Chapter 58
Chapter 58
Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 77-78* *_AFTER 2 WEEK'S_* Duk wasu shirye shirye na bikin kusan an gama kammala komai sai jirab ranar lokacin wanda ya kama nan da next week zasu fara shagalin biki. Amarya Suhaima kuwa ta k'ara wani irin kyau da cika a jikinta duk wani gyara na saman fata da ciki yi mata ake yi amman masu kyau da inganci ake amfani dasu, har anje anyi mata jeren kayanta a gidan Sabeer, sosai Yaya Aliyu yayi mata kok'arin siya mata kayan d'aki zuwa na kitchen na zamani don Aunty Aliya da Jiddah sai Suhaima suka tafi zuwa kasuwa suka siyo duk abin da ya dace. Suhaima ce gaban dressing mirror tana taje dogon gashin kanta bayan ta gama taje wa ne ta d'aure shi da ribbon sannan ta mik'e ta zura wata black gown mai touch d'in red a jiki sai tayi rolling kanta da veil d'in gown d'in black shima, nan 'yar beautiful face nata ya fito gwanin sha'awa gata daman abin ka da fari cikin bak'in abu, bata yi wani makeup sosai ba simple make-up tayi daga powder sai red na jambaki da ta sanya ta taje kwantaccen gashin girar ta sai kawai ta fesa perfumes different colours ajikin ta masu sauk'in k'amshi. Black flat shoes ta d'auko ta sanya a k'afar ta, gama sanya takalmin kenan taji wayarta na ringing d'auka tayi tare da yin picking cikin sanyin murya tace "Hello! " "Hi! Mata ta kina ina gashi na k'araso" Fuskarta d'auke da murmishi tace "Gani nan zuwa kana ina? " Sai da ya lumshe ido kafin yace "Baby ina zaune cikin mota a k'ofar gida" "Okay gani nan zuwa" Tana gama fad'in haka ta kashe wayar, sannan ta fito zuwa tsakar gida Aunty Aliya ce tana zaune sai faman shirya Ameer tayi wanda tayi mishi wanka yanzu, kallon ta tayi fuskarta d'auke da smiling tace "Amarya tasha k'amshi hala angon ya k'araso?" "Eh Aunty Aliya ya k'araso" "Naga alama ai irin wannan kyau haka kada ki rud'a musu d'a ya kasa kai kanshi gida" Cike da zolaya Aunty tace, sunk'e kai Suhaima tayi cikin 'yar jin kunya tace "Kaiiii Aunty! " "Gaskiya ne ai, ki tafi kin barshi a waje shi kadai" Tashi tsaye tayi ta nufi k'ofar fita a gidan cikin tafiyar ta na nutsuwa, Aunty Aliya ta bita da kallo don kwalliyar nata ya birge ta. Tana fita suka yi 4 eye's da Sabeer wanda yake tsaye ya jingina bayan shi da mota ya hard'e hannun shi saman kirjin shi ya zubawa k'ofar fitowa ido yana kallon ta inda Babyn shi zata fito. Ajiyar zuciya ya sauke wanda Musaddiq da yake kusa dashi sai da yaji shi har ya d'ago daga danne dannen da yake a phone nashi suna charting da Mufidah ya kalli Sabeer sannan ya kalli inda yake kallo, ko ba'a fad'a mishi ba yasan wannan ce Suhaima amman yayi mamakin yanda sam batayi kama da en k'auyen ba anya ba zuwa take family d'in en uwanta hutu ba, sai dai kuma da ganin ta k'aramar yarinya ce sosai don bata fi 17 zuwa 18 ba, d'aga kafad'ar shi yayi alamar ba damuwar shi bane na sanin ko ita wace, don haka sai kawai ya cigaba da abin da yake. Kallon ta Sabeer yake tamkar ya had'iye ta haka yake ji ko kuma ya d'auke ta ya tafi da ita gaba d'aya ta kid'ima shi, gaba d'aya Suhaima ta rasa nutsuwar ta saboda irin kallon da Sabeer yake mata, kunya ce ta lullu6e ta kawai dakyar ta iya k'arasa wa inda suke tayi musu sallama amsawa sukayi kafin ta gaida su, nan Sabeer ya k'ara gabatar mata da Musaddiq a matsayin abokin shi na sosai, nan suka k'ara gaisawa tana tambayar shi iyalan shi. Sannan Musaddiq ya shige cikin mota don shi ba mai son magana ba ne, zama Suhaima tayi saman wani dutse mai d'an fad'i da tsayi ta kasa magana duk a tak'ure take, ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu sannan yace "Baby nah ji nake tamkar na d'auke ki na gudu da ke, kinyi min kyau sosai " Ya k'arasa fad'i eye's nashi akan lips nata har sai da ya had'iyi yawu har ya hango shi irin shan da zai mishi bana wasa ba kuwa idan ya kama shi. "Baby kin yi shiru fah kin bar ni da surutu ni d'aya " D'an murmishi kawai tayi kafin tace "Ba haka bane ni na rasa abin da zance ne?" "Haba yarinya daman mata tana rasa abin da zata ce idan zasu yi hira ita da mijinta " Ya k'arasa maganar yana zama kusa da ita, d'an turo mishi bakinta kad'an tayi tukunna tace "Toh! Ni mai zance maka" "A'a babu komai kiyi ta kallona ma kawai " D'an hararar shi tayi ta gefen ido kad'an, ashe ya gani d'an girgiza kai yayi yana murmishi yace "Ni kike harara yarinya koh!?, ki cigaba komai da lokacin shi nima nawa ya kusa" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben azurfar hannun ta yayi da shi kuma ya tsurawa dogayen 'yan yatsun ta ido ji yake tamkar ya lashe su kai shi da yana da dama gaba d'ayan ta zai yi mata don yanda ta k'ara yi mishi wani kyau na daban. "Duk naji event's d'in da zaku yi Baby sun isa ko zaku k'ara? " "A'a sun ishe mu ni da ba wasu kawaye ne dani sosai ba, da Jiddah ma zata yarda iya walimah kawai zamu yi '' "Haba Baby ayi mana har da dinner saboda aboki nane ya had'a mana gashi family d'ina sun had'a mana wata ranar da aka kawo min ke" D'an shiru yayi yana kallonta kafin ya cigaba da cewa "Ni sai naga kamar zasu takura min yaushe har aka gama dinner mu dawo gida sannan mu bawa junan mu kulawa... Uhm kin dai gane? " Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira wata kunya ce ta sake lullu6e Suhaima daman haka Sabeer yake, ta rasa abin cewa tayi tsit da ita tamkar babu ita a wurin. "Ya dai Baby ko kin gaji ne? " "Uhmmm" Kawai ta iya cewa don tana tsoron ya Kara 6aru mata wani sabon rashin kunyar tashi, nan dai sai ya sako wani zancen na daban sannan ta saki jikinta suka d'an ta6a hira. "Washhh! Baby bari mu zo mu wuce gida kinsan wancen mutumin duk ya dame ni da kira yana tsoron kada matar shi ta rufe mishi k'ofa yak'i shiga gidan baya son yin nesa da matar shi sai dole " "Uhm ai ya kyauta gwara yana bata kulawa matsayinta na matar shi, don mazan da basa kula da matansu haushin su nake ji" "Eyyye Baby kice nima haka za'a na rik'e ni a gida " "Ai bani zan ma rik'e ka ba da kanka zaka zauna ma " ta k'arasa maganar da murgud'a baki. Er dariya kawai yayi yana cewa "Huh Baby rigima ni ake murgud'a wa baki koh, to bari nazo na tafi baza ki k'ara gani na ba sai ranar dinner " Nan suka yi sallama da junan su kamar kar ya tafi haka yake jin shi don gani yake 1 week d'in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104