Chapter 82
Chapter 82
bag sai laptop d'in shi ko atm card's nashi bai d'auka ba, bayan ya gama ne ya shiga wanka a d'an jima a cikin bathroom kafin ya fito ya shirya cikin wani lallausan farin boyel perfumes different colour ya sanya. Yana gama wa ne ya d'auki bag d'in tare da rataya ta saman kafad'ar shi ya fito hannun shi rik'e da phone nashi, Daddy shima har ya gama shiryawa don raka Sabeer airport har sun fito zasu tafi sai ga Mumy nan da car key a hannunta tana cewa "Son muje nayi maka rakiya airport " Ko kallon ta Sabeer bai yi ba ya wuce zuwa cikin motar da Daddy yake zaune, fita suka yi daga gidan gaba d'aya motar Mumy tana bin bayan tasu Sabeer. Bayan sun k'arasa airport ne nan Sabeer yayi sallama da Daddy don uwa uwace kawai Sabeer ya sanya shi yiwa Mumy sallama ya wuce su ya tafi zuwa cikin airport ne, dad'i ya ishe Mumy ganin Sabeer ya kulata tana tunanin ko ya fara sakkowa ne, cikin mota ta wuce ta shiga driver yaja ta don hospital zata tafi. Sabeer ya d'auki wajen 30 minute's azaune kan ya tashi ya fito daga cikin airport d'in zuwa waje, tsayar da taxi ya fara kok'arin yi yaji an dafa mishi kafad'a a razani ya juyo 4 eyes suka yi da Daddy wanda ke faman yi mishi murmishi, ajiyar zuciya ya sauke kawai. Hannun shi Daddy ya rik'o zuwa cikin mota bayan sun zauna Daddy ya kalle shi kafin yace "Son tunda ka fad'a min zaka tafi England nasan ba haka bane jikina ya bani akwai wani abun dalilin da ya sanya ni ban tafi ba kenan, ina zakaje? " "Daddy kauyen su Suhaima zan tafi don na dawo da mata ta " "Hakan yayi kyau Son ina goyon bayan ka, amman bai kamata ka 6oye min ba " "Am so sorry Daddy bana son Mumy tasan da inda zan tafi don kada ta hanani dawo da Suhaima cikin rayuwa ta " Hannunshi Daddy ya rik'o kan yace "Ka tafi Sabeer idan ta kama duk tsayin lokacin da zaka yi acan kayi shi amman kada ka dawo gida babu Suhaima don yarinya ce mai hankali, ka daure duk wani yanayi da zaka fuskanta acan don nasan dole ka fuskanci hukunci awurin su, Allah yayi maka albarka ya taimaka maka ya tsare min kai a duk inda kake" Rungume Daddy Sabeer yayi yana goge hawayen da suka zubo mishi sun d'an jima a haka kafin Daddy yace "Ka tafi Son kada kayi tafiyar dare, amman kada mance ka kashe wayar ka saboda Mumyn ka idan ta ji shiru zata iya bibbiyar layin ka har ta gane a inda take ", gid'a kai Sabeer yayi. Fitowa suka yi daga mota jikin Sabeer duk a sanyaye Daddy ne yayi k'arfin tsayar mishi da taxi ya biyashi kud'i masu yawa tare da ce mishi ya kai Sabeer duk inda yake so, sallama Daddy da Sabeer suka yi har taxi d'in ta wuce Daddy yana tsaye a wajen zuciyar shi fal tausayin d'an nashi kafin ya juya ya shiga mota driver yaja shi sai gida. Idanun Sabeer a waje yana kallon yanayin gari amman tunani da fargaba tsoro fal cikin zuciyar shi ta yanda za'a kar6e shi gidan su Suhaima idan yayi duba da abin da Aliyu yayiwa Jiddah wadda bata da laifi ko kad'an a wannan abu da ya faru. Har k'ofar gidan su Suhaima d'an taxi d'in ya sauke Sabeer, dakyar ya iya jarumtar fitowa daga motar gaban shi na dukan goma goma don baisan me zai je ya tarar ba. Yana fitowa d'an taxi ya k'ara gaba sake gyara jakarshi yayi ta saman kafad'ar shi ya doshi gidan, amman duk takun da zai yi sai gaban shi ya fad'i a haka ya k'arasa k'ofar gidan. Kallon gida yake da mamaki sosai cikin fuskar shi ganin yanda aka gyara gidan kamar a birni ba'a karkara ba, zauren gidan ya kutsa kanshi, dakyar ya iya bud'e baki yayi sallama cikin sanyin murya. Amsa mishi sallamar akayi babu tantama yasan muryar Aunty Aliyah ce. "Suhaima sanya hijab d'inki ki duba ko bak'on Yayan ki ne kice ya jirashi ya shiga wanka " "Toh Aunty " Suhaima ta fad'a cikin tsintar kanta da fad'uwar gaba, d'aki ta shiga ta d'auko hijab ta sanya tare da nufar k'ofar zauren still gabanta bai bar fad'uwa ba. "Ka d'an jira shi ya shiga wank........ " Suhaima bata k'arasa maganar ba da zatayi sauran ta maka'ale a saman fatar bakinta ganin mutumin da ta had'a ido dashi, rufe idonta tayi ta sake bud'e wa ko mafarki take but still Sabeer take gani cikin eyes nata, tsayawa kawai taji jikinta na rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi kallonta yake cikin wani irin tausayin ta da yake ratsa shi ga wani sabon sonta da yake sake kwaranya cikin zuciyar shi, ita ma kallon nashi take kawai cikin mamakin me ya kawo shi gidan su ko dai ya zo ya baki takardar saki ne wannan tunanin da Suhaima tayi ya sanya firgita da tsorata. "Suhaima wane ne naji kin tsaya lafiya " Cewar Aunty Aliyah, maganar da Aunty Aliyah tayi shi ya dawo da Suhaima hayyacin ta, da sauri tabar wajen da sauri Sabeer ya biyo bayanta yana cewa "Suhaima ki tsaya ki saurare ni please " A tsorace Suhaima tayi bayan Aunty Aliyah ta 6uya ganin sauran kad'an Sabeer ya cafkota, a firgice Aunty Aliyah take kok'arin cewa Sabeer ya gudu ya bar gidan amman kafin ta bud'e bakinta Aliyu ya fito daga toilet sanye da jallabiya ajikin shi. Kallon Suhaima da Aliyah yayi ganin gaba d'ayan su a razane yasa shi kallon inda suke kallo aikuwa suka had'a ido da Sabeer, kamar wani zaki ya nufi inda Sabeer yake tsaye wanda ko gezau bai yi ba na nuna tsoro hasali ma gaba d'aya hankalin shi na kan Suhaima............. Aishat A Muh'd Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/16, 8:48 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 102-103* Afusace Yah Aliyu cakumi wuyan Sabeer ya matse da k'arfi idanun shi tuni suka yi ja ya fara wani irin tari, cikin fusata yake cewa 'Me kazo yi kuma, bayan ka koreta daga gidan ka ina fatan takardar sakin ta ka kawo min don k'anwata bazata ta6a komawa gidan ka ba? " Dakyar Sabeer yake jan numfashi don ba k'aramin shak'a Aliyu yayi mishi ba, cikin murya k'asa k'asa yake cewa "Nazo ne domin na baku hak'uri akan abin da ya faru na kuma dawo da Suhaima gidana " Dad'a shak'e shi Aliyu yayi kan yace "Kaiii asuwa da har zaka sanya Suhaima dawowa gidan ka, k'anwata ta barka har abada bakai ba ita " Sabeer na kok'arin magana Yah Aliyu yaja shi tare da watsa shi waje ya mayar da k'ofar ya rufe har da sanya sakata, kallon su Suhaima da Aliyah yayi ganin yanda suke kuka sosai hararar ya maka musu kan ya wuce d'aki yana huci. Suhaima ma da gudu ta shige d'akinta tana kuka da ta rasa na mene, yayin da Aunty Aliyah ta tafi wajen Aliyu ko zata rarrashe shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104