Chapter 46
Chapter 46
da murya tace "To sarkin tonon silili kina son ki kunyata ni gaban su Yaya " Hannunta ta rik'o tare da juyawa da nufin su k'arasa wajen tabarmar su zauna, sai suka had'a ido da Aunty Aliyah wadda ihun Suhaima ya fito da ita daga d'aki ba shiri. Cikin farinciki Aunty Aliya tace "Jiddah yau kece a gari" Cikin dariya Jiddah tace "Ni ce wallahi Aunty ina Yaya Aliyu da Ameer ne ban gan....... " Sauran maganar Jiddah ta mak'ale a bakinta saboda had'a ido da Sabeer da tayi. Cikin mamaki tace "Yaya Sabeer! " Da murmishi kan face nashi yace "Sai yanzu kika kula dani kenan " Tana dariya tare da rufe bakinta tace "Yah Sabeer ba haka ba ne wallahi d'okin ganin Besty ne ya sanya ban kula da kai ba " D'an murmishi kawai yayi kafin ya wuce ya tafi, da mamaki sosai Jiddah take bin shi da kallo ko a mafarki bata zaci Sabeer zai zauna a irin wannan yanayin ba, kuma tayi farinciki da hakan don tun ba yanzu ba take sha'awar wani nata ya auri Suhaima saboda son da take mata, kama hannun ta Suhaima tayi suka zauna nan ta kawo mata ruwa kafin su fara gaisawa da Aunty Aliyah tana yi mata barka da samun Baby sun d'an ta6a hira kafin su wuce cikin d'akin Suhaima. Nan suna shiga hira ta 6arke tsakanin su Suhaima sai tsokanar Jiddah take yanda tayi k'iba, Jiddah na dariya tace "Yarinya sai kin yi uku nama don nasan Yah Sabeer zai baki kulawa ba kad'an ba" "A haba taya zan yi ukun ki da ban ganu ba" "Babyn kune ya sanya min wannan k'ibar don kiji yana zuwa nan duniya zan koma kamar yanda nake " Da haka suka cigaba da hirar su inda Jiddah take fad'awa Suhaima abin da ya sanya bata zo ba lokacin da suka dawo daga honeymoon laulayin ciki ne ya sanyata a gaba sai yanzu ta samu dama dama. Sai wajen mangarib Jiddah ta tafi cike da kewar Suhaima bayan ta ajiye musu tsarabar su har ta tafi dai basu k'ara had'uwa da Sabeer ba..... Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/6, 11:04 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 65-66* Suhaima ta shigo gidan kenan daga rakiyar Jiddah k'ofar gida sai taji rik'o hannunta a d'an tsorace ta juya don duhu ya fara yi gaf ake da kiran sallahr mangarib. Had'a ido tayi da Sabeer yana mata wannan kyakkyawan murmishin nashi "Matsoraciya kawai " D'an sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace "Ni Allah kaban tsoro na kusa sanya ihun neman taimako " 'Yar dariya yayi kafin yace "Sorry Baby nah kin cika tsoro, haka jiya kika cika mana kunne da ihu don kinga lizard ya shiga toilet kina wanka " Murmishin dariya Suhaima tayi don ta tuna lokacin Allah yaso ta ko cire zanin jikinta bata yi ba ta hango shi manne jikin bango. "Baby ki rage tsoro please bana son ganin abin da zai na tsorata ki " D'aga kanta tayi alamar toh kawai nan ya cika mata hannu tare da cewa "Baby anjima zamu yi magana fah da kai lokaci yayi da ya kamata mu yi aure na bar rungumar pillow koh yah? " Ya k'arasa fad'in haka yana d'aga mata gira ya cigaba da cewa "Nasan kema kina buk'atar hakan koh? " Kunya ce ta rufe Suhaima don haka sai kawai ta ruga da gudu zuwa cikin gida tana 'yar dariya a hankali, bayanta Sabeer yabi da kallo yana murmishi kafin kuma ya juya ya fita zuwa masallaci. Suhaima tana shigowa tsakar gida ta nufi wajen alwala, nan tayi alwala ta wuce d'aki tana shiga ta shimfid'a abin sallah ta fara sallahr mangarib after ta idar ne ta janyo Qur'an ta hau karatu har zuwa sallahr ishsha bayan ta idar ne sai tayi addu'o'in ta daga k'arshe ta rufe addu'ar da neman za6in Allah tare da yiwa mahaifiyar ta addu'a kamar yanda ta saba, bayan ta kammala ne sai ta kwanta saman sallayar tana mai fad'awa duniyar tunani ta yanda zata iya d'auke kai daga duk wani wulak'anci da family d'in Sabeer zasu yi mata, ta jima tana wannan tunanin kafin kunnen ta ya jiyo mata kiran sunan ta da Aunty Aliyah take mata. Tashi tayi tare da kallon k'aramin agogonta taga har 8:32 na dare, da sauri ta rarumo hijab nata ta d'an fesa turare ta fito tunawa da tayi Sabeer ya fad'a mata zasu magana anjima, tana fitowa ta tarar da Aunty Aliyah a zaune tana bawa Ameer mama. Zama tayi kusa da ita tare da cewa "Aunty ga ni " Yawwa Suhaima daman Sabeer ne yake kiran ki yana k'ofar gida" Tashi tayi ta wuce ta fita a k'ofar gida ta hango shi zaune shi da Ashiru wajen ta nufa tayi musu sallama cikin sanyin murya, Sabeer sai da ya lumshe idanun shi kafin ya bud'e su akanta ya amsa sallamar ta. Ashiru ya gaida Suhaima ta amsa cikin fara'a kafin ya tashi yace "Toh Yaya ni sai da safe zan shiga gida " "Okay Ashiru sai goben" Yana gama fad'in haka ya wuce gidan su, sannan Sabeer ya dawo da hankalin shi kan Suhaima wadda take tsaye yace "Amarya ta zauna mana kada ki gaji da tsayuwa " D'an nesa kad'an dashi ta zauna saman wani dutse, nan ya fara tsokanar ta yana dariya ita kuma kunya yake bata don har yanzu ta kasa sakin jiki dashi musamman idan ta tuna abin da tayi mishi a baya. Bayan ya gama tsokanar ta ne sai kuma ya gyara zama cikin nutsuwa yace "Suhaima! " D'an d'ago wa tayi ta kalleshi kad'an saboda jin yanda ya ambaci sunan nata kafin tace "Na'am! " D'an ajiyar numfashi yayi kafin yace "Suhaima ina son gobe zan koma gidan mu fah" A d'an razane ta d'ago tana kallon shi don lokacin da ya fara maganar kanta a k'asa yake tana wasa da 'yantsunta. "Yes! Baby gida zan tafi zanje na samu Daddy yazo neman min auren ki, mun gama magana da Yah Aliyu dasu Baba don sam ban so awuce 2 month's ban mallake ki matsayin mata ta ba" "Wata 2 fah Sabeer haba me ma laifin nan da 2 year ". Cewar Suhaima kanta a sunkuye don bazata iya jurar ganin irin kallon da Sabeer yake mata, ji take kamar ta kwashe da dariya saboda tasan tsokanar shi take so take taga yanda zai yi don haka danne dariyar ta. Aikuwa wata harara ya dank'ara mata kafin yace "Sun yi kad'an ma 2yrs a barshi nan da shekaru goma ma yafi" Ba shiri dariyar da take danne wa ta kubce mata aikuwa ta fara kyalkyala dariya amman ta nutsuwa, sakin baki Sabeer yayi yana kallonta sai a time d'in ya lura tsokanar shi take, lallai kuwa idan ya kama Suhaima a hannun shi zata yi bayani. "Ya hak'uri mai da wuk'ar tsokanar ka nake a daina harara ta" D'an murmishi yayi tare da cewa "Lallai yarinyar nan kin rainani da yawa but zaki bayani idan kika shigo hannuna duk sai na rama abin da kike min " Marairaice fuska Suhaima tayi tare da cewa "Wayyo Allah kayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104