Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 63

Chapter 63

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tak'i cikata sai dakyar aka kwaci Babaa Lantana don ba k'aramin riko Suhaima tayi mata ba, Jiddah ce ta rik'e ta tana rarrashin ta yayin da su kuma suka tafi Babaa Lantana har da goge hawayen ta na kewar Suhaima. Gidan sai yayi tsit daga Jiddah sai friends na Suhaima gyaran gidan suka yi suna gama gyarawa kowacce ta fara shirin tafiya dinner na family d'in D'an fillo, Jiddah ta sanya Suhaima tayi wanka ta bata wata white gown ta material har k'asa take ja sosai sai adon flower's silver ajiki, dakyar ta tsayar da hawayen idon ta aka yi mata makeup sannan aka nad'amata net white akanta sai hill shoes and purse white sai d'igon silver ajikin su, sunyi mata kyau sosai kayan different perfumes Jiddah ta fesa mata kafin ta rik'o hannun ta suka fito zuwa compound na gidan. Suhaima na shiga cikin motar tun kafin Jiddah ta rufe murfin motar Sabeer ya rungume ta ajikin shi yana sakin wata ajiyar zuciya gaba d'aya yabi ya wani matse ta cikin jikin shi k'am tamkar za'a kwace mishi ita. "Kaiii Yah Sabeer agaba na ji yanda ka matse ta" Jiddah ta fad'a tana rik'e da murfin motar, wata harara ya watsa mata don bazai iya magana ba dariya ta kwashe da ita kan ta rufe motar. Kok'arin zame jikin ta take amman yak'i sakin ta sai faman shinshina wuyan ta yake yana wani sauke ajiyar zuciya da numfashi cikin murya k'asan mak'oshi yace "Baby ki barni mana kinsan dai yanzu kin zama tawa ta har abada hakan da nake miki babu haramci aciki tunda an d'aura mana aure, Baby kinsan tun yaushe nake mafarkin zuwan wannan ranar kuwa? " Ita dai Suhaima a tsorace take dashi ganin yanda Sabeer d'in ta ya rikid'a ya koma wani daban tamakar bashi ba jikin ta har ya fara 6ari na tsoro, da haka suka k'arasa wajen da za'a yi dinner, yana rungume da kusan rabin jikin ta suka shiga wajen. 'Yan uwan Sabeer gaba d'aya yawancin sun zo haka ma Hajja Hauwaa, Dr Ahmad d'an fillo, Daddy da k'annen shi Dr Faridah da sauran matan k'annen Daddy, haka ma yaran duk sun zo tun daga manya har k'ananu waje dai ya cika masha Allah gashi sun sha gayun su na kece raine, ga friends na Dr Faridah wato Mumy duk kusan sun zo manyan hamshak'an en boko da en siyasa da kuma likitoci gaskiya anyiwa Dr Faridah karar zuwa wajen bikin tilon d'anta. Amman fuskar ta sam baza ka iya karantar yanayin da take ciki ba farinciki ko akasin haka, kusan nace gaba d'ayan su Daddy ne kawai yake faman zuba murmishi cikin zuciyar shi yana yaba za6en d'an nashi don sai yanzu yasan Suhaima da ido, bayan ango da amarya sun yi rawa an musu lik'i ne sun yanka wedding cake ne suka bi ko'ina suna gaida en uwa da abokanan arzik'i da suka zo an ci ansha sannan aka watse da tarin gift's d'in da Suhaima ta samu a wajen friends na Daddy da k'annen sai na Dr Ahmad d'an fillo tasha kyautittaka sosai a wajen su, zuwa lokacin gaba d'aya jikin Suhaima ya gama yin sanyi ganin irin kallon da mahaifiyar Sabeer take bin ta dashi da sauran en uwan shi ita duk ma kallon da Mumy take binta dashi yafi hargitsa mata kai ko gaisuwar ta bata amsa ba sai tashi tayi da sauri tabar wajen tana amsa kiran karya a wayanta don kuwa ba kiranta aka yi ba. Sai karfe 11 da wajen rabi aka tashi kowa ya kama gaban shi, Suhaima ce take rik'e da hannun Jiddah k'am sai fitar da hawaye take tana cewa "Ni dai tare daku zan tafi gaskiya " Dariyar da take neman kubce wa Jiddah ta had'iye ta kafin tace "Haba Suhaima kiyi hak'uri ku tafi kin ga yanzu dare yayi gashi na gaji sosai amman nayi miki alkawarin gobe zan zo na kawo miki friends naki kuyi sallama dasu " Kasa magana tayi sai hawaye gaba d'aya hankalin ta a matuk'ar tashe, sosai Jiddah ta bata tausayi cikin sanyin murya da kwantar da hankali take rarrashin Suhaima tana rik'e da hannun ta har ta sanya ta cikin mota ji take kamar itama ta taya Suhaimar kukan sai dai ta daure. Sabeer yana shiga motar ya umarci driver ya dasu tafi don ya matsu ya ganshi su kadai da Babyn shi awaje daban, rarrashin ta shima Sabeer d'in yake har suka k'arasa gida cak ya d'aga ta sama ya d'auke ta suka nufi cikin gidan bai dire ta a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom nata. Hannun shi ya sanya ya fara warware mata net d'in kanta sannan ya dawo kan sark'a, d'an kunne warwaro zuwa takalmin k'afar ta, bata ankara ba taji yaja zipe d'in rigar tun daga sama har k'asa wani 'yar k'ara Suhaima ta saki tare da yin baya da sauri ta jingina da bango idanun ta taf hawaye take kallon shi. Shima ita yake kallo da wasu birkitattun eye's nashi da suka fara canja launi zuwa ja, matsowa yayi kusa da Ita murya a shak'e yace "Baby what wrong? " Girgiza kai kawai take tana hawaye ganin haka ya sanya shi cewa "Okay shikenan yanzu ki je kiyi wanka kinji " Da muryar rarrashi ya fad'a gid'a kanta tayi kawai, ganin tak'i tafiya ya sanya shi barin d'akin ya tafi side d'in shi yana jinjina yarintar Suhaima daga zuge zipe shine take k'ara. Yana fita Suhaima tayi saurin zare rigar ta shiga toilet wanka tayi da ruwan d'umi sosai ta gasa jikinta Saboda gajiyar da take tattare da ita sannan tayi alwala ta fito, lotion kawai ta shafa sannan ta fesa body sprays da shafa humra a jikinta sannan ta sanya wata red d'in sleeping dress mai siririn hannu ce tsayin ta iyakar gwiwa sai ta d'ora ta saman ta wanda ake d'aure ta da mad'auri a gaba kayan sun mata kyau, tana cikin gyara gashin kanta Sabeer ya turo k'ofar ya shigo, sai da gaban Suhaima ya fad'i shima yayi wankan shi cikin sleeping dress na maza farare ne sol masu laushi sosai, kallonta yake tamkar ya lasheta haka yake ji. "Baby zo mu yi sallah " Hijab ta d'auko mai hannu har k'asa ta sanya sannan suka tada sallah sai da suka yi sallahr ishsha sannan suka kawo raka'a biyu ta nafila ya dad'e yana musu addu'o'i na samun zaman lafiya da zuri'a mai albarka, ya dafa kanta yayi addu'ar da Annabi SAW ya umarci kowanne ango da yayi wa amaryar shi. Yana gama wa ya tashi ya fita bai dad'e ba ya dawo d'akin hannun rik'e da babban plate, ajiye shi yayi ya fara bata naman abaki kad'an ta iyaci ta girgiza kanta alamar ta k'oshi sannan ya bata fresh milk tasha, shima kad'an ya iya ci ya barshi don sun ci abinci a wurin dinner. Janyo ta yayi jikin shi yana rad'a mata "Baby ki saki jikin ki dani please bazan cutar da ke ba" Ita dai gaba d'aya jikinta rawa yake na tsoro, yana kok'arin had'a bakin shi anata yaji alamar shigowar message a wayan shi d'an tsaki yayi kad'an sai lokacin ya tuna da bai kashe ta ba. Janyo wayar yayi

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});