Chapter 19
Chapter 19
hakan yana mik'a mata hijab d'in ta, bata yi musu ba ta sanya hannu ta kar6a tare da sanya wa, daidai lokacin Suhaima ta gama gyaran wajen ta k'araso rumfar, kallon ta Aliyu yayi tare da cewa "Ki tafi gidan Babaa Lantana ki zauna zamu je asibiti ne " Fuskar Suhaima d'auke da tsantsar damuwa tace "Toh Yaya Allah ya dawo daku lafiya, Aunty Aliyah sannu Allah ya baki lafiya " "Amin ya rabbi " Cewar Aliyu don Aliyah bata iya magana saboda jin jikin da take yi, d'aki Suhaima ta shiga ta d'auko hijab d'in ta sannan ta fito hannu Aliyah ta rik'e suka fito zuwa kofar gida, inda Yaya Aliyu ya fito da machine d'in, sai da ya kulle gidan tukunna ya hau machine d'in dakyar Aliyah ta iya hawa saboda rashin jin dad'in jikin ta, sai da Suhaima ta ga tafiyar su sannna ta k'arasa gidan Babaa Lantana. Da sallama ta shiga gidan Babaa Lantana da take wajen marhu tana soya gyad'a ta siyar wa ta amsawa Suhaima sallamar tana cewa "Tabbb yau wa nake gani a gidan nan ba dai Suhaima ba?" Ta fad'a cikin sigar wasa, d'an murmusawa Suhaima tayi tare da cewa "Ni ce nan Babaa Lantana ina d'an tsohon ki? " Suhaima ta k'arasa fad'i tana zama kusa da Babaa Lantana. "D'an tsoho ya fita can gidan mai unguwa zasu tattauna matsalalon mu na garin nan musamman akan al'amarin matasa" "Yayi kyau hakan " Cewar Suhaima kenan "Lafiya dai kike koh? " Cewar Babaa Lantana tana sauke kaskon suyar gyadar, kallon ta Suhaima tayi tare da cewa "Me kika gani? " "Ganin ki nayi kamar fuskar ki da damuwa ne " "Uhm Babaa Aunty Aliyah ce bata da lafiya yanzu haka sun tafi asibiti da Yaya " Da sauri Babaa Lantana tace "Me yasame ta? " "Tun jiya take kwara amai har yau bai tsaya ba ko ruwa tasha sai ya dawo duk ta rame " D'an shiru Babaa Lantana tayi kafin kuma ta saki murmishi akan fuskar ta daman tayi hasashen haka don taga alamomi sosai a jikin d'iyar ta ta magana ce bata yi ba. Kallon mamaki Suhaima take yiwa Babaa Lantana ganin tana murmishi kamar wadda tayi mata wani babban albishir ba lalura ta fad'a mata ba kasa hak'ura tayi Babaa Lantana tayi magana tace "Wai Babaa lafiyar ki kalau ina fad'a miki rashin lafiyar Aunty kina murmishi? " "Uhm Suhaima ai abin farinciki ne ya samu shi yasa kika ga ina murmishi " Cikin rashin fahimta Suhaima tace "Rashin lafiyar Auntyn ne abin farinciki? " 'Yar dariya Babaa Lantana tayi tare da cewa "Matsala ta da ke Suhaima rashin gane wa ina nufin Auntyn ki ciki ne da ita wannan lalurar da take yi ta laulayin ciki ne kin fahimta? " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Suhaima daman burin Aunty Aliyah ta samu ciki ta haihu kusan kullum sai ta fad'a wa Suhaima ta taya ta da addu'a Allah ya bata 'ya'ya, sai gashi Allah maji rik'on bawan shi ya bata, lallai yau Aunty Aliyah da Yaya Aliyu akwai murna an samu abin da ake so, amman duk da haka sai da Suhaima tace "Da gaske kike Babaa? " "Insha Allahu kuwa Suhaima " Washe baki Suhaima tayi tana mai jin dad'i farinciki fal cikin zuciyar ta tana jiran dawowar su Yaya Aliyu. Suna nan zaune Suhaima na taya Babaa Lantana d'aurin gyad'ar a leda suka ji tsayuwar machine d'in Aliyu a kofar gida, da gudu Suhaima ta fita har tana wancakali da faratin gyad'ar ya watsowa Babaa Lantana a fuska amman Suhaima bata tsaya ba tayi waje da gudu. "Oh ni 'yasu Allah ya shiryi Suhaima ji yanda ta zubar min da gyadar nan " Cewar Babaa Lantana tana tsince gyadar da ta zube a k'asa. Suhaima tana fitowa kofar gida ta hango su har ma Yaya Aliyu ya bud'e gidan sun shiga, da sauri Suhaima ta k'arasa gidan ta shiga kallon fuskar Yaya Aliyu tayi taga sai washe baki yake haka ma Aunty Aliyah duk da kuwa jin jikin da take hakan bazai sa mutum ya kasa fahimtar farincikin dake shimfid'e a fuskar ta ba, nan Suhaima ta tabbatar da ciki ne dai da ita zancen Babaa Lantana ya zama gaskiya. "Albishirin ki " Cewar Yaya Aliyu yana kamo hannun Suhaima, cikin murmishi tace "Goro fari tas Yaya " 'Yar dariya yayi kafin yace "Auntyn ki ciki ne da ita zata haifar miki d'a " Wani tsalle Suhaima ta daka ta rungume Yaya Aliyu tana dariya kafin ta cika shi ta rungume Aunty Aliyah tana cewa "Wayyo dad'i Allah mun gode maka " Hannun Yaya Aliyu ta rik'o dana Aunty Aliyah tace "Yaya Aunty na taya ku murna sosai Allah ya fito mana dashi lafiya " "Amin Thumma Amin " Suka fad'i fuskar su k'unshe da murmishin farinciki, ana haka Babaa Lantana ma ta shigo ita da Baba Adamu don dawowar shi kenan Babaa Lantana take sanar mishi shine suka taho duba jikin Aliyah. Anan Baba Adamu yaji abin farinciki daman Babaa Lantana ta hasaso hakan, nan suka taya juna murnar samun k'aruwar da zasu samu kafin daga baya su yi musu sallama su tafi...... Aishat A Muh'd 🏌🏻♀ [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 28-29 Tun daga lokacin ya kasance Aunty Aliyah bata da ishashshiyar lafiya a jikin ta yau lafiya gobe ciwo, duk ta rame sosai saboda laulayin da ya sanya ta a gaba, aiyukan gidan kuwa Suhaima ce mai yin su don Aliyah bata iya komai sai kwanciya saboda rashin k'arfin jikin ta dakyar take iya tashi zaune, ga baccin da take sosai abinci ma ba kowanne take iya ci ba ba k'aramin walaha take sha ba. Da haka aka cinye kwanaki biyar Aunty Aliyah tana fama da azababben laulayi, ya rage sauran kwanaki biyu a fara bikin Jiddah kuma ayau ne ranar da Jiddah ta fad'a zata zo ta dauk'i Suhaima su tafi gidan su don fara hidimar biki, gashi Aunty Aliyah ba lafiya Suhaima ma ta fitar da ran zuwa bikin Jiddah saboda ganin yanda jikin Aunty Aliyah yak'i sauk'i duk hidiman gidan ita kad'ai ce mai yi don ma wani lokacin Babaa Lantana na zuwa taya ta 'yan ayyuka. Wajen k'arfe biyun ranar laraba Jiddah ta zo lokacin Suhaima ta kammala girkin rana tana share gidan taji da sallamar ta aikuwa yar da tsintsiyar hannun tayi da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su cikim tsananin jin dad'i. "Amarya kinsha k'amshi sai wani kyalli kike tun kafin a fara jin amarcin " Cewar Suhaima cikin murya k'asa k'asa tana dariya, dukan wasa Jiddah ta kawo hannu zata yi mata da sauri Suhaima ta goce suna dariya. "Allah Suhaima kin fara zama mara kunya, zan fad'a wa Yaya Aliyu yayi miki aure ke ma " Rik'e bakin ta Suhaima tayi da hannun ta d'aya kafin tace "Wooh rufa min asiri ni har yanzu yarinya ce da saura " Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa "Uhm a hakan kike yarinya ai kuwa ki zuba ido ina aure zan ziga Yaya Aliyu yayi miki ke ma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104