Chapter 20
Chapter 20
nace ke kika fad'a min na fad'a mishi aure kike so kina jin kunyar sanar dashi shi yasa kika aiko ni " Jiddah ta k'arasa magana tana dariyar mugunta, kwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa "Wayyo Allah nah Jiddah ki rufa min asiri, waiii idan Yaya yaji hakan ina tunanin 6a66ala ni zai yi " "6a66alawar lafiya, ai ba wani mugun abu kika yi " "Besty albishirin? " "Goro fari tas mai ya faru k'awata? " "Aunty Aliyah tana da ciki taawon 3 month's " Wani uban tsallen murna Jiddah ta doka tare da rungume Suhaima tana cewa "Da gaske kike Suhaima don Allah? " Cikin tabbatar wa Suhaima tace "Da gaske ne wlh Jiddah, sai dai yana bata wahala baki ga yanda ta koma ba duk ta rame ko abincin kirki bata iya ci " Suhaima ta k'arasa maganar cikin yanayim damuwa, nan take Jiddah ita ma fuskarta ta koma kalar damuwa, hannun Suhaima ta rik'o suka nufi d'akin Aunty Aliyah tana cewa "Kada ki damu Suhaima Aunty Aliyah zata samu lafiya, kinsan wani cikin yana bawa mace wahala sosai kafin ya girma, da zarar ya girma insha Allah zata samu sauk'i addu'a zamu cigaba da yi mata " Gid'a kai Suhaima tayi kawai a lokacin suka k'araso kofar d'akin Aunty Aliyah sallama suka yi mata, dakyar ta iya amsa musu sallamr k'asa k'asa cikin irin sanyin muryar mara lafiyar nan wanda yake jin jiki sosai, d'aga labulen d'akin suka yi tare da shiga ciki tana kwance a falo saman sallaya da hijab a jikin ta alamar yanzu ta idar da sallahr azahar. Zama suka yi kusa da ita sosai Jiddah hankalin ta ya tashi ganin yanda Aunty Aliyah ta koma wata iri duk ta rame sosai ta fita a hayyacin ta tamkar ba ita ba. "Sannu Aunty Aliyah Allah ya baki lafiya " Cewar Jiddah kenan, murmishin yak'e Aunty Aliyah tayi tare da cewa "Yawwa Jiddah, Amin " Dakyar take maganar tana jan numfashi irin wanda yake idan mutum yana jin ciwo sosai idan yayi magana yake yi. "An kaita hospital kuwa Suhaima? " Jiddah ta tambayi Suhaima tana kallon ta. "Eh Yaya ya kaita amman magani suka bata " "Wanne hospital ne wannan da ko drip baza su sanya mata, jiki babu kwari ga ba cin abinci, yanzu da sun sanya mata drip zata ji k'arfin jikin ta " Tana gama fad'in haka ta ciro wayar ta dialing d'in digit na Yaya Aliyu tayi bayan sun gaisa ta fad'a mishi tazo tana son ganin shi, babu dad'e wa sai ga Yaya Aliyu ya shigo bayan sun dad'a gaisawa ne tace "Yaya Aliyu don Allah ina son kayi min alfarma mu kai Aunty Aliyah hospital d'in da muke zuwa, ba don na raina kulawar da kake bata ina son zan kaita inda zasu duba ta sosai " Girgiza kai Yaya Aliyu yayi tare da cewa "Baza'a yi haka ba Jiddah wahalar zata yi yawa, ki fad'a min sunan hospital d'in gobe zan kaita da kaina a duba ta " "Don Allah Yaya ka daure mu je na roke ka " Nan Jiddah tayi ta rok'an shi dakyar daga k'arshe ya amince don har Jiddah ta fitar da ran zai barsu, nan da nan suka shirya tafiya hospital a motar da Jiddah tazo, Yaya Aliyu da driver a gaba Jiddah, Suhaima da Aunty Aliyah a baya su bayan sun yiwa Babaa Lantana sallama, sai addu'ar fatan alkhairi Babaa Lantana take yiwa Jiddah. Wani had'add'en private hospital wanda Jiddah da families d'in ta suke zuwa nan ta sanya driver ya kaisu, babu 6ata lokaci aka kar6i Aunty Aliyah saboda sunsan wace Jiddah, nan aka shigar da Aunty Aliyah special room ita d'aya sai doctor da kuma nurse guda biyu. Sun d'auki tsawon lokacin suna checking nata kafin daga k'arshe su sanya mata drip tare da yi mata injection na bacci kafin su fito a room bacci mai nauyi ya d'auke ta. Bayan sun fito ne likita ya buk'aci ganin su cikin office d'in sa bayan sun shiga sun zauna ne, sai da yayi rubutu cikin file sannan ya fara cewa "Ciki ne da ita na tsayin 3 months so kunsan kowacce mace da irin halittar ta na laulayi ciki kafin yayi kwari, shine yake bata wahala baya ga wannan babu wani abu babba sai malaria, zamu yi iya kok'arin mu na ganin koda cikin kashi biyar ne ta samu saukin kashi uku sauran kuwa sai a hankali don haka mun bata gado zamu rik'e ta har zuwa gobe insh Allah " "Okaya doctor thank U very much, yanzu zamu iya ganin ta? "Why not sai dai ban da hayaniya please and kuma ga maganin da za'a yi amfani dashi na rubuta ana buk'atar shi da wuri don tana tashi zata sha " "Okay doctor ba damuwa" Nan doctor ya bawa Aliyu suka yi musabiha tare da cewa "Allah ya bata lafiya ya kuma raba su lafiya congrats Yalla6ai " "Amin nagode likita " Sam doctor yayi tuanin cousins d'in Jiddah ne ganin su suma kyawawa dasu tamkar family d'in su Jiddah shi yasa bai kawo komai a ranshi ba, sai dai yanayin su da ya nuna basu da kud'i kamar su Jiddah. Bayan sun shiga room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah ne suka zauna shiru kowa da nashi tunani ta 6angaren Aliyu yana tunanin da kunya ya iya kallon idon Jiddah yace bazai bar Suhaima ta tafi bikin ta ba ganin irin d'umbin hallacin da tayi musu bai kamata ya hana Suhaima zuwa ba, gashi kuma Aliyah na buk'atar kulawa sosai gashi idan suka koma gida gobe Suhaima ce k'arfin ayyukan gidan idan ya barta ta tafi ya zasu yi?... Kuyi hak'uri da wannan fan's sai gobe kuma insha Allah. Aishat A Muh'd 🏌🏻♀ [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz This page is for U my Ramlat ar manga (Real mai dambu 🥗) thanks for luv nd everything Allah ya bar zumunci ya raya zuri'a, ina matukar alfahari dake wannan shafin naki ne kyauta 👄 PAGE 30-31 Tashi Jiddah tayi tsaye tare da d'aukan bag d'in ta gida take son tafiya saboda yau ne ranar kamu sai faman kiran ta ake a waya ana tambayar ta inda take, kallon ta Aliyu da Suhaima suka yi, ita ma kallon su tayi tare da cewa "Yaya Aliyu zan tafi gida ana nema na, zan dawo gobe da safe na mayar da ku gida Allah ya bawa Aunty Aliyah lafiya " Kallon ta Aliyu yake gaba d'aya ya rasa ma mai zai ce mata dakyar ya iya bud'e bakin shi yace "Amin Jiddah nagode sosai da karamcin ki gare mu, nasan kina son tafiya da Suhaima koh? " D'an murmishi tayi tare da cewa "Haba Yaya Aliyu taya zan tafi da ita bayan itace ke kula da Aunty babu komai wlh nasan lalura ce taja hakan " Girgiza Aliyu yayi kafin yace "Idan lokaci bai k'ure ba ki d'auki Suhaima kuje gida ta d'ebi kayan da zata yi amfani dasu, sai ku taho da Babaa Lantana ta zauna da mu anan zuwa gobe " Duk da Jiddah taji dad'in abin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104