Chapter 53
Chapter 53
Aunty Aliya kenam dariya suka sanya kafin Jiddah ta k'ara cewa "Yanzu sai ki kawo min d'an wake na mu fara maganar da ta kawo ni koh yah amaryar mu? " "Ban yi ba kuwa don ki ji" "Tabd'ijam yarinya kinma isa tun wuri kije ki kawo min " Tashi tayi tana murmishi taje ta kawo mata duk ta zuzzuba ta yawun Jiddah har wani tsinkewa yake, tana gama hadawa ta mik'a mata, kar6a tayi tana cewa "Da kuwa baki yi ba da sai na kaiwa my dear k'arar ki kuma yau sai anganmu a rana " Dariya Suhaima tayi tare da cewa "Aci lafiya Maman twins" Mik'e wa Suhaima ta sake yi don tafiya yiwa Sabeer kunun da yake buk'ata, kallon ina zaki je Jiddah tayi mata duk ta wani tsatstsare ta da idanu abin ya bawa Jiddah dariya don haka tace "Keee Jiddah irin wannan tsatstsare ni da eyes haka " "Dole na tsatstsare da ido mana naga kin mik'e kuma kinsan ban da ishashshen time da wuri zan koma " "Had'a mishi kunu zanyi yanzu zan gama" "What! Wa zaki had'a wa kunu Yah Sabeer koh? " "Eh shi " "Tabbb aini tun da nagan shi nasan yau bazai barmu yin abin da ya kamata ba wallahi duk tak'ura mana zai yi ji har da wani cewa kiyi mishi kunu tsabar sanya mutum aiki " "Eh d'in ina ruwan ki tun da bake aka sanya ba " Ta k'arasa fad'i tana murgud'a bakinta tabar d'akin, Jiddah wadda ta saki baki tana kallon Suhaima da D'an k'arfi yanda zata ji tace "Eheyyy yarinya ni kike fad'awa haka lallai Aunty Aliya kinji Yah Sabeer zai shiga tsakanin mu " Dariya tayi sannan tace "Kun fi kusa don ba'a shiga tsakanin ku yanzu mutum zai ji kunya don anjima kad'an zaku jone ". Cikin shagwa6a Jiddah tace "au haka zaki ce Aunty? " "Eh mana idan na shiga ni za'a bari da jin kunya" Murmishi Jiddah tayi ta cigaba da cin d'anwaken ta suna ta6a hira da Aunty Aliyah. Suhaima kuwa bayan fitar ta a palon tana jin abin da Jiddah tace murmishi kawai tayi, nan ta fara aikin had'a kunun da yake tana da gyadar shi yasa aikin yazo mata da sauk'i don tana son shan kunun gyada shi yasa take ajiye markad'add'iyar gyad'a, bayan ta gama ne ta zuba mishi a dogon jug na silver sai k'aramin cup shima na silver ta ajiye mishi a kitchen sannan ta zuba musu nasu a cup ta d'auka ta koma d'akin Aunty Aliya ta mik'a wa Jiddah da Aunty Aliya nasu. "Yawwa tawan shi yasa kike birgeni kamar kinsan inason sha tun lokacin da kika ambaci sunan shi raina ya biya" "Ai daman nasan Babyn mu naso shi yasa na dama" Bata dad'e da zama ba Sabeer yayi mata text ya dawo ta kawo mishi, nan ta d'auki k'aramin tiren silver wanda ta shirya kunun akai ta kai mishi sun d'an ta6a hira har yasha kunun da yawa kafin kuma yayi mata sallama don akwai inda zasu je da Daddyn shi, mota ya shiga drive yaja suka tafi sai da taga tafiyar shi sannan ta dawo gida. "Lailah ina Majnun d'in? " Fad'in Jiddah wadda take zaune tana kallon Suhaima da take warware veil d'in kanta, d'an yatsina fuska tayi kafin tace "Auuu! Sunan da muka koma kenan? " "Kun ma fi haka " Girgiza Suhaima tayi tana murmishi ta zauna tana shan kunun ta, nan Jiddah ta bud'e k'atuwan bag d'in da tazo da ita ta fara fito da kayan ciki. Duk abubuwan kusan irin su dilka, kurkum da sauran nau'ikan kayan gyaran fata har dasu sabulu na wanka da cream da akayi mishi had'e had'e na abubuwan da suke sanya fata laushi da santsi da turaren da zata nayin amfani dashi idan zata yi wanka, sai kayan gyaran ciki masu kyau da nagarta sosai kayan suke da yawa kuma da ganin su kaya ne masu kyau da inganci amman fah za'a kashe kud'i ba karami ba. Daga Suhaima har Aunty Aliya sakin baki suka yi suna kallon kayan nan Jiddah ta fara yi mata bayanin kowanne yanda zata yi amfani dashi kafin daga k'arshe tace "Abin da ya sanya naje wajen mai mana gyaran jiki na auren mu nace ta had'a miki saboda kun yi nisa, shine nace ta bani wanda zaki amfani dashi kafin sauran sati d'aya biki tazo ta yi miki da kanki amman don Allah Suhaima ki d'aure kiyi amfani dasu suna da kyau wallahi don nagani akaina bama su cutar wa ba ne " Jiyowa tayi ta kalli Aunty Aliya sannan tace "Aunty don Allah ki sanya ido tana yi kullum don so nake Yah Sabeer ya rikice mana " Ta k'arasa fad'i da dariya, Suhaima dai da Aunty Aliya sai addu'a suke yiwa Jiddah don ta hanasu godiya, addu'a sosai tasha ta musamman ta rabuwa da cikin jikinta lafiya. Kayan suka d'auka zuwa d'akin Suhaima bayan sun ajiye Suhaima rungume Jiddah tayi kawai sai ga hawaye yana fita a idanun ta karamcin Jiddah na daban ba k'aramar masoyiyar ta bace batasan da me zata saka mata shi ba. "Haba tawan mene kuma na hawaye share hawayen ki, kin fi k'arfin komai a wajena tun lokacin da Allah ya nufa na ganki naji kin shiga raina, yanzu bari na fara gwada miki yanda zaki yi ki gani " Zama Suhaima tayi nan Jiddah ta fara had'a dilka da sauran abubuwa kayan had'in bayan ta gama ne sai ta fara mutstsuke jikin Suhaima bayan ta gama ne suka jira zuwa 30 minute's kafin ta murje shi sai kuma ta shafa mata had'in kurkum shima sai da ya d'auki 30 minute's d'in sannan tayi wanka da ruwa wanda aka sanya turare acikin shi, tun daga wajen wankan Suhaima ta tabbatar ta fara canjawar fatar jikin ta yanda take zuba santsi da k'amshi ga wani irin laushi da skin nata ya dad'a yi duk da kuwa fatar ta mai laushi ce amman yanzu ta k'ara laushi. Tana fitowa ne kuma Jiddah ta gama had'a garwashi tana jiranta tana zuwa ta zuba turaren jiki acikin wutar nan Suhaima ta shiga tana turare jikinta yayin da Jiddah ta fito ta barta a d'akin, sai da ta d'auki wajen 10 minutes sannan ta gama turaren kafinx ta zauna ta shafa cream d'in nan bayan ta gama ne ta zura wata yellow d'in gown har k'asa sai dai hannun vest ne da ita, wani irin mugun kyau na daban Suhaima ta k'ara yi ga gashin ta mai kyau na asalin fulani mai laushi da santsi ya zubo mata a kafad'unta tana cikin tajewa Jiddah ta shigo. "Wow! Suhaima kin ganki kuwa yanda kika koma tabbb gaskiya Yayana zai more " Ta k'arasa fad'i tana d'auko wayanta pic's ta fara d'aukan ta, cikin dariya Suhaima tace "Don Allah Jiddah ki daina d'aukan pic's nawa please kalli fah ki ga yanda rigar take" "Ina ruwa mijin ki zan nuna wa ya bani kyauta" Ta fad'i hakan tana daukan Suhaima lokacin da take dariya, ita kanta Jiddah pic d'in yayi matuk'ar birgeta ba kad'an ba. D'an waro ido waje tayi kafin tace "Haba Jiddah kada ki tura mishi please " Ta fad'i tana langa6e kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104