Chapter 21
Chapter 21
da Aliyu yace mata amman sai da ta sake cewa "Ka barshi Yaya yanzu babu lokaci sauri nake sai kirana ake lokacin kamu yayi amman insha Allah gobe zan dawo sai mu tafi tare " "Shikenan Jiddah Allah ya biya ki, Allah ya sanya alkhairi " "Amin Yaya, amman godiyar ta isa haka " Murmishi suka yiwa junan su kafin Suhaima da Aliyu su tashi rakiyar Jiddah har zuwa compound d'in hospital d'in suka sake yin sallama kafin ta shiga mota driver yaja motar su tafi, Aliyu da Suhaima suka dawo cikin room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah har yanzu dai bacci take bata farka ba zama suka yi jigum jigum, sai jefi jefi suke d'an ta6a hira sannan nurses suna shigowa duba Aliyah, da dare sai da Jiddah ta aiko driven da suka zo tare da takeaway na abinci sai kayan tea acikin leda bak'a 'yar babba, sosai Aliyu da Suhaima suka ji dad'in haka daman a lokacin yake tunanin fita neman masu abin da zasu ci sai gashi, nan Aliyu ya sake jinjina k'aunar da Jiddah take yiwa Suhaima dasu kansu basu da abin da zasu biyata abin da tayi musu sai dai addu'ar fatan alkhairi. Washe gari da safe Aliyah ta tashi jikin ta da sauk'i sosai ta samu k'arfin jikin ta, tana cin abinci sai dai wani ya zauna wani ya fito amman sosai sun ga sauk'i fiye da lokacin da suka zo jiya tun da tana tashi da kanta ba tare da an taimaka mata ba. Ganin haka ya sanya likita basu sallama tare da rubuta mata maganin da zata nayin amfani dashi, sannan ya fad'a musu idan taji wani canjin yanayi a jikinta ta dawo hospital d'in tun da file Jiddah ta sanya aka bud'e mata. K'arfe 11:25 na safe sai ga Jiddah ta shigo room d'in sosai taji dad'in ganin Aunty Aliyah jikin da sauk'i, bayan an gaisa kuma suka fito daga cikin asibitin zuwa inda motar da Jiddah tazo da ita, yau babu driver ita d'aya tazo da kanta tayi driving, bayan sun shiga motar ne suka d'auki hanyar zuwa k'auyen nasu. Bayan sun isa gida ne a gurguje Suhaima ta gyara gidan tsaf tana kok'arin d'ora girki Babaa Lantana ta shigo gidan ta kar6in aikin tare da ce mata ta shirya su tafi, aikuwa nan ta shiga wanka bayan ta fito ne ta shirya jikin ta a lokacin Jiddah har ta gama had'a mata kaya a cikin bag d'in da ta bata suka fito zuwa tsakar gidan. Inda Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suke zaune zama suka yi suma a k'asan tabarmar da suke kai, nasiha sosai mai ratsa jiki Yaya Aliyu yayi wa Jiddah na irin rayuwar da zata shiga nan da kwana d'aya, haka Babaa Lantana ma tayi mata nasiha sosai Aunty Aliyah ce babu k'arfin yin magana sai murmishi da take mata cikin zuciyar ta tana mata addu'a. Daga k'arshe Jiddah ta fito daga gidan da bag d'in Suhaima a hannun ta, saboda taga alamar kamar akwai abin da suke son fad'a wa Suhaima, aikuwa tana fita Yaya Aliyu da Babaa Lantana suka yi mata nasiha na ta tsare mutunci kanta ban da kula samari da rawar kai komai ta gani ta kawar da kai tana yin alkunya kodan saboda Jiddah sannan Yaya Aliyu daga k'arshe ya gargad'i ta da babbar murya kada tayi shiga matsatstsiya na sutura, ta suturce jikin ta matsayin ta na 'ya mace. Bayan sun gama mata nasihar ne Yaya Aliyu ya bawa Suhaima kud'i masu dama sannan yace "Wannan kud'in ki nemi abin da zaki siyawa Jiddah gift's dashi ki rage wasu kuma don ki rik'e a hannun ki " Aunty Aliyah cikin muryar marasa lafiya tayi wa Suhaima magana da ta shiga d'akin ta ta d'auko mata wani box cikin drower d'in gadon ta, nan Suhaima taje ta d'auko ta mik'a mata kar6a tayi ta bud'e sai ga wata sark'a, d'an kunne, zobe da warwaro guda uku sai sark'ar k'afa masu kyau sai kyalli suke da d'aukan ido farare ne. "Ki bawa Jiddah kice mata ba yawa tayi hak'uri " Cewar Aunty Aliyah kenan cikin sanyin murya, rik'e hannun ta Suhaima tayi tana murmishi tace "Toh Aunty zan bata insha Allah " Daga haka Suhaima ta tashi haka ma Yaya Aliyu suka fito zuwa nan kofar gida inda Jiddah take zaune cikin mota, shiga seat d'in gaba Suhaima tayi tare da rufe k'ofa, nan Jiddah tayi wa motar key suka fara tafiya sannan Yaya Aliyu ya buga machine d'in shi yana binsu a baya don ganin gidan su Jiddah saboda zuwa d'auko Suhaima. "Malama da haka zamu tafi kina min hawaye salon ace na sato ki " Fad'in Jiddah cikin sigar tsokana, "Kewar gida na fara yi Jiddah tun da nake ban ta6a zuwa wani wajen kwana ba sai yau" Cewar Suhaima tana kwantar da kanta a jikin kujera. "Lallai da drama duk lokacin da kika yi aure za'a kai ki gidan miji kenan, tun da shi fatan zama na har abada ake " D'an zaro ido Suhaima tayi tare da cewa "Tabbb ni fah auren ma baya gaba na Jiddah, har yanzu ban ta6a tsayawa da wani ba da sunan zance ba " "Lallai yarinya da sauran ki kina tunanin Yaya Aliyu zasu zuba miki ido babu aure? " D'an marairaice fuska Suhaima tayi tana cewa "Ni fah da za'a bi tason ra'ayi na karatu zan cigaba da yi wlh tun da gaba d'aya ni yarinya ce nawa na ke " Hararar wasa Jiddah tayi wa Suhaima kafin tace "Ai yanzu tsab za'a yi miki aure ki zauna akwai wad'anda basu kai ki ba ake musu su zauna lafiya ma " D'an shiru suka yi na 'yan minute's kafin Jiddah tace "Ni kuwa Suhaima wane irin Namiji kike son aura i mean halayyar shi, yanayin shi and everything da kike son mijin ki ya kasance? " Shiru Suhaima tayi na tunani kafin ta sauke ajiyar numfashi tace "Ni a tsarin rayuwa ta bana son auren miji mai kudi da yawa nafi son auren talaka dai dai ni wanda bazai wulak'anta ni ba da 'yan uwana ba ko dangin shi su na wulakanta mu ba, kuma bana son auren miji mai irin kyan nan da yawa ina da kishi wallahi bazan iya jure ganin 'yammata suna kai mishi farmaki ba, sannan bana son mai saurin fushi,ina son kuma mijina ya kasance mai ilimi both side addini da boko kuma...... " "Kaiii Suhaima idan kuma Allah ya baki handsome mai kyau da kudi fah, kamar yanda kike da kyau ke ma? " "Hmmm bana fatan haka Jiddah na fison talaka d'an uwana, ni koda misali wani mai kud'in zaice yana sona bazan amince mishi ba wulak'anci zan tayi mishi har ya hak'ura ya bar ni, nasan ma bazai jure wulakanci ba zai rabu da ni " Dariya sosai Jiddah tayi kafin tace "Koda wanda kika watsa mishi ruwa ne idan ya dawo yace yana son ki fah ya zaki yi? " "Tabbb ai korar shi zanyi balle nasan bazan sake ganin shi ba har abada ma" Cikin zolaya Jiddah tace "Kika sani ko shine mijin naki Allah ya kawo miki " Dukan wasa Suhaima ta kaiwa Jiddah da sauri ta goce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104