Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,186 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ya k'arasa fad'i yana yatsine fuska, da kan ganshi kasan d'an shagwa6a ne na ajin k'arshe ma. Murmishi Mummy ta saki tare da cewa "Haba my son kasan yau ne na had'a partyn murnar dawowar ka gida lafia da kammala karatun ka koh" D'an yatsina fuska yayi tare da sake 6ata fuska yace "No need Mummy kinsan ban son hayaniya right? " Hannun ta ne saman gashin kanshi tana shafawa tace "Nasan da haka son but kamar kai ka dawo daga wata k'asar ka kammala karatu cikin sa'a kace bazan had'a party ba I'm sorry to say son sai nayi " Bai kulata ba ya yaye blanket d'in jikin shi ya zuro k'afafun shi a k'asa tare da tashi tsaye daga shi sai short niker white colour irin skin tight d'in nan ya wuce toilet a fusace, don sam bai jin dad'in dage wa da Mummy tayi ba aka wannan party da ta had'a mishi. Da murmishi Mummy ta bishi da kallo cikin so da kaunar shi tace "Son d'an rigima kenan, bazan biye maka balle ka hanani nuna wa duniya cewar kai d'an gatan family d'in Alhaji D'an fillo ba ne gaba da baya " Tana gama fad'in haka ta bar bedroom d'in don ba k'aramin aikin son ba ne yasa ta a gaba ba sai ta shirya shi saboda tsabar gata da sangarta irin ta d'an nata SABEER... AISHAT A MUH'D ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💖 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ PAGE 11-12 Yana fito wa daga bathroom yaga Mummy bata cikin bedroom d'in, ta6e fuska yayi kamar zai saki kuka ya dafe gishin shi yana cewa "Oh my God shine Mummy kika gudu koh? " Yana gama fad'in ya k'arasa wajen tafkekiyar wardrobe d'in shi ya bud'e ta a kasalance, don Sabeer ba k'aramin sangartacce ba ne komai idan zaiyi a sangarce yake yi. Dakyar ya iya d'auko wani white 3quater da T-shirt yellow mara hannu ya sanya su, tukunna ya k'arasa wajen dressing mirror ya gyara gashin kanshi sannan ya sanya perfumes different colour designer, masu matuk'ar k'amshi yana gama wa ya sanya hannun shi ya d'auko d'aya daga cikin favorite phone nashi. Sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin nashi, idan mutum ya kalle shi sai ya zaci irin jarumin namijin nan saboda k'irar k'arfi da yake da ita, amman idan mutum yasan irin yanda yake matsoraci gashi sangartaacce ne na ajin k'arshe, don iyayen shi ba k'aramin sangartashi suka yi ba gashi Shagwa66e6e ne. Cikin takun tafiyar shi ta kalar Shagwa6a ya k'arasa sauka zuwa k'asan stairs, kai tsaye inda parents d'in shi suke ya nufa a dinning table inda suke breakfast, wajen dinning table d'in kanshi abin kallo ne ya had'u sosai gashi babba wanda a k'alla zai d'auki mutum goma. Suna hango shi suka fad'ad'a fara'ar su kallon shi suke cikin so da k'auna tamkar yau suka fara ganin shi, a tsakanin Mummy da Daddy baza ka iya tantance wanda wani yafi k'aunar tilon d'an su ba, tashi Daddy tsaye yayi tare da yin hugging d'in shi har da wani bubbuga bayan shi kad'an yana cewa "My lvly son good morning" Cikin shagwa66iyar murya Sabeer yace "Morning Dad " Bayan sun gama gaisawa Daddy yaja mishi kujera ya zauna, sannan yace "Son me zaka ci Mummyn ka tayi serving naka " "Nothing" D'an zaro ido yayi kad'an yana kallon Sabeer kafin yace "What! Son kasan bazan barka da yunwa ba don haka oya tell me " Duk wannan maganar da suke Sabeer ko kallon inda Mummy take bai yi ba sai wani 6ata fuska yake tamkar irin wanda ake mintsina sannan aka hana mutum kuka haka Sabeer yake. Ganin hankalin Daddy ya tashi ne yasa shi cewa "Okay Daddy na don't worry, a bani one cup of coffee ma" "Yawwa Son ko kai fa " Sai lokacin hankin Daddyh ya kwanta but yasan an 6atawa Son nashi rai cox haka yake fushi da abinci idan an 6ata mishi rai. Cikin murmishi Mummy tace "I'm so sorry my son nasan dalilin fushin ka" Ta k'arasa fad'a tana rik'o hannun shi cikin sigar rarrashi take mishi magana, kallon ta Daddy yayi tare da cewa "Oh I know ke kika 6ata mishi rai, tun da naga yak'i kallon inda kike " "Bafa wani abun babba ne ba fah Daddy" Cewar Mummy. "Fad'a min abin da ya had'a ku " Murmishin dai har yanzu Mummy take tana had'a wa Sabeer coffee sai da ta gama had'a shi tukunna ta bawa Sabeer cup d'in a hannun shi, sannan ta kalli Daddy da har yanzu kallon ta yake yana jiran ta fad'a mishi abin da ya had'a ta lvly Son d'in shi. Cikin yanayin k'sisina da karya murya tana wani fari da eye's nata tace "Daddy ka tuna lokacin da na sanar da kai idan Son ya gama karatun shi zan had'a mishi party na gayyato k'awaye na da abokanan arzik'i mu taya shi murnar kammala karatun shi lafiya, akan na sanar da shi fah ya fad'a min baya so shine ni kuma nace yayi hak'uri zan yi, shine fah yake fushi da Mummyn shi " D'an murmishi Daddy yayi don yasan halin Mummy wajen son nuna wa duniya d'an nata d'an gata ne duk abin da Sabeer yake so a wajen ta zata siya mishi indai akwai shi a duniyar nan, bata wasa da al'amarin Sabeer indai kuwa abin yayi mata tana rawar jiki zata yi mishi. Kallon Sabeer yayi yaga ko kallon inda suk bai yi ba hankalin shi yana kan wayar time to time yana kur6ar coffee nashi tamkar baisan abin da suke magana akai ba. Daddy ya rasa yanda zai yi baya son 6atawa d'an nashi rai haka kuma baya son ran Mummy ya 6aci, gashi ta zuba mishi eye's d'in ta da suke matuk'ar rud'a shi sai wani salo na daban take mishi. Da ido yayi wa Mummy alamar bari ya gwada rarraso shi, hannun Sabeer ya rik'o tare da cewa "My son kayi hak'uri da abin da Mummyn ka zata yi, kasan saboda son da take maka shi yasa take yin komai don taga ta faranta maka rai, gashi ta gama kashe kud'i masu yawa domin tayi maka abun da zai sanya ka farinciki, please Son kayi hak'uri ka bata wannan damar kada kace a'a son " Shiru suka yi dukannin su suna jiran abin da d'an lele zai ce, cikin zuciyar Mummy tana addu'ar Allah ya sanya Sabeer ya amince, sai da ya k'arasa shanye coffee d'in shi tukunna ya mik'e tsaye har ya juya bayan shi zai tafi. Gaba d'aya Mummy ta gama hak'ura da zai amince da party, sai kuma suka ji amon sautin muryar shi yana cewa "Alright naji Mummy but 30 minutes only zanyi a wurin " Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi, cikin Farinciki Mummy tace "Yes! Daddy i can't believe ya amince min" Murmishi Daddy tare da cewa "Daman kece baki bishi ta rarrashi ba kinsan d'an naki sometimes sai da rarrashi " Mik'e wa tsaye suka yi Mummy saboda jin dad'i tayi hugging d'in Daddy tare da bashi peck a cheek d'in shi. Murmishi suka

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});