suhaima taje ta kirawo mata Babaa Lantana. Tana fitowa taci karo da Sabeer wanda yake tsaye a bakin k'ofar hankalin shi a tashe kamar ya fad'a d'akin haka yake jin shi. Ganin Suhaima zata fita yasa shu rik'o hannun ta yace "Baby what wrong with U? " Kamar ta share shi sai kuma tace "Aunty ce zata haihu tana shan wahala " "Innalillahi bari naje na kirawo Yaya da Babaa Lantana ki zauna kusa da ita " Da sauri ya juya ya fita yayin da Suhaima ta koma cikin d'akin, babu dad'e wa da fitar shi sai ga Babaa Lantana da Aliyu sun shigo gidan tare da Sabeer nan suka shiga cikin d'akin ban da Sabeer wanda yake tsaye zuciyar fal tausayin Aliyah. Yana nan tsaye Suhaima ta fito tana kuka da Aliyu wanda idanun shi suka yi ja na tausayin halin da matar shi take ciki akabar Babaa Lantana a cikin d'akin "Ya kamata mu tafi hospital " Cewar Sabeer da ya matso kusa da Yaya Aliyu, d'an girgiza kai Aliyu yayi kafin ya bud'e baki yayi magana sun ji kukan jariri. "Alhamdullilah " Suka furta gaba d'aya suna nan tsaye Babaa Lantana ta fito fuskarta d'auke da farinciki tace "An sauka lafiya mun samu namiji " Nan fuskar su ta fad'ad'a da fara'ar farinciki, Suhaima mai kuka ta dawo dariya har da buga tsallen murna ta rungume Yayanta, kallon su Sabeer yake cike da sha'awa daman shima yana da k'anwa ko Yaya wanda suka fito ciki d'aya da shima ya nuna mishi irin son da yaga Aliyu da Suhaima da suke yiwa junan su. Suhaima ruwa ta d'ora kan wuta bayan ta hura itace bayan yayi zafi ne ta kwashe takai toilet sannan ta d'ebo wanda za'a yiwa jariri wanka ta kai d'akin Aliyah inda har Babaa Lantana ta gyara ko'ina fes ta sanya turaren wuta na kamshin d'akin. "Sannu Aunty Aliya " Suhaima ta furta tana rik'o hannunta fuskarta d'auke da murmishi, "Yawwa kanwata ke ma sannun ki " Kamata Babaa Lantana tayi ta kaita band'aki wanka tayi mata suka fito sannan tayi wa jariri lokacin da suka gama tsaf suka shirya sai ga Yaya Aliyu nan da taxi ya taro zasu je asibitin da Jiddah ta kaisu lokacin tana laulayin ciki. Suka tafi aka bar iya Suhaima a gidan tana dad'a gyarawa, bayan ta gama ne sai tayi wanka ita ma ta fito d'aure da zanin wanka ko hijab bata sanya ba da yake tasan a tunaninta Sabeer ya bi su hospital ne. Tsayawa tayi bayan ta fito daga wankan tana taje dogon gashin kanta ta sunkuyar da kan gashin yayi gaba tana taje shi, bayan ta gama irin ta d'ago kanta gashin yayi baya sai a fuskar Sabeer wanda shigowar shi kenan gidan, ya hango ta tana taje kanta. "Wash! kin sanya min gashi a ido da bakina fah" A d'an tsorace Suhaima ta jiyo jin muryar Sabeer a kusa da ita, suna had'a ido nan gabanta ya hau fad'uwa ganin irin kallon da yake jifanta dashi idanun shi har sun fara canja launi, na shiga uku ni Suhaima daman wannan mutumin bai bi su ba, ta fad'i hakan cikin zuciyar ta tana mai ja da baya shima yana bin ta da haka har bayanta ya jingina da bangon d'akin ta sai kawai ta runtse ido tare da k'ank'ame jikinta

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});