Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 81

Chapter 81

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta fashe da kuka ganin yanda komai ya jagule mata lokaci d'aya ta rasa d'anta da mijinta!........ _kuyi hak'uri da wannan fan's_ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/16, 10:12 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 101-102* Kallon ta Dr Ahmad d'an fillo yayi cikin jin tausayin ta yace "Faridah kiyi hak'uri babu inda zaki je har idan ina raye, ki cigaba da zaman ki kamar da nasan ta inda zan 6ullowa al'amarin " Gid'a kanta take kamar k'aramar yarinya tana goge hawayen face nata, bayan ya gama rarrashin ta ne sai ya tafi yayin da ita kuma Mumy ta nufi upstairs zata fara hawa steps sai ga Daddy nan zai sakko. Suna had'a ido ya sakar mata harara kafin yace "Me kike har yanzu baki bar min gida na ba!? " Ko kallon inda yake Mumy bata yi ba ta wuce shi da sauri zuwa side d'inta da kallo ya bita kafin ya girgiza kanshi kawai, ya wuce zuwa 6angaren masu aiki ya bud'e Larai da take cikin d'akin wadda ta kasa zaune ta kasa tsaye tsabar firgita da razana. Jin an bud'e k'ofar nan ta jiyo a rikice ganin Daddy ne ya sanya ta zubewa a k'asa cikin tsorata tace "Don girman Allah Alhaji kayi hak'uri ka barni na tafi nayi alkawarin bazan sake maimaita abin da nayi ba wallahi " "Ya isa haka zan barki ki tafi amman kiji tsoron Allah a duk inda kike kisan yana ganin ki komai zaki aikata, ina son ki tafi kada ki k'ara dawo min gida " Abin da ya sanya Daddy kyale ta ganin ga babbar mai sanyawa a aikata laifi amman an hanashi d'aukan mataki akanta shi ya sanya rabuwa da ita, nasiha yayi mata kan ya bar d'akin.Aikuwa cikin rawar jiki ta sungumi ghana must go d'inta ta k'ara gaba da sauri ko waiwaye bata yi. Cikin kwana 2 gidan ya koma shiru babu walwala acikin shi kamar da, Sabeer baya iya zuwa ko'ina kullum yana cikin bedroom a kwance yana tunanin ta yanda zai tunkari Suhaima da wanne ido zai kalle ta yace ta koma gidan shi baya ga cin mutuncin da yayi mata tare da 'yan uwanshi tun da ta tafi wajen 7 months bai je inda take ba. Wad'annan tunanin ne idan yayi suke matuk'ar hargitsa mishi kai ya rasa sukuni cikin zuciyar shi, ta 6angaren Mumy da Daddy ma babu wata jituwa tsakanin su kowa yana side shi gashi babu mai shiga harkar wani acikin su, duk da Mumy kusan kullum sai tayi kuka a 6oye saboda ganin d'anta da mijinta sun guje mata amman bata ta6a nuna musu hakan a fili ba. Sabeer kasa hakura yayi sai kawai ya nemi Jiddah a waya dakyar Jiddah tayi picking wayar saboda haushin shi take ji ya rabata da Suhaima da tasan sanadin auren Yah Sabeer zai kawo matsala a tsakanin ta dasu Suhaima da bata bayar da goyon baya. Murya ciki ciki ta amsa mishi sallamar tashi, d'an murmishin yak'e yayi cikin zuciyar shi yana cewa, Jiddah da zaki fahimci halin da nake ciki yanzu da kin tausaya min amman a fili sai yace "Uhmm Jiddah kina fushi da ni koh? " "Ni kuma! Me kayi min da har zanyi fushi da kai? " "Saboda na rabu da k'awar ki mana alhalin kina sane da ban saketa ba saboda son da nake mata " "Tabd'ijam Yaya a haka kake son Suhaima bayan baka tsaya kayi bincike ba ka kore ta daga gidan ta? " Wani irin abu ne ya taso ya lullu6e mishi cikin zuciyar shi na tsananin nadamar abin da ya aikata kafin ya sauke numfashi mai zafi yace "Ina son Suhaima Jiddah har yau amman nasan bai kamata na kore ta ba, bincike ne farkon abin da ya kamata nayi sai na kasa controlling d'in zuciya ta har takai da na aikata hakan, amman yanzu na gane gaskiya " "Da gaske kake Yaya an gane wanda ya shirya makircin nan!? " "Ehhh Jiddah duk wannan shirin Mumy ne don kawai ta raba ni da Suhaima " No wonder ai nasan itace zata aikata hakan don kuwa ita nake zargi fiye da kowa, fad'in Jiddah cikin zuciyar ta kafin ta d'ora da cewa "Alhamdullilah nagodewa Allah da ya sanya k'awata ta fita daga zargi " "Yanzu ki fad'a min ta ina zan bi don na dawo da mata ta na kasa tunanin mafita komai ya hargitse min wallahi" "Tabd'ijam Yaya babu ruwana ni kaina ka shafa min laifi wajen Yah Aliyu sau biyu nake zuwa yake korata baya barina na shiga gidan haka nake dawo wa, bani na aikata laifi ba amman Yah Aliyu ya kasa tsayawa ya fahimci ne babu hannuna cikin aikata wannan abun wallahi " Ta k'arasa maganar cikin rawar murya hawaye na zuba daga idanun ta, wani fad'uwar gaba Sabeer ya tsinci kanshi aciki kafin ya iya bud'e baki dakyar yace "Yanzu kenan babu wani idea a wurin ki wanda zai sanya ni zuwa wajen Suhaima na dawo da ita? " "Ni dai shawarar da zan baka kawai ka je wurin Suhaima duk abin da Yah Aliyu zai yi maka ka hakura ka daure zuciyar ka har zuwa lokacin da zai sakko ya hakura, don Yah Aliyu mutum ne mai zafi amman yana da tausayi sosai amman ina mai baka shawara kada Mumy taji labarin tafiyar ka can don zata iyayin wani abun don kawai Suhaima kada ta dawo wajen ka " "Nagode k'anwata" "Babu komai Yaya Allah taimaka " Dakyar ya iya cewa Ameen sannan suka yi sallama, tunani ya fad'a sosai kafin daga k'arshe ya fito daga bedroom d'in shi. Parlour ya fito ya tarar da Daddy yana zaune yana aiki a laptop yayin da Mumy take ta shirya kan dinning table duk da ba cin abincin suke ba wani lokacin idan tana free tana kok'arin had'a musu abinci da kanta. "Daddy ina son zan tafi England akwai wani abu da zanyi mai amfani acan " Kallon shi Daddy yake cikin mamaki kafin yace "Son me zaka je kayi acan? " "Daddy abun sirri ne idan na dawo zan fad'a maka shi " Gid'a kai Daddy yayi kan yace "Okay bari na sama maka visa wajen friend d'ina " "No Daddy na gama komai nan da 2hrs jirgi zai tashi " Kallon ban yarda da kai Daddy yake yiwa Sabeer, yayin da ya d'an yi murmishi kawai yana kauda kanshi don baya son had'a ido da Daddy. "Shikenan Son sai kaje ka fara shiri, amman kwanaki nawa zaka yi?" "Daddy ni kawai sai an ganni huh don na gaji da zaman gidan " "Ni kaina Son na gaji da zaman don haka mybe na biyo ka can sai kawai mu huta " Murmishi Sabeer ya d'an yi hannun shi zube cikin aljihun shi yace "Okay Daddy amman ni sai na fara yin gaba " 'Yar dariyar farinciki Daddy yayi ganin yanda yau Sabeer ya sake yana hira har da murmishin shi, akwai abin da Son ya shirya yi dole na bincike shi, fad'in Daddy cikin zuciyar shi. Sabeer bai d'auki wani abu masu yawa ba kayanshi set 3 ya sanya cikin k'aramar

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});