Chapter 42
Chapter 42
Suhaima ashe kece " Cewar budurwar yarinyar tana washe baki, wata harara ta gallawa buduwar wanda batasan ta iyata ba, sauran kad'an dariya ta kubcewa Sabeer ganin abin da tayi. D'an wani tunani Suhaima tayi sai kawai ta k'ak'alo yak'en dole tace "Eh ni ce Sadiya ya kike? " Tana washe hakora tace "Lahiya lau wallahi yanzu tahowar da zanyi gidan ku zan shigo ganin jaririn Aunty Aliya sai wannan d'an binni ya tsayar da ni " "Hmmm " Abin da Suhaima ta fad'a kenan, sannan ta mayar da hankalin ta kan Sabeer ta mik'a mishi wayar shi ba tare da sun had'a ido ba tace "Kiran ka akai " Bata bari ma ya kar6a ba ta sakar mishi ita Allah ya sanya yayi saurin cafewa ba don haka ba da ta kwankwatse sai kawai ya bita da kallo har ta wuce cikin gida kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mik'e shima ba tare da ya kula Sadiya ba ya wuce cikin gidan d'akin shi ya shiga ya rufe k'ofa tare da kwanciya saman katifa yana son fassara abin da yake kan fuskar Suhaima amman ya kasa tantacewa nan ya fara juyi kawai. Suhaima kuwa tana shiga gidan ta wuce zuwa cikin d'akin ta idanun ta sun rufe da wani irin abu da ta tabbatar da ba komai ba ne sai kishin Sabeer, fad'a wa tayi kan gadon ta tare da fashewa da wani irin kuka, tasan idan ka fara son mutum dole kayi kishin sa kenan ya ita ta fara son Sabeer tunda gashi daga nin shi da wata batasan dalilin tsayuwarta ba ta ji wani abu ya tokare mata wanda tasan ba komai ba ne sai kishin Sabeer!...... _ku cigaba da hak'uri fan's da ni, ga wannan ku yi manage da shi please_ Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/28, 5:42 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 59-60* Tana kwance kawai taji an dafa bayanta a d'an tsorace ta d'ago kanta sauke ajiyar zuciya tayi don ganin Aunty Aliya ce ta dafata. "Tashi mu yi magana Suhaima" Tashi zaune tayi tana mai sunkuyar da kanta tana murza 'yantsunta batason ta kalli Aunty Aliya su had'a ido kada ta karanci wani abin akan fuskarta. "Hala Suhaima kin fara son Sabeer ne kike kishi dashi? " A razane ta d'ago kanta tana kallonta, gid'a kanta Aliyah tayi tare da cewa "Idan baka son mutum taya zaki fara jin haushi don kin ganshi a tsaye da wata?" "Ni fah Aunty bason Sabeer nake ba ni ba haushi naji ba fah dana ganshi da wata a tsaye" "Shikenan tun da ni ban isa ki fada min matsalar ki ba amman tabbas kwanaki biyun nan kin canja don ba haka kike ba, amman tun da kin ce ba haka ba" Tana gama fad'in haka ta juya zata tafi da sauri Suhaima ta sanya hannun ta ta rik'o na Aunty Aliya da D'an k'arfi ta matse hannunta "Ni kada ki ji min ciwo kawai ki cikani na tafi tunda ni baki d'auke ni matsayin Yayar ki ba kuma abokiyar shawarar ki, ni da nasan Suhaimar dana sani ba haka take ba bata iya 6oye min komai nata" "Aunty kiyi hak'uri ki zauna zan fad'a miki koma mene " Zama Aunty Aliya tayi kusa da Suhaima. Kamar bazata yi magana ba tayi shiru sai mutsu mutsu take da baki, d'an kallonta Aliyah tayi tare da girgiza kai kawai wani lokacin Suhaima tana bata mamaki idan tana wasu abubuwan. "Idan baza ki magana ba zan tafi ". Cikin rawar murya kamar mai shirin fashewa da kuka tace "Uhm... Uhm Aunty ni kaina na rasa mai yake damuna haka, cikin kwanaki biyun nan idan Sabeer yayi min magana ko muka had'u sai naji gabana yana fad'uwa, sannan kuma kawai d'azu dana ganshi da wata sai naji wani takaici wanda ya sanya ni kuka" "Kin fara son Sabeer kenan ". Waro ido waje tayi tare da dafe kirjinta da hannu kafin tace "Taya na fara son Sabeer Aunty bayan ni kuma sam baya gabana? ". "Ta yanda kika fara kishi dashi, Suhaima ina mai k'ara tunasar da ke da kada kiyi abin da zai sanya ki dana sani daga baya saboda na tabbatar idan kak'i Sabeer zaki zo kina nadama mara amfani don kafin ki samu wanda zai so ki kamar Sabeer zaki dad'e kina nema, kiyi amfani da damar ki Suhaima kafin ta kubce miki " Tana gama fad'in haka ta tashi ta fita saboda kiran da Babaa Lantana tayi mata, ta bar Suhaima cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa. "Nayi amfani da dama ta kafin ta kubce min, me Aunty take nufi.....! " Dafe kanta take wanda ya fara yi mata ciwo gaba d'aya ta rasa me ya kamata tayi shin zata bi shawarar Aunty Aliya ne ko kuwa zata bi abin da zuciyar ta yake kitsa mata na kada ta bari son Sabeer ya zauna mata cikin zuciya idan ba haka ba zatayi nadama don family d'in Sabeer baza su so ta ba a matsayin surukar su duba da wulak'ancin da tasha lokacin bikin Jiddah. *_After two weeks_* Acikin wannan satin ne bayan an sha sunan d'an Yaya Aliyu wanda aka sanya mishi sunan Baba Adamu, su Babaa Lantana sun so ya sanya sunan mahaifin shi Umaru amman Aliyu da Suhaima suka k'i aminta da hakan k'ememe don baza su ta6a mance abubuwan da mahaifin su ya aikata musu ba, Ameer Suhaima ta sanya yaron suna fad'a mishi saboda 6oye sunan shi da suka yi. Zuwa wannan lokacin Sabeer ya dad'a ramewa sosai sakamakon tunani da ya sanyawa kanshi gashi yaja baya da al'amarin Suhaima da yana da ikon da zai cire sonta cikin zuciyar shi da yayi, duk wanda yasan Sabeer a baya yanzu ya ganshi sai ya tausaya mishi musamman akasan A SANADIN SO ya zama hakan gaba d'aya ya fita hanyar Suhaima tunda ko ya kulata ba wani sauraren shi take ba, sosai Aunty Aliya da Yaya Aliyu suke tausaya mishi don yayi alkawarin bazai yiwa Suhaima auren dole ba sai dai kawai taji ana d'aura auren ta da Sabeer sosai Aliyu yana bashi tausayi. Ta 6angaren Suhaima ma duk ta wani rame saboda son Sabeer da kullum yake shiga cikin zuciyar ta yana nuk'urk'usa kowanne sashi na cikin zuciyarta, sai dai ta kasa bawa zuciyar ta aminta har takai da ta furtawa Sabeer cewa tana son shi zata aure shi sannan zata iya jure duk wani wulak'anci na family d'in shi zata jure shi indai Sabeer zai rik'e ta cikin mutunci bazai juya mata baya. Da wannan tunanin take kwana take tashi tana jiran Sabeer ya k'ara furta mata kalmar so a time d'in take son sanar dashi ita ma ta kamu da son shi, a lokacin da take kok'arin fad'a mishi ta kamu da sonshi a lokacin kuma ya canja mata ko magana bata had'a su yanzu ya zatayi kenan. Zaune take a d'aki tana wannan tunanin da ya zame mata kamar karatu don a kullum makamancin tunanin take yi, runtse ido tayi hawaye masu zafi suka samu sauka asaman face nata, zafi zuciyar take mata. Zumbur ta mik'e tsaye da zaunen da take ta fito tsakar gida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104