Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,189 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duk lokacin da ta ganshi ba k'aramin tsorota take ba shi yasa yake yawan yi feshin maganin kwari saboda ita. "Kiyi k'anwata bari na fitar miki da ita kin ji? " D'aga kanta tayi kafin ta cikata ta rik'e Aunty Aliyah, toilet d'in ya shiga da tsintsiya ya maketa tukunna ya fito da ita ya yar cikin shara, sai lokacin hankalin Suhaima ya d'an kwanta amman duk da haka sai da tace "Yaya ka duba babu wata " "Na duba Suhaima babu komai kije kiyi wankan ki " A tsorace ta shiga band'akin don ji take kamar zata sake ganin wata ko ma ta hak'ura da wankan gaba d'aya, yayin da suka juya suka koma inda suke zaune suna hirar su daga k'arshe Aliyu ya fita daga gidan gaba d'aya. Sai fitowa daga wanka tayi taga baya nan sai Aunty Aliyah a zaune, tsokanar ta ta fara yi na ihun da take musu murmishi kawai tayi ta shige d'aki, shiryawa tayi cikin wata gown mara nauyi mai k'aramin hannu ta gyara gashin kanta sannan ta sanya hula ta fito nan inda Aunty Aliyah take zaune hira suke tana cin gashin naman da akayi mata cikin jin dad'i saboda dad'in da yayi mata bayan ta gama ci ta d'ora da madarar shanu mai d'umi, suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib suka yi alwala kowa ya wuce dakin shi don gabatar da faralli. ****************** Tun lokacin da Sabeer ya zube kan kujera ya had'e kanshi cikin jikin shi, yana jin fitar Suhaima ya kirawo driven shi a waya yazo ya kai Suhaima gida yana gama wayar ya koma ya kwanta saman kujera ya tuk'unk'une jikin shi waje d'aya hawaye ne masu zafi suke zuba cikin idon shi. Wai shi yau yarinya k'arama take duban tsabar idon shi tace bata son shi, wad'anda suka fita girma da komai ma na wayewa suna nuna mishi so tamkar su cinye shi amman ita ta samu ma yace yana son ta zata wulak'anta shi, wayyo Allah nah yanzu ya zanyi gashi son yarinya ya shiga zuciya ta dole nasan yanda zan shawo kanta ta amince ta kar6i soyayya ta, duk wannan maganar cikin zuciyar shi yake tashi zaune yayi idon shi sunyi ja sun kumbura kallo d'aya mutum zai mishi yasan cewa yayi kuka daman abin ka da shagwa6a66e bashi d wahalar yin kuka, kanshi ciwo yake tamkar ya cire haka yake ji. "Dole ki soni Suhaima sai nasan yanda nayi na cusa miki son na cikin zuciyar ki, A SANADIN SON KI zan iya shiga kowacce matsala na sani amman har idan zan samu nasarar ki soni komai mai wuce wa " Yana gama fad'in haka ya tashi tsaye kafin kuma ya fita daga parlourn a compound na gidan ya had'u da driven da ya mayar da Suhaima gida mota kawai Sabeer ya shiga ya zauna nan driven ya gane me yake nufi da sauri shima ya tashi ya shiga motar yayi mata ya tada ita suka fita daga gidan. "Yalla6ai ina zamu je? " Driver ya buk'aci son inda zasu je, dakyar Sabeer ya iya cewa "gida zaka kai ni" Yana gama fad'in haka yayi shiru nan driver ya cigaba da tuk'i har suka k'arasa gida ko gama dai daita parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar. Daf da zai shiga part d'in su ya kusan cin karo da Alhj Alhmad d'an fillo wato kakan shi, ganin Sabeer d'an lele a yanayin da bai ta6a ganin shi a haka ba yasa gaban shi ya fad'i tare da kamo hannun shi yace "Sabeer what wrong with U?" Fincike hannun shi Sabeer yayi tare da yin gaba don gaba d'aya ba'a cikin nutsuwar shi yake ba yana tafiya hawaye na zuba cikin idon shi " Cikin tashin hankali Alhj Ahmad ya bishi a baya yana kiran shi amman ko waiwayen shi bai yi ba, yana shiga parlourn a dai dai lokacin mai aiki ta fito daga kitchen hannun ta d'auke da babban farantin saman shi foodflaks ne da plates zata jera a dinning table. Sabeer yana k'arasa wajen zai haura stairs ya sanya hannun shi ya ture abin da ke hannun ta, ai kuwa gaba d'aya tayi baya ta zube haka foodflaks da plates din suka zube a k'asa na fashewa suka fashe, ko takan ta Sabeer bai bi ya haye stairs still kuma hawayen na zuba don ya kasa rik'e su zuciyar sai bugawa take da k'arfi kanshi yana mishi ciwo sosai. Duk wannan abin akan idon Alhj Ahmad aikuwa ya dad'a rud'ewa sosai ya bi bayan Sabeer da sauri, haka ma Mumy wadda take kitchen k'arar fad'uwar abu ya fito da ita da sauri hango tilon d'an nata tayi yayi upstairs kamar a fusace ga surukin ta yabi bayan shi ya sanya itama ta bisu cikin tashin hankali. Babu wanda ya kula 'yar aikin haka ta tashi cikin sanyin jiki da zafin fad'uwa ta fara tattara wajen da ya 6aci dakyar take aikin saboda ba karamin buguwa tayi ba da alama wani abin ne ya faru da d'an lelen don ba haka Sabeer yake musu ba sai dai idan ranshi ya 6ace shi da Jiddah su kad'ai ne masu kirki a gidan. Kai tsaye bedroom d'in shi ya wuce yana shiga ya rasa me yake mishi dad'i gaba d'aya zuciyar shi da idanun shi Suhaima suke son gani muryar ta suke son ji. "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka ba " Muryar Suhaima yaji cikin kunnen shi tamkar a lokacin take furta mishi hakan, runtse idon shi yayi da k'arfi yace "Nooo Suhaima sai kin so ni!" Ya k'arasa fad'in haka yana zubar da kayan saman dressing mirror a k'asa nan perfumes wasu suka faffashe, nan ya dawo cilli da pillows d'in kan bed da na sofa cikin lokaci kad'an ya hargitsa d'akin cilli yake da duk abin da ya samu saboda ya rasa yanda zai yi kuwwar muryar Suhaima ce take mishi amo a kunnen shi. Yana kok'arin zubewa a k'asa ne yaji an rik'o shi kallon wanda ya rik'e shi yake sai yaga Alhj Ahmad ne ga Mumyn shi kuma a gefe tana kuka hankalin ta a tashe sosai me yake damun Sabeer d'in ta, kwace jikin shi yayi ya samu k'asa ya zauna cikin tashin hankali Alhj Ahmad yace "Sabeer me......? " D'aga mishi hannu Sabeer yayi tare da cewa "ku fita ku ban waje " "What! Kana nufin zamu tafi mu bar ka a wannan halin? " Idanun shi sun ja haka fuskar shi ma ga hawaye suna zuba ya d'ago kanshi ya kalle shi, sai da gaban Alhj Ahmad da na Mumy ya fad'i ganin yanda Sabeer ya koma tamkar ba Sabeer d'in da suka sa ni ba. Cikin magana da k'arfi yace "Leave me alone please don't disturbing me". Yana gama fad'in haka ya sanya hannun shi dukka biyun cikin gashin kanshi yana hargitsawa su kuma kallon shi suke tamkar wasu sokaye sun rasa abin yi dakyar Alhj Ahmad ya zauna yana goge hawaye don ya d'auka Sabeer ya haukace haka Mumy ma kuka take sosai, sun dad'e a haka kafin ya tashi ya shige bathroom ya sakarwa kanshi shower, ya dad'e sosai a ciki kafin ya fito d'aure da towel. Ko'ina an

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});