Chapter 72
Chapter 72
fara yayyafi suka tafi gida, bayan sun je gida Suhaima tana yin wanka wani zazza6i mai zafi ya rufe ta sosai da ciwon kai sai kuma amai sosai ranar basu iyayin baccin kirki ba saboda yanda jikinta ya rikice sosai don Sabeer ba k'aramin tsorata yayi da jikin ba. Washe gari da safe ya kirawo Dr Aishat don ta dubata, babu jimawa tazo tayi mata gwaje gwaje nan ta hango ciki d'an wata 2 ajikin Suhaima sai kuma damuwar da ta saukar mata da zazza6i, ganin yanda ta gala6aita ne ya sanyata sa mata drip don taji kwarin jikinta sannan tayi mata allurar bacci. Nan tayiwa Sabeer albishir d'in cikin jikin Suhaima, dad'i da farinciki ne ya rufe Sabeer saboda tsakanin murna sai da yayiwa Dr Aishat kyautar mota, dad'i ya ishe shi Dr Aishat nan tayi ta zuba godiya da addu'a sannan tace da zarar Suhaima ta farka ya kirawo ta awaya tukunna ta tafi, Sabeer ya koma d'akin Suhaima kallon ta yake kawai wata zazzafar kaunar Suhaima take sake mamaye cikin zuciyar shi sai shafa cikinta yake Daddy ya iya kira yayi mishi albishir sosai Daddy ya nuna murnar shi. *** **** **** Dr Faridah ce zaune a katafaren office d'in ta sai jujjuyawa take cikin kujera idanun ta a lumshe, turo kofar akayi tare da shigowa. Bata bud'e ido ba taba da umarnin azauna, wadda ta shigo ce ta zauna kan kujera kanta sunkuye tana jiran abin da Dr Faridah zata ce. "Dr Aishat ina kika je bakizo office akan time ba? " Cikin girmama wa tace "Ranki ya dad'e naji gidan Yalla6ai Sabeer ne duba matar shi bata jin dad'i " "Okay me ya same ta " Cikin fara'a Dr Aishat tace "Ai abin farinciki ne ya same mu Doctor don Matar shi ciki ne da ita har tsayin 2 months " Wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki mutum ya zaci murmishin farinciki ta saki har da wani cewa "Masha Allah Dr Aishat naji dad'i sosai da wannan albishir d'in " Bud'e bag nata tayi ta d'auko kud'in da batasan adadin su ba ta mik'awa Dr Aishat tace "Ga nawa tukuicin " Kar6a Dr Aishat tayi cikin fara'a tace "Kaiii wannan d'a da farinjini yake tun kafin yazo duniya nake samu alkhairi yanzu Yalla6ai fah ya bani kyautar mota " "Babu komai zaki iya tafiya " Tashi tayi tana godiya ta fice daga office d'in, wata shegiyar dariya Dr Faridah ta saki tare da cewa "Lokaci na yayi dole cikin nan ya zube ta kowanne hali " *** **** **** Bayan ta tashi daga bacci ne Sabeer yayi mata wanka tare da bata tea ta d'an sha kad'an da maganin da Dr Aishat ta bata, sannan ya kirawo Dr Aishat ya fad'a mata ta farka babu 6ata lokaci tazo ta sake dubata tare da bata shawarwarin yanda zata kula da kanta daga nan tayi musu sallama ta tafi. Kulawa sosai Sabeer yake bawa Suhaima don haka cikin kwana 2 ta d'an warware tunda cikin ba mai laulayi bane, tana cin abinci babu laifi, sai dai baccin da yake damunta don sai ta yini tana bacci ganin haka ya sanya Sabeer tunanin samin 'yar aiki don tana tallafa mata da wasu abubuwan. Suna zaune da Daddy a parlour yake gaya mishi yana son 'yar aiki da zata na taimaka wa Suhaima saboda yawan baccin da take yi, abin da Mumy ya kamata ya fad'awa hakan amman babu fuskar hakan. Suna cikin tattauna yanda zasu samu house girl ne can daddy yace "Sabeer ina tunanin ka nemi Jiddah ta samo mata" "Yawwa haka za'a yi Daddy " Yana kok'arin zaro wayan shi ne a aljihu yaji muryar Mumy tana cewa "Haba Son basai ka kirawo Jiddah ba, zan baka d'aya daga cikin house girl's nawa su taimaka mata " Kallon ta suke da mamaki sosai ganin yanda take fara'a, duk yanda suka so su fahimci akwai wani nufi cikin zuciyar ta suka kasa gane hakan da yake Mumy 'yar duniya ce baka gane gabanta balle bayanta green snake ce. Daddy duk da haka sai da yaji shakku da abin da tace bai yarda da ita ba amman sai yabar abin cikin zuciyar shi kawai, sai kuma ta zauna sosai ana hira da ita wanda rabon ta sakewa Sabeer tun lokacin da ya fara son Suhaima. Da ya tashi tafiya ta had'a shi da house girl d'in yarinya ce bata fi 18yrs ba suka tafi amman bata bi motar Sabeer ba sai drive ne ya kaita, Suhaima taji dad'in zuwan 'yar aikin sosai gashi kuma taga bata da rawar kai. Cikin kwana 2 ta tsaya tana aikin ta sosai yanda ya kamata gashi bata da k'iwa Suhaima najin dad'in zama da ita. Da wani yammaci ne Suhaima tana zaune a parlour tana ta6a charting ita da Jiddah ne, sai ga Larai mai aiki ta kawo wa Suhaima wani had'in so6o acikin jug ga cup nan ta ajiye su kan center table tace "Aunty ga so6o nan na had'a miki " D'an yatsina fuska Suhaima tayi kan tace "Anya zan sha so6on nan Larai bana sha'awar shanshi " Murmishi tayi kan tace "Haba Aunty ki daure kisha na 6ata lokaci ina shirya miki shi fah " "To shikenan zuba min " Cikin rawar jiki ta fara zuba mata har Suhaima taso d'ago wani abun atattare da ita ganin yanda take rawar jiki amman sai ta share zancen ta kar6i glass cup d'in ta fara shan sa6on, bata ji wani canjin wani yanayi aciki ba sai ma kamshin cocomber da kayam kamshi kawai taji sai zak'in sugar, taji dad'in so6on don har cup biyu ta shanye, tana gama sha ne Larai ta tattara ta d'auke gaba d'aya takai kitchen ta zubar cikin sink ragowar ta wanke jug da cup d'in tas ta goge su tare da jera su. Tana gama wa ta bud'e k'ofar baya ta fita garden, zaro waya tayi cikin zanin ta tare da lalubo wata number ta danna kira, babu dad'e wa aka d'auka. "Hajiya nayi duk yanda kika umarci ne nayi tasha har cikin so6o biyu " Daga can akayi mata magana banji dai abin da akace ba sai naga Larai ta washe baki tana zuba godiya tare da kashe wayar cikin tsananin farinciki ta koma cikin gidan. Suhaima kuwa ko 10 minute's bata yi da shan so6on nan ba taji cikin ta marar ta da bayan ta yana wani irin ciwo na daban tun tana daurewa har ta kasa ta fara kuka sosai tana kiran sunan Allah, zaro ido tayi gabanta yana bugawa mai tsanani ganin jini yana bin k'afar ta da yawan gaske saboda tsabar firgita da razana ga azabar ciwo ta fad'o daga kan kujera kanta ya bugu da center table lokaci d'aya numfashin ta ya d'auke........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/10, 8:54 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ* *PAGE 89-90* Sabeer yana zaune a office kawai yaji gaban shi yana fad'uwa sosai Suhaima ce kawai ta fad'o mishi arai don haka phone nashi ya d'auka tare da lalubo number d'in Suhaima ya fara kiranta, sai dai wajen 10 missed calls ba'a d'auka ba. Nan ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104