Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

labule na k'ofa dana window kafin su fito kuma su shiga d'akin Aliyah sai ga Aliyu ya fito da k'aramar katifa ta k'aramin gado ya sanya d'akin Aliyah kuma ta shimfid'a mishi zanin gado a jikin katifar ta kunna turaren wata na tsinke sai d'akin ya fito fes dashi, Aliyu ya d'auki jakar Sabeer ya shigar mishi da ita kafin kuma su d'unguma shi da Sabeer su tafi masallaci don yin sallahr ishsha.... Aishat A Muh'd 💃🏻 [2/18, 5:01 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 53-54 Bud'e labulen d'akin Aliyah tayi tare da shigowa zama tayi kusa da Suhaim wadda ta kwanta rub da ciki a saman gadon ta, dafa bayan ta tayi kafin tace "Suhaima tashi mu yi magana " Tashi Suhaima tayi zaune tana goge hawayen fuskar ta da hannunta, kallon mamaki Aliyah take mata kafin tace "Me yasa kika yi mishi haka Suhaima?, haba Suhaima bansan ki da halayyar wulak'anta mutane ba, ki tuna saboda sanadin son ki fah ya bar gatan shi da komai nashi na jin dad'i ya dawo nan k'auye wanda bai ta6a rayuwa acikin irin wannan yankin ba ya aminta zai jure kowacce wahala indai zai same ki, koda da iya abincin mu ma kafin ya saba aiki ne zai hak'ura ya jure duk don A SANADIN SON KI, haba Suhaima ki tausaya mishi kada ki bashi wahala don na tabbatar Sabeer son ki yake tsakani da Allah ba yaudarar ki yake, idan yaudara ce ma bazai zo har nan ba don haka kiyi tunanin kafin ki yanke hukunci tukunna " Zum6ura baki Suhaima tayi tare da cewa "Ni gaskiya Aunty bana son Sabeer hasalima kinsan na tsani auren mai kud'i saboda gujewa wulak'anci, musamman gidan su Sabeer tunda na baki labarin abin da suka yi min" D'an shiru Aliyah tayi tana d'an tunani kafin tace "Kina da gaskiya don wannan amman ni ina mai baki shawara kiyi tunani sosai kafin ki yanke hukunci,tare da addu'ar neman za6in Allah kada ki yanke hukunci da gaggawa" Gid'a kai Suhaima tayi kawai tare da cewa "Ni bama zan so shi ba" "Hmmm na dai ji ki Suhaima kawai amman wannan zakad'ed'en sauryin ne kece bakya sonshi kawai ra'ayin ki ne ya hana ki tsayawa kiyi tunanin kin fad'a son Sabeer daga irin kallon da kike mishi d'azu " Wayyo aikuwa Suhaima ji take kamar ta rusa kuka jin abin da Aunty Aliyah ta fad'a mata, zum6arar baki tayi tare da kwanciya ta juyawa Aliyah baya, abin ya bata dariya tashi tsaye tayi tare da cewa "Abincin ki yana kitchen fah kije ki ci kada ya huce " Tana gama fad'in haka ta fito daga d'akin, nan ta tarar da Sabeer da Aliyu sun dawo bayan tayi musu sannu da dawowa ta yiwa Sabeer sai da safe ta wuce cikin d'aki. Sun d'an jima suna hira kafin Sabeer ya wuce d'akin da aka sauke shi bayan yayi wa Aliyu sai da safe, yana tafiya yana waiwayar d'akin Suhaima ko Allah zai sanya ya hango ta don kuwa yana son sake sakata cikin idanun shi kafin yayi bacci, Aliyu yana kallon yanda yake kallon d'akin Suhaima nan ya sake tabbatar wa Sabeer yana son Suhaima bana wasa ba, amman mene dalilin k'in amincewar Suhaima na ta kar6i soyayyar Sabeer?. Sabeer yana shiga d'akin sai yaji shi kamar wanda aka sanya shi a akurki duk da d'akin yana da d'an girma kuwa hakan bai hana sa Sabeer ganin k'ank'antar shi ba irin wanda ya saba kwanciya da shi ba. Zama yayi gefen katifar yaji ta tik'irk'ir tauri sosai, ga wani hucin zafi da d'akin yake fitarwa alamar dai ba'a yin amfani dashi a rufe yake sai shegen kukan sauro da ya addabi kunnen shi, ga ba wadataccen haske wata 'yar k'aramar fitila ce kawai a rataye jikin k'usa a bango mai irin mai batir d'in nan, zabga tagumi Sabeer yayi yana tunanin yanda ya tsinci kanshi inda bai ta6a tsammanin ganin a haka ba koda a mafarki sai gashi kwatsam lokaci d'aya ya tsinci kanshi aciki ikon Allah kenan. Zumbur ya mik'e kamar wanda aka tsikara sakamakon wani fitsari da ya matse shi, wayyo Allah nah yanzu ta ina zan fara shiga toilet d'in su, fad'in haka cikin zuciyar Sabeer yana faman matse k'afa, fuskar nan tashi tayi kalar tausayi tamkar wanda zai fashe da kuka kasa jurewa yayi kawai ya tashi da sauri ya fito daga d'akin zuwa tsakar gidan. Ba kowa a tsakar gidan ga duhu yayi tsit kake ji, yana nan tsaye sai ga Suhaima ta fito a d'aki zata shiga kitchen d'ebo ruwa suka kusan cin karo da Sabeer saboda duhu gashi babu wadataccen hasken farin wata, ba k'aramin tsorata tayi ba ta d'auka ko wani aljanin ne amman lokacin da ta fuskanci Sabeer ne sai kawai ta dake tare da d'aure fuska zata wuce daga sauri yasha gabanta ya tsaya "Malam lafiya? " "Uhm ina son ki nuna min toilet " Da hannu ta nuna mishi ba tare da tayi magana ba ta wuce shi ta d'auko ruwan ta shige d'aki ko kallon inda yake bata sake yi ba, buta ya d'auka ya wuce cikin toilet d'in a d'an tsorace, duk da a duhu ne hakan bai sanya shi gane tsabtar da band'akin yake dashi ba a tsorace yayi abin da zai yi ya fito yana share gumi sai kace wanda yayi tseren gudu duk gumin tsoro ne, da sauri ya wuce d'akin ya rufe kafin ya kwanta saman katifar. A cikin wannan daren ya zame wa Sabeer daren da bai ta6a tsammanin zai irin shi a wannan duniyar ba saboda yanda zafi da sauro suka hanashi runtsawa, idan zafin ya isheshi sai ya cire kayan jikin shi iya vest da 3quater ne kawai a jikin shi sai buge bugen sauro yake yi ko baccin kirki ya kasa samu ga wani tsananin ciwon kai da ya kamashi saboda gajiya ga rashin bacci. Washe gari kuwa jikin Sabeer yayi luhu luhu da cizon sauro abin ka da d'an hutu kuma farar fata duk tayi ja tundaga fuskarshi kuwa har jikin shi inda kaya bai rufe ba, idanun shi sun yi ja sosai ga wani zazza6i da ciwon kan ya saukar mishi dashi wajen asubah, har gari ya waye yana kwance a d'aki bai iya fitowa ba sai da Aliyu ya shiga ya ganshi kwance sai rawar sanyi yake ya tukunkune waje d'aya. Cikin tashin hankali Aliyu ya k'arasa tare da cewa "Subhanallah! Sabeer baka da lafiya ne? " D'an murmishin yak'e yayi hawaye na zuba a idanun shi na zafin ciwo yace "Zazza6i ne yake damuna da ciwon kai ko zaka taimaka min da paracetamol? " "Sannu Allah ya baka lafiya, bari na d'auko maka amman ka d'aure ka fito sai kayi brush kaci wani abin kafin ka sha maganin " D'aga kai kawai Sabeer ya iya yi sannan Aliyu ya taimaka mishi suka fito tsakar gidan bayan ya d'auko mishi maclean da brush nashi cikin bag d'in da ya taho da ita. Aunty Aliya da Suhaima suna zaune a kan tabarma ga breakfast a saman tabarmar da yake tare suke karyawa, Aunty Aliya batasan sand ta mik'e tsaye ba

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});