Chapter 68
Chapter 68
kallon ta kawai jinshi yake kamar a mafarki yau wai shine da Suhaima a matsayin ma'aurata, sannan abin da su Mumy suka yi yaji haushi sosai Jiddah ce take fad'a mishi a waya bayan tabar gidan Suhaima, da yaso yin magana dasu Mumy but Daddy ya rarrashe shi kan yayi hak'uri komai mai wuce wa ne wataran sai labari ya zuba musu ido kawai, shi ya cigaba da kula da matar shi don bata da kowa a kusa sai shi. Kiran sallahr mangarib ne ya tashe shi daga zaunen, addu'a yayiwa Suhaima sannan ya tashi ya fita side nashi ya shiga yayi alwala ya wuce masallaci sai after ishsha ya dawo gidan, yana shigowa farfajiyar gidan ya had'u da driven Jiddah bayan ya gaida Sabeer ne ya bashi sak'on Jiddah na basket mai d'auke da foodflaks 3 sai Jug kar6a Sabeer yayi sannan ya d'auko kud'i ya bawa driven, sosai driven yayi godiya kafin ya tafi, shiga cikin gidan yayi hannun shi rik'e da basket d'in cikin zuciyar shi yana jinjinawa Jiddah da matuk'ar kok'arin da take akan su, yaji dad'in kawo abincin nan daman yanzu yake shirin fita yi musu take away sai gashi na kuma ta hutar dashi, addu'a yayi mata cikin zuciyar shi na Allah ya sauke ta lafiya. Ajiye basket d'in yayi saman dinning table sannan ya wuce bedroom ya tarar har Suhaima ta tashi tana bathroom don yaji k'arar zubar ruwa, don haka sai yawuce nashi side d'in yayi wanka ya shirya cikin wani catton na kayam bacca and sky blue ya fesa different perfumes masu dad'in kamshi, tukunna ya koma bedroom d'in Suhaima ya tarar har ta fito daga bathroom sallah ma take. Shiga yayi cikin d'akin ya zauna kan sofa ya d'an lumshe idanun shi, bacci ne sosai cikin eyes nashi ga gajiya, tana idar da sallahr mangarib and ishsha ne bayan tayi shafa'i da wutiri tare da addu'o'in ta ne sai ta tashi ta cire hijab d'in jikinta. Tana sanye da wata sleeping dress white tsayin ta iyakar shi tsakiyar cinyar ta sai zanin da ta d'aura tayi sallah, batasan Sabeer ya shigo ba sai kawai ta warware zanin ta ajiye shi sannan ta k'arasa wajen dressing mirror ta taje gashinta tare da sanya perfumes ajikinta. Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta yayi luf ne kawai ajikin sofa, tuni ya fara jin wani canjin yanayi a jikinshi don kuwa Babyn shi tayi mishi kyau amman sai dai ya had'iye abin da yake ji dole yabar ta taji sauk'i. Tashi yayi tsaye yana wani binta da kallon k'asan ido ya k'arasa inda take tana d'aure kanta da ribbon hannun shi ya sanya ya cikin gashin kan nata yana wani yamutsa shi, a d'an tsorace ta jiyo ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya........ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ✍🏻 [4/9, 5:00 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 83-84* Ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tare da juya kanta, rungume ta yayi ta baya ya sanya kanshi cikin gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar kamshin daddad'an perfumes d'in ta saukar d'umin numfashinshi a wuyanta shi ya saukar mata da wani irin kasala, hannun shi ya sanya yana shafa dogon hannun ta daga kafad'a zuwa 'yan yatsun hannun, kasa jure abin da yake mata tayi sai kawai ta juyo tare da fad'awa kan kirjin shi tsam ya rungume ta ajikin shi yana saukar da ajiyar zuciya, suna nan tsaye wajen 5 minutes ahaka kafin kuma ya bud'e baki yace "Baby muje kici abinci sai kisha magani " Hannun ta ya rik'o zuwa parlour har kan dinning table ya zaunar da ita kan kujera, sannan shima ya zauna yana zuba musu abinci, kasa barinshi tayi da ya zuba musu ta kar6i serving spoon tana zuba musu. Abaki suka dunga bawa junan su har suka k'oshe sannan ta tattara kayan ta kai kitchen, ta dawo ta gyara dinning table d'in, zama suka yi a parlour suna kallo tare da ta6a 'yar soyayya. Sai da Sabeer ya bawa Suhaima hutun kwanaki biyu sannan aka d'ora daga inda aka tsaya, soyayya, kulawa da duk wata kauna suke nuna wa junan su, cikin farinciki da kwanciyar hankali suke abin su, babu mai zuwa gidan sai Jiddah ce ke lek'o su, sai dai waya da take yi dasu Yaya Aliyu kullum Sabeer kuwa yana kok'arin zuwa gida gaida iyayen shi, amarcin su suke sha yanda suke so babu mai tak'ura musu ko house girl basu da ita Suhaima ta hana Jiddah ta kawo mata tace ba yanzu ba. Akullum cikin nuna wa junan su so suke biyayya sosai da kyautatawa Suhaima ke yiwa Sabeer yayin da shima yana kok'arin wajen sanya ta farinciki koyaushe, idan ka shiga gidan su kuwa sai ya birge ka saboda tsananin yanda suke kula da junan su. Motarta tuni Jiddah ta aiko mata da ita gashi Sabeer ma ya bata kyauta ta mota mai matuk'ar kyau da tsada da sabuwar tsadaddiyar phone, sosai Suhaima tayi mishi godiya ta nuna mishi dad'in da taji addu'a sosai yasha ta daga bakin ta, gashi yana koya mata driving duk weekend da yamma zasu fita yana koya mata, yanzu matsalar ta d'aya shine ta cigaba da karatu amman tun da tayi mishi maganar sau d'aya ya nuna ba yanzu ta hak'ura duk da tsananin son da take yiwa karatun ta cigaba da farantawa mijinta rai ta barwa Allah za6in alkhairi akan makaranta. _*After 3 Month's*_ Zuwa wannan lokacin idan kaga Sabeer da Suhaima sai kayi mamaki sun k'ara wani kyau musamman Suhaima ta k'ara cika sosai tayi 'yar kiba kad'an, bata fita ko'ina sai zaman gida kullum sau d'aya ta sake jarraba zuwa gidan su Sabeer amman har ta karaci zaman ta babu wanda yace mata ci kanki har gwara lokacin da Daddy ya dawo ya zauna sun d'an ta6a hira dashi amman ko a fuska bata nunawa Sabeer jin haushin abin da suka yi mata, Sabeer a lokacin tuni ya fara aiki da company d'in shi da Daddy ya bashi kyauta. Zaune suke a garden da wani yammaci lokacin damina ne garin yayi luf luf dashi sai iska mai dad'i da take kad'awa mai ratsa jiki da sanya mutum nishad'i. Suhaima tana sanye da wani wandon jeans iyakar shi rabin cinyar ta blue sai half vest white, yayin da Sabeer kuma yake sanye cikin 3quater kawai suna zaune kan wani babban carpet ga kayan fruits da juice da ruwa a gefen su. Sabeer ne yake danna laptop d'in shi da hannu d'aya, d'ayan hannun kuma yana rungume da Suhaima ta gefen shi, cikin shagwa6a ta bud'e baki tace "Ni Allah ka bar aikin nan kazo ka goya ni idan ba haka ba zanyi maka kuka " D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai wani turo baki take murmishi yayi tare da jan hancin ta yace "Oh Baby rigima naji zan goya ki amman kiyi min afuwa na k'arasa aikin nan please " D'aga kanta tayi, da sauri ya rik'o d'ayan hannunta yace "Amman ban da kuka please" D'an murmishi tayi sannan tace "Toh bazan yi ba " "Yawwa 'yammata na " Cikin 10 minute's ya k'arasa aikin tare da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104