Chapter 5
Chapter 5
mai d'umi a bakin ta, a hankali Fatima take kur6a har ta gama shan kusan rabin kofin, sannan ta zame bakin ta a bakin kofin tana girgiza wa Babaa Lantana kai alamar ya ishe ta. Sauke kofin tayi a k'asa ta ajiye, tukunna ta d'auko kofin maganin da aka jik'a ta bawa Fatima tasha, bayan ta gama ta kwanta tana mai mayar da ajiyar zuciya, ita kad'ai tasan abin da take ji cikin jikin ta. Babu dad'e wa bacci ya d'auke ta, fito wa suka yi zuwa tsakar gidan gaba d'ayan su don kada ayi hayaniya ta tashi, Babaa Lantana da Suhaima suka fara kimtsa gidan da yake Fatima bata sangartar da ita ba, tana d'an sata aikace aikacen da zata iya wanda baifi k'arfin ta. Aliyu kuwa fita yayi a gidan don zuwa neman wani aikin da zai siyo wa Inna lemo da kankana don tasha, tun da yasan mara lafiya yafi son cin kayan itatuwa fiye da komai. Babaa Lantana tana wanke wanke ne Aliya d'iyar ta ta shigo gidan, nan ta kar6i aikin da Babaa Lantana take yi ta cigaba da yi, gefe d'aya Suhaima nayi mata dauraya. Lokacin da Farima ta farka daga baccin jikin ta da d'an dama don ta iya tashi taje band'aki da kanta, sai dai har zuwa lokacin jini yana zuba a jikin ta, amman ba mai yawa sosai ba, sai bayan ishsha Babaa Lantana ta tafi gida, ta bar Aliya anan wurin Fatima ko zata na taimaka mata da wani abin a yafi k'arfin Suhaima. Bayan tafiyar kenan Aliyu ya dawo gidan da yankan kankana a hannun shi k'arami sai lemo mai 6ayo guda biyu, dakyar ya same su bayan yasha wahalar ferar lemo mai tarin uban yawa da mai siyar da lemon ya bashi, sannan ya bashi wannan kankanar da lemon tare da nera ashirin, cikin farinciki ya taho gida. Bayan ya shigo gidan duk suna d'aki don haka ya shiga kitchen ya d'auko silver da wuk'a ya yanka su k'anana sannan ya shiga d'akin da sallama, Fatima, Aliya da Suhaima suka yi amsa mishi, da sauri Suhaima ta mik'e tana rik'e shi cikin shagwa6a tace "Yaya shine kayi zaman ka ina ta jiran ka, kasan bana son ka fita ka dad'e " D'an murmishin yak'e yayi tare da shafa kanta yace "Yi hak'uri 'yar k'anwa ta aiki ne ya tsare ni " "Toh Yaya na " Fatima kallon su take kawai, kafin wasu hawaye su zubo mata, da sauri ta sanya hannun ta, ta goge su don kada su Aliyu su gani, don ma babu wadataccen haske a d'akin. K'arasa wa yayi inda take ya zauna tare da mik'a mata silver d'in yace "Inna gashi kisha, ya sauk'in jikin naki? " "Da sauk'i Aliyu nah, nagode Allah yayi muku ya albarka " "Amin Inna" Aliyu ya amsa, nan ya fara bata a baki a hankali, bayan ya d'an sanwa Suhaima don Aliya k'in kar6a tayi. A hankali yake bata har ta shanye tas, sannan ya d'auke silver d'in ya bawa Aliya takai kitchen, shi kuma ya fara jera wa Fatima tambaya akan yanda take jin jikin nata, Fatima kuwa amsa mishi kawai take da sauk'i, har zuwa lokacin kwanciya bacci, har ya tafi Fatima ta kirawo shi tana dad'a yi mishi nasiha tare da k'ara bashi amanar ya kula da kanshi da Suhaima, jiki a sanyaye Aliyu ya fito ya shige d'akin shi. Can cikin dare wajen asuba ne jini ya tsinke wa Fatima kafin kace me tuni ta fara fita daga hayyacin ta, aikuwa Suhaima da gudu ta shiga d'akin Aliyu ta taso shiga, daman ba baccin yake ba, don gaba d'aya ji yayi baya jin bacci a idanun shi, ganin Suhaima tana kuka ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba, ko tambayar ta bai tsaya yi ba ya fito daga d'akin nashi ya fad'a d'akin Fatima. Yana shiga yaga abin da ya gigita shi, ya rud'u iya rud'ewa kamar wani babban mutum, da sauri ya k'arasa wajen Inna Fatima ya rik'e ta yana fashe wa da kuka yace "Inna don Allah kada ki tafi ki bar mu, ki bud'e idanun ki " Ya fad'i hakan ganin yanda take lumshe ido tana jan numfashi da dakyar, gashi ta kasa magana sai kok'arin bud'e baki take tayi magana ta kasa bud'e shi, kallon Aliyu kawai take da Suhaima. "Yaya Aliyu ka kirawo Babaa mana " Yaji saukar muryar Aliya a kanshi, sai lokacin ya tuna hakan, aikuwa ya ajiye Inna a hankali ya fita da wani irin gudu. Fatima bin shi da kallo tayi Sannan ta mayar da kallon ta kan Suhaima, sai kuma a hankali ta bud'e bakin ta zata yiwa Suhaima magana, amman sai kawai taji ta tsinci bakin ta da furta kalmar shahada, a hankali ta k'arasa fad'a sannan Lokacin d'aya kuma numfashin ta ya tsaya da aiki, idanun ta kuma a lumshe suke har zuwa lokacin da zuciyar ta tabar bugawa komai na jikin ta ya tsaya cak da aiki ya daina motsi, ta koma tamkar wadda ta mutu ko irin ta suman nan. Da iyakacin k'arfin shi yake bugun gidan Babaa Lantana yana d'aga murya da k'arfi yana kiran Babaa Lantana da Baba Adamu, sam kamar Aliyu baya cikin hayyacin shi yama mance da wani dare ne Saboda tsabar rud'ewa. Da sauri Babaa Lantana da Baba Adamu suka fara rige rigen bud'e kofa, jin muryar Aliyu, Baba Adamu ne yayi nasarar bud'e kofar saboda Babaa Lantana zaninin jikin ta da kunce yana kok'arin sullu6e wa k'asa. And rikice Aliyu ya rik'e hannun Baba Adamu yana cewa "Ku taimaka min Inna ta " Abin da ya iya furta kenan, aikuwa tsakanin Babaa Lantana da Baba Adamu tare da Aliyu suka kasa tsere don shiga gidan. D'akin Fatima suka fad'a dukanin su, kallo d'aya Baba Adamu yayi wa Fatima yasan bata numfashi, ganin haka ya sanya korar Aliyu, Aliya da Suhaima daga d'akin. Suna fita Baba Adamu ya kalli Babaa Lantana ido jawur yace "Sai dai mu yi hak'uri Lantana Fatima ta rigamu gidan gaskiya " Hannu Babaa Lantana ta sanya a kanta dukka hannun tare da zaro ido tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Malam da gaske Fatima ta mutu ko suma tayi ne " Cikin dauriya Baba Adamu yace "Haba Lantana ki kalle ta da kyau, ai kina kallon Fatima kinsan gawa ce " Lokaci d'aya Babaa Lantana ta rushe da kuka sosai, yayin da Baba Adamu ya sanya zani ya lullu6e ta tun daga saman kanta har k'afar ta, Sannan ya kamo hannun Babaa Lantana suka fito waje tsakar gida, ina Suhaima da Aliyah suka yi tsuru tsuru suna kuka, yayin da Aliyu ya kasa zama waje d'aya sai safa da marwa yake yi. Ganin fitowar Babaa Lantana da Baba Adamu jikin su a sanyaye ga Babaa Lantana tana kuka, yasa Aliyu tahowa wajen su da sauri yana cewa "Ku fad'a min meke faruwa, ina Inna ta, kada ku ce min ta mutu don Allah " Babu wanda yayi karfin halin yi mishi magana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai d'akin Lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai...... Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in banyi editing ba. Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻:
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104