Chapter 29
Chapter 29
kafin ta shiga motar bayan ya bud'e mata k'ofar motar. Babu dad'e suna tafiya ba aka suka k'araso gidan su Jiddah bayan yayi parking ta kwashe kayan ta da tayi shopping ta fito daman a motar ta bar su, tana shigowa d'akin Jiddah sak'on harara ne ya fara ziyartar Suhaima a wajen su Zahra da sauran cousin's d'in Jiddah sa'annin ta, bata kula su ba ta k'arasa wajen Jiddah taya zata iya aminta da soyayyar Sabeer alhalin 'yan uwan shi suna kyamatar ta bazata kai kanta cikin matsala ba. Daga baya ma sai suka zame suka bar musu d'akin daga Jiddah sai Suhaima, nan Suhaima ta bawa Jiddah gift's din da ta siyo mata hannu biyu Jiddah tasa hannu ta kar6a tana yiwa Suhaima godiya, tuni Suhaima ta watsar da abin da ya faru da ita da Sabeer ta fara harhad'a kayanta don gobe ana gama bud'an kai Yaya Aliyu zai zo ya d'auke ta zata koma k'auyen su inda hankalin ta zai fi kwanciya. Da dare kuma dinner d'in da friends na ango suka had'a aka gabatar wanda iya k'awayen amarya da na ango ne kawai, daga nan kuma aka wuce da amarya gidan ta wanda yake nasarawa GRA gidan ya had'u sosai, nan Suhaima da 'yan uwan amaryar suka kwana. Washe gari kuma da safe akayi walima anan farfajiyar gidan nata wanda ya had'a manyan malaman addinin musulunci mata suka gabatar da lectures akan rayuwar aure da tarbiyyar yara zuwa 1 aka tashi daga walimar bayan anci an sha. Sallahr azahar Suhaima tayi bayan ta idar ta ne babu dad'e wa Yaya Aliyu yayi wa Jiddah waya yana k'ofar gidan, nan Jiddah da Suhaima suka rungume junan su suna kuka sosai dakyar dai Suhaima ta zame jikin ta ta d'auki bag nata suka fito babu wanda Suhaima tayi wa sallama cikin families d'in Jiddah don basu yi maraba da bak'unta suka yi ba. Har compound d'in gidan Yaya Aliyu ya shigo suka gaisa da Jiddah tare da bata hak'urin rashin zuwan su da basu yi ba saboda jikin Aliyah sai a hankali, nan ta nuna ba komai yayi mata fatan alkhairi na zama lafiya, sannan suka yi Jiddah sallama suka tafi bayan kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima sosai, tana tsaye a wurin har suka fita daga gidan kafin ta koma ciki tana zubar hawaye na kewar Suhaima don tasan zasu kwana biyu basu had'u ba sai a waya. Bayan Yaya Aliyu ya tada machine d'in shi suka fara tafiya Suhaima na bashi labarin yanda bikin ya kasance amman ba komai ta sanar mishi ba don bata sanar shi had'uwar ta da Sabeer ba da kuma yanda 'yan uwan Jiddah suka kar6e ta, murmishi kawai Yaya Aliyu yake na jin dad'in ganin tilon k'anwar tashi cikin koshin lafiya..... Sai dai kuyi manage da page d'in nan ban samu time d'in da zan yi editing ba, mu had'u a next page don jin ko Sabeer zai hak'ura da Suhaima? Ko mai zai kasance a gaba?... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 42-43 Bayan sun k'arasa gida ne Yaya Aliyu nayin parking d'in machine Suhaima ta sauka da d'an gudunta ta nufi k'ofar shiga gida, a zauren gidan suka yi ki6is da Aunty Aliyah fuskar ta d'auke da murmishin farinciki, rungume Aunty Aliyah tayi cikin farinciki tace "Aunty nayi kewar ki " Cikin murmishi Aunty Aliyah tace "Nima haka Suhaima ba k'aramin kewar ki nayi ba, tun da kin dawo lafiya Alhmdullilah naji dad'i " "Aunty ya jikin ki da babyn mu? " "Jiki Alhmdullilah Suhaima, ya kika baro Jiddah amarya? " "Jiddah mun kaita gidan ta Aunty yayi kyau gidan tace tana gaida ke nayi miki sannu da jiki kuma ta gode sosai, bari dai anjima zan baki labarin yanda bikin ya kasance" 'Yar dariya Aunty Aliyah tayi tare da kamo hannun Suhaima suka wuce cikin gida, suna shiga Yaya Aliyu ya shigo hannun shi d'auke da bag d'in Suhaima da sauran kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima su. A tsakar gida ya tarar dasu a zaune saman tabarma Suhaima na yiwa Aunty Aliyah hira, d'an murmishi yayi kafin yace "Oh Suhaima surutu ko hutawa baki yi ba zaki dame mu da surutu " Dariya Aunty Aliyah tayi yayin da Suhaima ta turo baki na shagwa6a tace "Kai Yaya daga dawowa ta zaka ce na dame ka da surutu bayan yanzu Aunty tace lokacin da na tafi har d'akina kake shiga ka zauna ciki saboda kewa ta da kayi " Dafe goshin shi yayi yana girgiza kai kafin yace "Oh Aliyah har kin sanar mata me yasa kika fad'a wa wannan sarkin surutun? " Aunty Aliyah na dariya tace "ai gaskiya ne gwara na fad'a mata tasan ni da Yayan ta mun damu da ita sannan munyi kewar ta na tsayin kwanaki biyu " "Yawwa Aunty naji dad'i da kika fad'a min, kai kuma Yaya nayi maka yajin aikin magana na minti d'aya " Dariya suka kwashe da ita kafin Yaya Aliyu ya janyo hannun ta zuwa kusa dashi ya zaunar da ita, cikin k'asa da murya yace "Haba 'yar k'anwata ayi wa wannan Yayan naki afuwa bazan iya jurewa ba " Rungume shi Suhaima tayi kafin tace "Yaya ina son ka ina alfahari da kai Allah ya bar ka da Aunty Aliyah, Allah ya jik'an Umma " Jikin su ne yayi sanyi sosai nan yasa hannun shi ya bubbuga bayan ta tare da cewa "Amin Suhaima, maza kije kiyi wanka kizo Babaa Lantana tayi miki gashin kaza mai dad'i irin wanda kike so" K'ara yin kasa da murya yayi kafin ya cigaba da cewa "amman fah mun ci miki ni da Auntyn ki " D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "bakomai Yaya nah Aunty babyn mu yake so ci ai, kai kuma Yaya kwad'ayi ne koh? " Dariya suka sanya dukkan su kafin Suhaima ta tashi d'aukan kayan nata tayi zuwa cikin d'akin ta, lumshe idon ta tayi saboda shak'ar k'amshin turaren wuta da taji ya daki hancina kafin ta bud'e idon, d'akin fes yake ko'ina a gyare tsab kamar tana nan, cire kayan jikin ta tayi ta d'aura wani zani wanda take wanka dashi sannan ta fito daga cikin d'akin zuwa tsakar gida inda toilet yake. Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna nan zaune suna hira, ruwan d'umi ta gani akan murhu nan ta d'iba bokitin wanka ta had'a da ruwan sanyi dai dai yanda take buk'atar ruwan ya kasance ta d'auka ta nufi toilet. Tana shiga ta ajiye bokitin har zata cire zanin ta sai ta had'a ido da abin da tafi tsana wato cockroach aikuwa ta runtse ido tare da sakin ihu da k'arfi ta fito, wanda ya sanya Yaya Aliyu da Aunty Aliyah taso wa da sauri, da gudu Aliyu ya nufi inda Suhaima take ya rik'e ta k'am yana cewa "Suhaima meyafaru lafiya? " Kusan lokaci d'aya suka yi mata maganar, cikin rawar murya tace "Yaya kyenkyaso ce a cikin band'akin " Shafa kanta yayi da hannun shi d'aya d'ayan hannun kuma yana goge mata hawayen fuskarta, tun Suhaima na k'arama yasan ta tsani wannan kwaron
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104