Chapter 50
Chapter 50
min hanci da k'amshi yawu na sai tsinke wa yake " Cewar Suhaima tana shiga madafin Babaa Lantana wadda ke zaune akan kujera 'yar tsugunno tana faman yin aiki. "Tafi can ki ban wuri kina kallo ina faman aiki ko kizo ki taya ni da yake ci ne ai gashi kin taho, toh ko d'and'ane bazan baki ba na megidan nawa ne " Dariya Suhaima tayi tare da cewa "Yanzu duk wannan kamshin da nake shak'a ace baza'a sammin ba haba 'yar tsohuwa ta kaina " "Yarinya duk dad'in bakin ki bazan bayar ba ki bari idan yaci ya rage kyaci sauran " D'an turo baki tayi cikin sigar shagwa6a tace "Nayi ma fushi bazan ci ba " "Da naji dad'i kuwa " Cewar Babaa Lantana tana tattare kayayyakin zuwa cikin kitchen, nan ta shirya farfesun kaza da tayi mishi guda d'aya sai gashashshiya kaza d'aya tasha kayan had'i da mai sai shek'i da tashin k'amshi take, sannan ta dama mishi fura da ruwan randa mai sanyi ta zuba ta a dogon kofin silver, sauran kayan ma a cikin kwanan silver ta zuba sai ta d'ora saman farantin silver, bayan ta gama had'a su ne ta fito daga d'akin girkin tana cewa "Gashi nan na gama shirya komai sauran ya zo ki kasa kawo mishi don nasan an fad'a mishi kina nan zuwa kowanne lokaci zaki iya ganin shi ". Suhaima na dariya tace "Toh naji 'yar tsohuwa sannun ki da aiki don nasan yau kika kwanta sai kin kasa motsi saboda gajiya " Da harara ta bita kafin tace "An gaya miki jikina irin naki ne koda zan yini aiki ras zaki ganni, Allah Suhaima ki rik'e yaron nan sosai saboda yana son ki wallahi na tsakani da Allah " Tana gama fad'in haka ko rufe baki bata yi ba suka jiyo sallamar Sabeer aikuwa da gudu Suhaima ta fad'a d'akin Babaa Lantana, sosai abin ya bawa Babaa Lantana dariya. Kallonta Sabeer yayi had'e da cewa "Matar ke dawa kike dariya haka? ". Cikin dariya tace "Ni da wannan matar da kake kok'arin jajibowa ne daga jin sallamar ka ta kwasa da gudu sai kace wadda taga wani abin firgitarwa ". Murmishi ya saki tare da cewa "Babyn tawa ce kunya ce da ita Babaa, amman gashi ai kin hutashshe ta sai ki min sannu da zuwa " Washe hakora Babaa Lantana tayi tana cewa "Eh mana rabu da ita ni na kwace ka ai tun da babu abin da ta fini " Sosai maganar ta bawa Sabeer dariya, Suhaima na jin su a d'aki tana mirmishi ita kadai. "Ai sai ki fita ki kai mishi tabarma kyayi murmishin da dalili ba ki k'ule d'aki kina murmusawa ba ke d'aya " "Kaiii Babaa " "Ni dai ki tafi maza kin bar mutum a tsaye " Babaa Lantana ta fad'a tana mik'awa Suhaima sabuwar tabarma, kar6a tayi sannan ta fito daman Allah ya taimake ta da hijab d'in ta a jikinta. Fitowa tayi daga d'akin tana d'aga kai suka had'a ido da Sabeer sai kawai ta zuba mishi don yayi mata kyau sosai duk d'an bak'in nan da yayi da rama ya washe tsaf dashi, yana sanye cikin wani black jeans and T-shirt black mai kwala sai kuma ya d'ora wata yellown T-shirt mai dogon hannu daga sama, takalmin shi baki haka ma belt d'in shi sai agogon hannun shi k'irar Gucci shima bak'i, gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake gwanin sha'awa, shagala da kallon shi Suhaima tayi haka shima kallon ta yake don tayi mishi kyau ba kad'an ba. "Idan kun gama kallon junan naku sai ka zauna ni na wuce d'aki zanyi bacci ". Firgigit suka dawo hayyacin su tamkar wad'anda suka tashi daga bacci, saboda jin muryar Babaa Lantana da suka yi a kusa dasu duk kunya ce ta kama su ba irin Suhaima da take ji tamkar ta nutse a k'asa, wayance wa tayi da shimfid'a tabarmar yayi da Sabeer yake sosa kai, murmishi Babaa Lantana tayi ta wuce d'aki ta bar su. Bayan ta gama shimfid'a tabarmar ne cikin sanyin murya tace "Ka zauna mana " Zama yayi yana cewa "Baby ki k'ara kyau mene sirrin " Kunya taji ta sake tuk'unk'une wa cikin hijab, sai kawai ta fara gaida shi amsawa yayi cikin murmishi. Suna gama gaisawa ta tashi ta d'auko mishi abubuwan da Babaa Lantana ta had'a ta ajiye mishi tare da da ruwa da lemo wanda aka aka siyawa bak'i Babaa Lantana ta tura aka kar6o na Sabeer. "Baby nah yanzu baza ki bud'e min fuskar na ganki sosai ba? " D'an murmishi tayi har dimple nata ya lotsa kafin tace "Ni dai kaci abinci kawai nasan mybe ko breakfast baka yi ba " "Kamar kin sani Baby don ruwan tea nasha cup d'aya saboda kawai ina saurin nazo na ganki don nasan idan nazo baby nah zata had'a min irin abincin ta mai dad'i " D'an murmishi kawai tayi cikin zuciyar ta tana sake godewa Babaa Lantana da tayi tunanin dafa mishi wani abin. Zuba mishi tayi ya fara ci yana santi don gashin kazar yayi mishi dad'i sannan yasha furar sosai ba laifi, bayan ya gama ne suka d'an fara hira irin ta masoyan gaske. "Wai ina Sabeer ne? " Cewar uncle Aminu, nan suka dudduba bashi ganshi ba, Daddy ne yace "Mybe yana wajen Babyn tashi can nasan zai gudu " "Kaji ja'irin yaro shine yabar mu salon mu gama yanke magana ya dawo yana cewa ba haka ba " Fad'in Uncle Aminu dariya suka yi kawai irin tasu ta manya, Daddy sai kallo Aliyu yake don yaron ya birgeshi da gani yana da nutsuwa da kamun kai, yana fatan haka itama Suhaima Allah yasa haka take. Nan aka kirawo shi a waya, suna tsaka da hira yaji kiran nashi dole babu yanda zai yi ya tafi wajen su don shi fah gaskiya bai gaji da ganin Babyn tashi ba. Bayan ya je wajen nasu aka fara tsaida lokacin biki inda Sabeer ya nemi a sanya sati uku, su Baba Adamu suka nuna yayi kusa dakyar nan dai aka bar shi a 2 month's, nan suka zube kud'ad'an neman aure har da na sadaki, kasa kar6ar kud'in su Baba Adamu suka yi don gani suke tamkar siyar musu da Suhaima zasu yi, dakyar suka lalla6a su suka kar6a anan suka sake tabbatar wa lallai 'yan uwan Suhaima basu da son abin duniya. Cikin farinciki suka yi sallama da junan su, har sun shiga mota suka ga Sabeer zai bar wajen kamo hannun shi Daddy yayi tare da cewa "Son ina zuwa ne? " Yana sosa kai yace "Daddy zanje yiwa Baby sallama ne " Murmishi manya Daddy yayi tare da cewa "Mun baka 5 minutes kayi sauri don kada dare yayi mana " "Okay Daddy yanzu zan dawo " Yana gama fad'in haka ya wuce da D'an saurin sa don yiwa Suhaima sallama, bashi ya taho ba sai da ya kusan 30 minute's sannan ya dawo su Daddy sai tsokanar shi suke shi dai kawai murmishi yake nan suka yi sallama cikin farinciki suka tafi gida..... Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/14, 8:54 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104