Chapter 56
Chapter 56
sani kuwa. Tana gama fad'in haka haka ta wuce side d'in ta tana shiga bedroom saboda tsabar takaici ta rushe da kuka kamar wata k'aramar yarinya, Allah yayi ta mace mai tsananin kishin sosai ji take har numfashin ta yana kokarin d'aukewa tsabar tashin hankali. Anutse Daddy ya shigo bedroom d'in jin kukanta ba k'aramin d'aga mishi da hankali yayi ba don shi yaushe rabon yaga kukan matar shi kamar haka har ya mance. Cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take ya zauna kafin ya dafa kafad'ar ta yace "Yake matata kukan me kike haka? " D'ago kanta tayi ta kalle shi idanunta suna zubar da hawaye ta fad'a jikin shi ta k'ank'ame shi tare da cewa "Ina tsananin son ka Hussein ina kishin ka bana son wata mace ta ra6ar min kai but why da zaka yi min haka kaje wajen wata kai da Son har kuci abincin ta? " Murmishi Daddy yayi kafin yace "Haba Faridah kinsan bazan iya kallon wata d'iya mace da sunan ina sonta ba, banyi hakan tun k'uruciya ta ba sai yanzu da na girma kinsan ke kadaice cikin zuciyata daga ke babu dad'i, duk wannan maganar tsokanar ki Sabeer keyi" Kallon idanun shi take don son tabbatar da gaskiyar maganar shi, gid'a mata kai yayi tare da lumshe eye's nashi alamun haka maganar take. "Toh ina kuka je da Son har kukayi dare? ". Fuskar shi d'auke da murmishi yace "Muna part d'in Hajjah ana hira " Rungume Daddy tayi tana sauke ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji ta a nutse nan kuma suka 6ige da nunawa juna kauna. Washe gari da yammacin ranar Jiddah da Yusrah suka d'aga zuwa dubai don siyayyar kayan lefe, sosai Daddy da Sabeer suka saki kud'i don a had'o kaya masu kyau da tsada. **** **** **** Satin su Jiddah 2 suka dawo Nigeria da tarin had'add'un kayan lefen da suka had'a, kaya sunyi ta ko'ina sosai kayan Daddy da Sabeer suka yaba za6en su ko Mumy sai da ta jinjina irin dukiyar da aka narka anan ko ita kayan sun birgeta duk hassadar mutum yaga kayan sai sun birgeshi, har da tukwici Daddy yayiwa Jiddah da Yusrah don sun mishi yanda yake so. Har zuwa lokacin Sabeer tsakanin shi da Mumy gaisuwa sam yak'i sake mata kamar da, don ba k'aramin 6ata mishi rai tayi ba akan lefen da ta had'a wai za'a kaiwa Babyn shi idan ya tuna hakan har ranshi 6aci yake. Duk wannan kayan da aka had'o sai da Jiddah ta kar6i kud'i na musamman hannun Sabeer ta siyawa Suhaima kayan da zata yi amfani dasu wajen biki komai sai da ta had'o yanda ya kamata. Bayan kwana 2 duk 'yan uwa sun gama ganin lefen sai zuzutashi suke saboda had'uwar shi but idan suka tuna 'yar kauye za'a kaiwa wannan duk sai ransu ya 6aci su fara jan tsaki da k'ananun maganganu, babu mai goyon bayan Sabeer akan wannan bikin sai Daddy don ko Dr Ahmad d'an fillo kadaran kadahan don farincikin Sabeer ya hak'ura. Shiyasa Sabeer da Daddy ne kawai suke kid'an su da rawar su, duk wadannan tarin kayan da aka had'a sai da Daddy ya k'ara da wata dank'areriyar sark'ar gold mai matuk'ar kyau da tsada ba kad'an ba da kuma key na mota, don Daddy tuni ya zubar da makaman yak'inshi na k'in talaka yanzu sosai yake tsayawa sauraren talakawa masu neman taimako yana taimaka musu kuma hakan ba k'aramin jin dad'i yake ba da kuwa daga iya fidda zakka shikenan. Wannan abun da Daddy yayi wa Suhaima ba k'aramin bak'anta ran Mumy yayi ba don ita aganin ta taya zai tsaya siyawa 'yar k'auye wannan gold d'in mai tsada bayan wad'anda aka zuba mata a lefe gashi har da wani kyautar mota ko'ina 'yar k'auye da tukin mota me zatayi da ita, banzatar dasu zata yi tunda batasan darajar su ba, Daddy sai da ya toshe kunnen shi don kuwa Mumy da Hajjah sai mitar abin suke yi, shi kuwa ganin farincikin tilon d'an shi yafi mishi komai. Ko ranar da za'a kai lefe motoci 3 Daddy yace za'a yi na mutane saboda bayason a had'a su da wahala kuma bayason ayi hatsaniya don sosai sai da ya gargad'i wad'anda zasu kai wanda suka kasance daga kanwar su Daddy sai k'annen matanshi da yaran su mata kad'an daga ciki, sai kuma motar Suhaima wanda aka zuba kayan lefen ta a ciki nan suka d'auki hanyar k'auyen su Suhaima. Sai wurin 3 na yamma suka k'arasa kowanne ya fito daga mota sai faman yatsina fuska da ta6e baki suke suna yiwa mutane kallon d'ai d'ai, koda suka shiga gidan su Suhaima sunsha mamakin ganin yanda gidan yake don kuwa Yah Aliyu ya kashe kud'i sosai wajen gyara gidan har da sabon fenti akayi, shi yasa ko'ina yayi kyau yayi fes ga an tsabtace gidan sai k'amshin turaren wuta yake. Anan tsakar gidan suka zazzauna saman tabarma, su Aunty Aliya da Babaa Lantana da wasu daga cikin 'yan uwan su Suhaima sun d'an zazzo kar6ar lefen, wasu kuma don ganin kwakwaf suka zo don sunji ance d'an mai kud'i Suhaima zata aura suna son tabbatar wa aikuwa da ganin irin motocin da suka zo acikin ta sun tabbatar da gaskiyar zancen. Babu wanda yayi gigin shiga toilet sai alwala da suka yi suna tsoron kada su shiga su ga abin da zai sanya su amai, dai dai da ruwan alwala da bottle na faro suka dunga yi saboda tsantsanin ruwan suke. Jiddah ranta ya 6aci sosai da wannan wulak'ancin da 'yan uwanta suka yi don an zuba musu ruwa a botoci suka k'i amfani dashi suka d'auko bottles na faro, kasa magana tayi don tsabar takaici, yayin da mutane suka saki baki da hanci suna kallon wannan sabon salon nasu, awurin sallahr ne kawai basu da yanda zasu yi suka yi akan tabarmar da aka shimfid'a musu bayan sun idar aka sake gaisawa sannan aka fara fito musu da abinci zuwa drink's da ruwa na bottles. Sunyi mamakin na ganin irin abincin da suka gabatar musu dashi don basu yi zaton samun hakan ba, basu san wannan duk aikin Jiddah ba ne don kawa batason a 'yanuwanta su wulak'anta mata Suhaima. Sun ci abincin bayan sun kammala aka gabatar da kayan lefen da car key sai kuma kud'in da ake d'ora wa saman kaya har 1 million, sakin baki, hanci sukayi 'yan kauye don ganin irin wannan abun da basu ta6a tsammanin zasu ganshi da ido ba nan kowa ya fara kokwanto cikin zuciyar shi anya ba siyar da Suhaima su Aliyu suka yi ba yo banda hakan ina za'a bayar da irin wannan kayan lefen haka har da mukullin mota da 1 million akai. "Kada ku damu wannan ba wani babban abu bane a wurin mu don mun bayar da wadannan 'yan kayan don haka ku dai na mamaki, kodan nasan dole kuyi mamakin don ido bai ta6a ganin irin kayan ba " Cewar Aunty Fadilah kanwar su Daddy tana wani yatsina fuska banda kallon raini da take bin su dashi, don 'yar gaban goshin Dr Faridah ce tana taya matat wan nata bak'in cikin wannan abu. "Haba Aunty Fadilah don Allah ki daina irin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104