Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,192 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'aya cikin jikokin shi, anya shine kuwa da hankalin shi ya aikata wannan abin ko dai mafarki yake yi ba gaske ba ne kamar wani mutum mutumi haka ya koma ya rasa me zaiyi ma. Dakyar Daddy ya lalla6a su Mumy da Hajjah suka fita don a bawa Doctor damar duba Sabeer haka Daddy yazo ya janye Alhj Ahmad dakyar suka fita tare da jan k'ofar bedroom d'in. Likita yana cikin duba Sabeer yaga ya bud'e idon shi tare da tashi ya zauna cike da mamaki Doctor yake kallon shi, kamo hannun likitan Sabeer yayi sannan yace "Doctor ina son abin da zan fad'a maka yanzu ka sanar da iyaye na bana son a samu matsala fah" Gid'a kai likita yayi kafin yace "Okay baza'a samu matsala ba insha Allah " A hankali Sabeer ya matso kusa da likitan kafin ya fara yi mishi magana cikin k'asa k'asan murya, bayan ya gama yi mishi maganar ne ya koma ya kwanta tare da rufe idon shi. Suna zaune jugum jugum a parlour kowannen su ya rafka tagumi suna tunani ba mai yin magana a tsakanin su, k'arar bud'e door suka ji da sauri suka mik'e tsaye tare da nufar Doctor da sauri kowanne na jefo mishi tambayar jikin Sabeer. D'an share zufa likitan yayi yayi shiru baiyi magana ba, cakumar wuyan shi Alhj Ahmad yayi tare da cewa "Kai wanne irin wawa ne muna maka magana ya jikin Sabeer zaka zuba mana ido kana kallon mu kamar ka samu tv" Ba k'aramin shak'a likita yasha ba dakyar Daddy ya cire hannun Alhj Ahmad daga wuyan shi, kafin yace "Abba mu bi a hankali please " Zama suka yi sannan likita ya shafa wuyan shi tare da jujjuya shi yace "A binciken da nayi damuwa ce tayi wa Sabeer yawa sosai wanda a yanzu yana d'auke da hawan jini, idan kuka cigaba da matsanta mishi da 6acin rai ko ku k'i mishi abin da yake so idan ranshi ya 6aci zuciyar shi zata iya bugawa na lokaci d'aya don haka ku kiyaye " "K'arya kake zuciyar Sabeer bazata ta6a bugawa ba " Cewar Alhj Ahmad cikin tsawa gaba d'aya hankalin shi a tashe yake, "a cigaba da kwantar mishi da hankali a bashi abin da yake so, zanje na kawo maganin da zai sha yanzu " Babu wanda ya kula shi haka ya zame ya tafi sannan suka shiga cikin d'akin inda Sabeer yake kwance, nan Alhj Ahmad ya zauna kusa dashi tare da rik'o hannun Sabeer yana mai nadamar abin da yayi mishi, a lokacin Daddy ya kirawo mai gyaran k'afa ya fara gyarawa Sabeer kafar shi kuka sosai Sabeer yasha shi a lokacin haka Hajjah da Mummy tare da Alhj Ahmad sun zubar mishi da hawayen tausayi Daddy ne kawai yayi dauriya ta rik'e Sabeer har aka gama gyara mishi kafin daga k'arshe wani wahalallen bacci ya sake d'aukan shi sai sauke ajiyar zuciya yake....... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/6, 8:12 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz Dis page is dedicated to my Biebie dee ina tayaki murnar k'arin shekara Allah ya k'aro shekaru masu albarka Allah ya baki miji nagari wanda zai kular mana dake muzo musha biki 💃🏻😍😅. _fan's kuyi hak'uri akan rashin yi muku typing kwana 2 akwai uzirin da ya dakatar da ni but yanzu insha Allah zan cigaba da yi muku daidai iyawata, inason ku oll my fan's_❣ *PAGE 48-49* Sai after mangarib Sabeer ya tashi daga wahalallen baccin da ya d'auke shi, lokacin da ya tashi zugin k'afar ya ragu babu laifi nan ya yunkura ya tashi bathroom ya shiga alwala yayi ya fito yana d'ingishi haka ya gabatar da sallahr la'asar da ta tsere mishi tare da mangarib, bayan ya idar ya zauna yin addu'o'in neman za6in Allah akan neman auren Suhaima, da haka har aka kirawo sallahr ishsha ya gabatar. Bayan ya idar ne ya tashi ya shiga bathroom wanka yayi da ruwa mai d'umi kafin ya fito ya shirya cikin sleeping dress koma wa yayi ya kwanta a ringingine ya fad'a kogin tunani, ta yanda zai tunkari k'auyen su Suhaima don neman soyayyar ta, yana cikin haka 'yan uwan shi da k'annen Daddy da kuma matansu suka shigo duba Sabeer, dakyar ya iya k'ak'alo yak'en dole ya sanya saman fuskar shi yana amsa musu sannun da suke mishi, kowanne fuskar shi da tausayin Sabeer ganin yanda k'afar shi ta kumbura sai wurin 9 na dare suka bar bedroom d'in nashi wanda har zuwa lokacin ba ga Mumyn shi ba da Hajjah. Bayan fitar su babu dad'e wa Daddy ya shigo bedroom d'in bayan shi kuma 'yar aikin Mumy ce da babban plate a hannun ta saman shi cike da kaya ajiyewa tayi saman k'aramin table d'in d'akin sannan tayi wa Sabeer sannu da jiki ko amsawa bai yi ba ta fita don shi ba wannan ne a gaban shi ba. "Son ya kake jin jikin naka?" D'an yatsina fuska yayi kafin yace "Daddy na samu sauk'i" D'an ajiyar zuciya Daddy ya saki tare da cewa "Allahmdullilah Son naji dad'in abin da ka ce, oya zo kaci abinci nasan rabon ka da abinci tun breakfast da kayi " Girgiza kai Sabeer yayi tare da cewa "Na k'oshi Daddy" D'an zaro ido yayi tare da cewa "What! Son kanason illata kanka ne? " Sai kuma ya sassauta murya cikin sigar rarrashi yace "Haba Son tun da na amince da buk'atar ka ya kamata kaci wani abin zan jure duk wata matsala da zan fuskanta a wurin Abba, Hajjah da kuma Mumyn ka duk don farincikin ka ". Kallon Daddy yayi sai yaga kamar ya fad'a a fuskar shi wani tausayin Daddy ne ya kama Sabeer har yana kok'arin fitar da kwalla duk don farincikin shi Daddy ya zama haka, yasan yanda bai ci wani abincin kirki ba yinin yau haka shima ya zauna. Tashi tsaye Sabeer yake kok'arin yi da sauri Daddy ya taimaka mishi ya tashi tsaye zuwa saman kujera wanda kujeru guda biyu ne kacal daga gefe tsakiyar su kuma table ne nan Daddy ya zaunar da Sabeer a d'aya daga cikin kujerar, sannan shima ya zauna a baki ya fara baiwa Sabeer abinci haka shima Sabeer yake bawa Daddyn shi a baki. Bayan sun kammala ci ne Daddy ya lalla6a Sabeer yasha maganin shi don sam baya k'aunar shan magani, k'ofar bedroom d'in aka bud'e aka shigo kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kanshi gaban shi yana fad'uwa, Mumy ce ta shigo fuskar ta a had'e babu alamar fara'a bata yiwa kowa magana ba ta wuce bathroom babu dad'ewa ta fito hannun ta rik'e da wani d'an madaidaicin bowl ruwan d'umi ne a cikin shi sai wani small towel a hannun ta. Inda Sabeer yake ta nufa tana zuwa ta zauna kan carpet tare da d'aukan k'afar Sabeer mai ciwon ta d'ora saman k'afar ta, towel d'in ta sanya cikin ruwan d'umin ta fara gasa k'afar Sabeer, daga Sabeer har Daddyn babu wanda ya samu fuska wajen Mumy balle su yi mata magana, runtse ido Sabeer yayi wani rad'ad'i da zafi yana shiga cikin zuciyar shi gefe d'aya na cikin zuciyar shi kuma yana tunanin hanyar

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});