Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,189 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya dame shi da ita ne yasa shi farka wa daga baccin da ba wani jin dad'in shi yake ba, kallon k'afar yayi yaga ta kumbura sosai tamkar ba k'afar shi ba, tsura mata ido kawai yayi yana kallo, yana jin an bud'e k'ofar d'akin an shigo. "Subhnallah Son haka k'afar ka ta koma? " Bai kalle shi ba balle yasa ran zai amsa mishi, ganin haka yasa Daddy d'auko wayar shi ya kirawo mai gyaran k'afa tare da kiran family doctor d'in su Kafin ya ajiye wayar ya zubawa Sabeer ido yana kallon shi, ya hana kowa shigowa inda yake amman dukkanin su suna parlour a zaune Mummy da Hajjah sun sha kuka sun more yak'i sanar musu da ainahin abin da Sabeer ya fad'a mishi saboda yasan ba k'aramin ruguntsumi za'a sha ba. Suna zaune har mai gyaran k'afa yazo bayan ya shigo d'akin sun gaisa da Daddy zai ta6a k'afar Sabeer ya janye ta da sauri tare da cewa "Bana buk'ata a duba min" "Haba Son taya ga ciwo a jikin ka kak'i yarda a duba maka, kayi hak'uri a duba maka please " Duk wani rarrashi da lalla6a Daddy yayi wa Sabeer amman yak'i yarda har Doctor d'in da Daddy ya kirawo yazo amman duk Sabeer yak'i yarda gashi k'afar dad'a kumbura take, Daddy kasa jure ganin tilon d'an shi a haka yayi don haka ya bud'e baki yace...... Mu had'u next page fan's, naga Comment's naku na jiya sosai naji dad'i Allah ya bar k'auna. Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 46-47 Daddy kasa jure ganin tilon d'an nashi a haka yayi don sam bazai iya ganin Sabeer cikin mawuyacin hali ba don haka ya bud'e baki yace "Ammm ku d'an bamu wuri zamu yi magana da Sabeer please idan muka gama zan kirawo ku" Tashi suka yi suka fita kafin Daddy ya matso kusa da Sabeer ya dafa kafad'ar shi da hannun shi d'aya, zame hannun Daddy yayi tare da juyawa ya kalli wani 6ari daban, d'an murmishin yak'e Daddy yayi wai yau Sabeer d'in shi akan soyayya yake juya mishi baya wannan wanne irin so yake mata, bar tunanin yayi ta hanyar cewa "Son look at me please" Fuska a had'e Sabeer ya jiyo yana kallon Daddy sai wani had'e rai yake. Girgiza kai kawai Daddy yayi kafin yace "Son bazan iya jurar ganin ka cikin wannan yanayin ba, na amince ka auri wannan yarinyar sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba tace maka bata son ka ya za'a yi? " Tuni fuskar Sabeer ta fad'ad'a da wani irin fara'a na tsantsar farinciki saboda jin abin da Daddyn shi yace, rungume shi yayi cikin dariya mai hawaye yace "Thank U Daddyna nasan kai mai k'aunar farinciki na ne duk abin da nake so kana kok'arin yi min, sannan zan tafi inda Suhaima take nayi rayuwa irin tasu don na sami soyayyar ta A SANADIN SON Suhaima zan iya jure duk wata wahala Daddy indai zan same ta " Kallon shi Daddy yake kawai cikin d'umbin mamakin abin da Sabeer ya fad'a ajiyar numfashi yayi kafin yace "Son kana nufin k'auyen zaka koma da rayuwa, kaci irin abincin su, ruwan su ka kwana irin d'akin su?" "Yes Daddy zan iya indai zan samu Suhaima " 6ata fuska Daddy yayi tare da cewa "ina Son bazai yiwu ba, kaje dai ka taho dasu ita da Family d'in ta zan basu gida da kud'i sosai sannan na bawa mahaifin ta aiki amman kaje k'auye kana matsayin jikan mafi soyuwa acikin family d'in d'an fillo kaje ka zauna a k'auye haba Son " D'an yatsina fuska yayi tamkar zai fashe da kuka yace "ni dai zan iya Daddy idan naje zanyi musu maganar dawowa nan da abin da zaka yi musu nasan zasu biyo ni " Girgiza kai Daddy ya fara alamar bai yarda ba, aikuwa Sabeer ya ta6e fuska irin ta shagwa6a66un yaran nan zai fashe da kuka da sauri Daddy ya rungume shi yana bubbuga bayan shi yace "Nooo Son don't cry please na amince Allah ya baka nasarar sace zuciyar ka kamar yanda ta sace maka zuciya lover boy" Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer, kafin ya saki wani murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ganin tafe zuwa gare ki Suhaima, rungume Daddy yayi cikin farinciki yace "Thank U so much Daddy i am proud of U" Bubbuga bayan shi Daddy yayi kafin yace "Don't worry Son farinciki ka shine nawa all the best" "K'arya kake Sabeer daman akan 'yar talaka 'yar k'auye kake wannan haukan duk ka d'aga mana hankali, danasan saboda haka kayi wannan abin da wallahi bazan zo wajen ka balle har na zubar maka da hawayen tausayi " Gaba d'aya suka jiyo a matukar razani daga Daddyn har Sabeer d'in had'a ido suka yi da Mummy tana tsaye sai faman sauke numfashi take fuskar nan ko kad'an babu fara'a. "Nima ina goyan bayan ta bazan ta6a zuba ido ya auro mana 'yar matsiyata ba daman akan haka kake wannan haukar to ko zaka mutu baza mu ta6a yarda ba, amman Sabeer ka bani kunya da mamaki, kai ma Hussein ka ban kunya da ka amince da buk'atar shi " cewar Hajjoh cikin tsananin 6acin rai. Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya kasa magana ma saboda tsantsar 6acin rai har wani rawa fuskar shi take lol, saboda 6acin rai magana ma ya kasa yi. Had'e fuska Sabeer yayi alamar ba wasa ya mik'e tsaye yana d'ingishi ya k'arasa wajen Hajjah yace "Hajjah kada ki k'ara kiran Suhaima da 'yar matsiyata ni Suhaima nake so ba ruwana da kud'in su don haka sai na aure ta babu wanda ya isa ya hanani! " Tasss Sabeer yaji saukar zazzafan mari a saman kuncin shi wanda tunda Mumy ta haifo shi ba'a ta6a marin shi ba, marin ba k'aramin shigar shi yayi ba don sai da gefen bakin shi ya fashe kad'an jini ya fito, dafe kumatun shi yayi cikin mamaki ya d'ago kanshi ya kalli wanda ya mare shi ba kowa bane sai Alhj Ahmad d'an fillo sai huci yake zuba kamar wanda ya had'iyi kunama har da had'a gumi tamkar babu ac da fanka a bedroom d'in yayin da Daddy, Mummy da Hajjah suka kusan suman tsaye tsabar kid'ima da abin da akayi wa Sabeer. Yana dafe da kumatun shi yana kallon Alhj Ahmad kafin kuma ya lumshe idon shi sai gani suka yi yayi baya luuu zai fad'i k'asa cikin zafin nama Alhj Ahmad da Daddy suka taro shi ya fad'o jikin su. Daddy jiki na rawa ya d'auko wayar shi ya kirawo Doctor, Hajjah da Mumy kuma kuka suka sanya tare da zube wa kusa da inda Sabeer yake suna cewa "Sabeer ka tashi please " Daddy ne ya d'auke shi ya d'ora kan bed da taimakon Doctor ya shigo don Alhj Ahmad zube wa yayi a k'asa yayi zaman 'yan bori hannun shi yake bi da kallo wanda ya mari Sabeer dashi tamkar wani soko haka yake kallon hannun, wai shi yau ya mari Sabeer mafi soyuwa cikin zuciyar a gaba

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});