Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da ita ba sosai kwatsam ana haka sai Fatima ta samu ciki tun daga lokacin ta rasa gane kan Umaru don gaba d'aya ya canja mata, duk wata kulawa da yake bata ya bari. Saboda sam shi baya son yara gaba d'aya wahala ne rainon su kawai, yayi rarrashin da ban bakin don kawai Fatima ta yarda a zubar, amman sam tak'i yarda saboda tana matuk'ar kaunar yara sosai, ganin tak'i yarda da buk'atar shi na zubar da cikin yasa shi fara gallaza mata tare da yi mata wulak'anci da rashin mutunci kala kala. Amman duk Fatima ta shanye wannan wahalar da yake bata har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta samu d'a namiji inda ya ci sunan shi Aliyu, saboda rashin babu ko suna ba'a yi ba balle yiwa yaro yanka kamar yanda ake yi a al'adance, saboda iyayen Fatima basu da k'arfi su ma kuma waje ba d'aya ba don suna da d'an nisa a tsakanin su, tun kafin ta haihu da Umaru ya sanya k'afa ya bar garin bai dawo ba har sai da tayi wajen wata biyu da haihuwa sannan ya dawo duk da kuwa yaji labarin haihuwar. Nan ya bi ya tsani Aliyu ko kad'an baya kaunar yaron, ga zafin talauci da ya kunno mishi kai saboda motar da yake aiki da ita mai shi ya kwace abar shi, sai buga buga da yake faman yi. Aliyu na da watanni 10 cif, Fatima ta sake samun wani cikin nan Umaru bak'in ciki ya isheshi, a lokacin babu irin cin mutuncin da bai yiwa Fatima daga k'arshe sai da yasan yanda yayi ya zuba mata maganin zubar da ciki a lemo, ya bata tasha babu dad'e wa ciki ya zube nan farinciki fal cikin zuciyar shi, yayin da Fatima bata zarge shi ba ta d'auka kawai 6ari ne tayi nan ta cigaba da rainon Aliyu wanda uban bai ta6a d'aukan shi ba, ko kallon mutunci baya yi mishi saboda tsabar tsanar da yayi mishi kamar ba shine uban shi ba. Bayan zubewar ciki ne ya dawo da d'an bata kulawa kafin daga k'arshe kuma wani cikin ya sake bayyana a jikin Fatima, wannan karon ma zubar mata da cikin yayi wanda sai a lokacin Fatima ta ankara da hakan, nan tayi kukan bak'in ciki da takaici na abin da mijin nata yake yi mata na mugunta. Sai da Umaru ya zubar wa mata da ciki sau uku bayan haihuwar Aliyu, ana hud'un ne kuma bai samu nasarar zubar wa ba har aka haifo Suhaima, sai da Suhaima tayi shekara 5 sannan ta sake samun wani cikin wanda har Fatima ta fitar da ran sake haihuwa ganin shekarun Suhaima sun d'an ja, kwatsam ta samu wannan cikin wanda ya sanya Umaru dana sanin auren Fatima a rayuwar shi ga talaucin da yake fama dashi mai tsanani. Har zuwa yanzu babu abin da ya canja daga tsanar da yake yiwa Aliyu, Suhaima da kuma cikin da yake jikin Fatima, daman abinci ba basu yake ba komai na abin da ya rataya a wuyan shi na hakk'in matar shi da yaran shi baya yi, kanshi kad'ai ya sani idan ya samu kud'i zai ci mai dad'i a cikin shi, wani lokacin agaban su zai ci abin shi sai dai su yi ta had'iyar yawu, amman ko kad'an ne bazai ba su ba, sai dai da dare ya bi ya tak'ura wa Fatima da buk'atar shi, bayan kuma ko abincin kirki baya bata wani lokacin ma tun karyawar safe har zuwa daren ba zata samu cin wani abincin kirkin ba, haka zai bi ya gala6aitar da ita shi yasa kullum sake rame wa take ga jiki babu k'arfi. Ban da uban dukan da su Aliyu da Suhaima suke sha a hannun shi, don kusan akan su yake huce haushin shi, har zuwa lokacin da Aliyu ya fara fita d'an aikin k'arfi yana d'an samun wani abin wani lokaci ya siyo musu abin da zasu d'an sa a cikin su, ko kuma idan makobcin su idan anyi girki da d'an yawa suna taimaka musu saboda sun san halin da suke ciki, bama iya su kad'ai ba kusan k'auyen gaba d'aya ma sun gane halin da suke ciki. *** *** *** *CIGABAN LABARI* Haka su Fatima suka cigaba da rayuwar wahala a hannun mugun mijin ta uban yaran ta, da ita da yaran nata don gaba d'aya had'a wa yake ya ci musu mutunci son ran shi. Kamar yau da sassafe suna zaune cikin d'aki, a gaban su garwashin wuta ne a cikin kasko suna jin d'umi, duk sun yi jigum jigum Fatima da Aliyu suna tunanin hanyar da zasu bi don su samu abin da za'a karya dashi, yayin da Suhaima kuma ta fara hawaye saboda yunwar da take nuk'urk'usar ta. Bankad'o labulen d'akin aka yi aka shigo, kamar kullum ba wanda ya kalle shi, cikin sauri ya wuce uwar d'aki ko kallon inda suke bai yi ba, babu jimawa ya fito hannun shi rik'e da jakar kayan shi kaf. Kallon matar ta shi yayi tare da cewa "to ni Fatima tafiya zan yi, kuma bansan ranar dawowa ta ba, watak'il na dawo ko kuma na tafi kenan, tun da kin k'i yin abin da nake so, zan tafi zan yi nesa da rayuwar ku, zan bar ki ke da yaran ki." Tun da ya fara magana Fatima take kallon shi tana kuka, yana k'arasa maganar shi ya sanya kai zai fice zuwa waje babu alamar damuwa a fuskar shi, da sauri Fatima ta rik'o rigar shi cikin kuka ta fara cewa "yanzu tafiya zaka yi ka barmu? " Babu wata damuwa yace "tabbas tafiya zan yi, bazan zauna bak'in cikin 'ya'yan ki ya kashe ni ba, tun kafin lokaci na yayi " Cikin tsananin kuka Fatima tace "Don Allah kayi hak'uri ka dawo mu zauna, kada ka mance ina da auren ka akai na, sannan kuma ga yaran k........." Kafin ta k'arasa fad'in maganar ta, Umaru ya sanya hannu ya ture ta da k'arfi, ta fad'i da6ar a k'asa, tuni marar ta tayi wani mugun d'aure wa, da sauri Aliyu ya nufi wajen Fatima shi da Suhaima suna mata sannu, cikin hassala da rashin mutunci yace "kada ki k'ara danganta ne da wad'annan shegun yaran, kuma zan tafi babu uban da ya isa ya hana ni tafiya " Yana gama fad'in haka ya kad'a kanshi ya fita, cikin zuciyar shi wasai babu damuwa ko kad'an. Dakyar Fatima ta iya gyara zaman ta, saboda mugun ciwon da marar ta yake, sakamakon ture ta da mijin nata yayi ta fad'i, wani irin zugi zuciyar ta take lokaci d'aya ta nemi hawaye ta rasa, ta kafe idon ta waje d'aya tamkar wata mara rai don ko motsin kirki bata yi. Tun motsawar da tayi bayan ta fad'i, a hankali wani abu mai d'umi ya fara zubowa ta jikin ta, sai a lokacin ta motsa idon ta, zuwa kallon jikin nata, sai ta ga jini ne yake zuba sosai, alamar cikin nata yana cikin hatsari, koma yana daf da fita, sai a lokacin taji wani kuka ya zo mata mai k'arfi. Cikin kid'ima Aliyu yace "Umma jini a jikin ki, na kirawo miki Babaa lantana? " D'aga kai kawai ta iya

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});