Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da Allah ya toni asirin munafuka" Cewar Mumy kenan tana jijjiga kafa hatta Daddy mamaki ne ya hanashi magana. "Yaya wallahi Suhaima bazata aikata haka ba " Cewar Jiddah tana faman kuka kamar zata shid'e, cikin 6acin rai yace "Jiddah close your mouth or I'll slap U wallahi " Juyowa yayi wajen Suhaima tare da cewa "Nagode Suhaima akan duk abin da kika yi min wannan shine sakayyar da zaki min A SANADIN SON KI mene banyi ba nayi fad'a da family na iyayena na bar inda suke na tafi wajen ki nasha wahala kafin ki kar6i soyayya ta ashe duk kallon wawa kike min bansan me nake ba, kin zubar min da cikin jikin ki sau biyu nasan baki sona dama don haka get out from my house i hate you Suhaima i hate you so much nasan bazan yi regretting wannan abin da nayi ba kuma da sannu Allah zai saka min " Yana gama fad'in ya nufi upstairs zuciyar shi na wani irin zafi, tashi Suhaima tayi tana faman kukan tashin hankali zata fita daga parlour tabar gidan taji muryar Daddy yana cewa "Suhaima kada ki tafi zansa ayi bincike ban yarda da wannan abun ba" Girgiza kai take tana cewa "A'a Daddy kabar na tafi bazan zauna ba " Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan da gudu tana kuka, Jiddah ce tayi kok'arin bin ta amman Mumy ta rik'e ta gam tana faman hararar ta.................. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/11, 11:38 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 93-94* Suhaima gudu take tana kuka har ta samu ta fito daga gidan, sannan ta d'an tsaya tana yiwa gidan kallon k'arshe don tasan bazata ta6a komawa cikin shi ba har abada kuwa. Fara tafiya tayi tana goge hawaye da hijab d'in jikinta ko takalmi babu a k'afar ta, wani mai taxi taga ya sauke wata mata bata tsaya tambayar shi ta fad'a cikin motar tana kuka kawai, daga matar har mai taxi d'in suka bita da kallo kowanne fuskar shi ta d'auki alhini suna tunanin ko mutuwa akayi mata mai zafi yasanya ta haka dad'in dad'awa da suka ga ko takalmi babu a k'afar nata, canjin matar mai taxi ya bata sannan ya tada motar suka fara tafiya sai da suka hau kan titi sannan yace "Baiwar Allah ina zan kai ki? " Dakyar ta iya tsayar da kukan tayiwa mai taxi bayanin inda zai kaita, mai taxi bai zaci wajen da nisa ba sai da ta fad'a mishi sunan kauyen da zai kaita yaso yi mata maganar ba nan zai je ba but ganin irin halin da take ciki ne kawa yayi niyyar taimaka mata. ***** "Faridah ina jiye miki duk ranar da gaskiya tayi halinta, idan har da sanya hannun ki cikin wannan abun to kiyi gaggawar warwarewa tun kafin kizo kina nadama " Turo baki tayi kan tace "Wai ni duk kun tattara laifi akaina ina ruwana da ita da har zanyi yunkurin zubar mata da ciki kawai ta samu sake ne kasan halin talakan mutum bai iya samun waje ba, kuma nagodewa Allah da ya sanya suka rabu da d'ana yaje ya auri wadda zata haifa min 'yan jikoki na, yanzu kawai saki nake so naji yayi mata yanda zasu rabu har abada" "Allah ya shirya ki Faridah " Cikin wani irin murmishi tace "Amin my Dear " Tashi Daddy yayi zai fita itama ta mik'e tana cewa "My Dear ka tsaya mu tafi da Son mana kada mu tafi mu barshi shi d'aya " Cikin jin haushin abin da Sabeer yayi wa Suhaima tunda bai tsaya yayi bincike ba kawai ya yanke hukunci yace "Ai ba yaro bane shi kuma yasan hanyar gida " Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita daga palon, Jiddah ma d'aukan Islam tayi ta wuce da sauri ta bi bayan Daddy da harara Dr Faridah ta bita tukunna ta wuce upstairs inda Sabeer yake. Agefen gado ta ganshi yayi ruf da jiki rabin jikin shi a saman bed rabin a k'asa sai wani irin shashshak'a yayi na kuka idanun nashi sunyi ja sun kumbura hatta face nashi tayi ja sai maimaita kalmar "Why! Why! Suhaima zaki yi min haka na tsane ki i hate U " . wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Dr Faridah jin yanda Sabeer yake furta ya tsani Suhaima kamar tayi tsalle da ihun murna haka take ji amman sai ta danne, zama tayi akan gadon ta tare da d'aukan kanshi ta d'ora kan k'afafun ta shafa mishi gashin kanshi take a hankali tana rarrashin shi but still Sabeer eyes nashi basu bar zubar da tears ba. "My Son kayi hak'uri mu tafi gida kaji bazan iya barin ka anan kai d'aya ba " "No! Mumy ki tafi ki barni zuciya ta yana daf da tarwatse wa, ina jin zafi acikin zuciya na idan na tuna Suhaima ta cuce ni taci amanata ta yaudare ni tayi min butulci Mumy! " Dafe saitin zuciyar shi yayi da hannun shi d'aya yana jan wani irin numfashi, wani irin zabura Dr Faridah tayi ganin yanda eyes d'in Sabeer suka kakkafe. Hannu ta d'ora saman kanta tana kuka tace "Wayyo Allah nah na shiga uku zan kashe d'ana da kaina! " ****** Sai bayan sallahr ishsha ne suka k'arasa kauyen su Suhaima har k'ofar gida mai taxi ya kaita har zuwa yanzu Suhaima bata bar kukan bak'inciki da takaicin hukuncin da Sabeer ya yanke ba batare da bincike ba aure ko shekara baiyi ba ace har an rabu daman ashe ba sonta yake tsakani da Allah ba yaudare ce yake mata irin ta mazan yanzu nima na tsane ka kamar yanda ka tsane ni Sabeer!. Maganar da d'an taxi yake mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani fitowa tayi daga motar cikin dushewar murya tace "Bari na kar6o maka kud'in ka " Ko taku uku bata yi ba taji ta bige mutum d'agowar da kanta da zatayi suka had'a ido da Yah Aliyu cikin tsakanin mamaki yace "Suhaima! " ai Suhaima batasan lokacin da ta fad'a jikin shi ba ta saki wani irin marayan kuka, wani irin tashin hankali da fad'uwar gaba ne ya ziyarci Yah Aliyu tuni fuskar shi ta fara canja yanayi. "Yay... Yaya ka biyashi kud.... kud'in shi " Ta fad'a cikin kuka tana nuna mai taxi da hannun ta, zuciyar Yah Aliyu tana tafasa yace "Malam nawa ne kud'in ka? " Nan d'an taxi d'in ya fad'a hannu Yah Aliyu ya zura a aljihu ya d'auko kud'in shi ya bashi yana bashi ya rik'o hannun Suhaima suka shiga cikin gida. Aunty Aliyah da take zaune tana jijjiga Ameer yayi bacci taga shigowar mijin nata batasan lokacin da ta kwantar da Ameer saman katifa ba ta mik'e a razane tana cewa "Suhaima kece da daren nan? " Jikinta Suhaima ta fad'a tare da fashewa da kuka da k'arfi, ruwa Yah Aliyu ya d'ebo mai sanyi a randa zama yayi tare da zaunar da Suhaima akusa da shi ya bata ruwan da hannun shi, bayan ya gama bata ne sannan cikin nutsuwa yace "Suhaima fad'a min me yafaru kada ki 6oye

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});