Chapter 17
Chapter 17
ne sai kawai ta k'urawa mirror ido tana kallon shi, ta fad'a tunani beautiful guy d'in da ta yi mishi tsiwa d'azu ta d'an jima tana tunanin shi a haka har sai da Aunty Aliyah taji ta shiru ta fara kwalla mata kira tukunna ta sauke ajiyar zuciya ta fito waje tana amsa kiran da take mata... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Where are U guys dis page is dedicated to oll My sisters of (Exclusive Writers Forum), i luv U all my sisters i really luv U guys like totally 👄 PAGE 24-25 Bayan kwanaki 2 kamar yau ranar laraba da yammaci wajen 4:30,Suhaima tana zaune a bedroom nata gyaran wardrobe d'in ta take gefe d'aya kuma Aunty Aliyah zaune gefen gadon tana mik'o wa Suhaima kayan da ta linke ita kuma tana jera su a wardrobe sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali. "Assalamu Alaikum " Kamar a mafarki Suhaima ta jiyo sallamar Jiddah, aikuwa da sauri ta wullar da kayan hannun ta da Aunty Aliyah ta mik'o mata, da gudu ta fita waje zuwa tsakar gidan cikin farinciki. Jiddah tana tsaye a tsakar gidan sai murmishi take tana rarraba ido don hango ta inda Suhaima zata fito, tana hango fitowar ta a d'aki aikuwa da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su suna dariya cikin tsantsar farinciki na jin dad'in ganin juna don anjima ba'a had'u ba. Cika junan su suka yi cikin murmishi Suhaima tace "My besty sannun ki da zuwa" Kunshe da marmishi kan face d'in Jiddah tace "Yawwa tawan kwana da yawa " Ta fad'i hakan suna kok'arin k'arasa shiga d'akin Suhaima, cikin fara'a Aunty Aliyah tace "Lale maraba da mutanen birni Jiddah kece tafe yanzu da yamma? " Zama Jiddah tayi akan sallayar da Suhaima ta shimfid'a mata a k'asa ganin kan gadon kaya ne akai, sannan Suhaima ta fita zuwa kitchen don samo wa Jiddah abin motsa baki. "Aunty kam nice tafe yanzu, ina yini? " "Lafiya qlau Jiddah, ya gida da iyayen ki? " "Duk suna nan lafiya Aunty suna gaida ku " (Hmmm Jiddah ta fad'i hakan ne kawai, amman gaskiyar zance iyayen ta basu san wasu su Aunty Aliyah ba, kawai suna jin tana basu labarin Suhaima duk a zaton su friend nata ne na schl, ko zuwa nan gidan nasu da take basu san da zuwan ba). "Muna amsa wa, ya fama da hidimar biki don nasan satin da zamu shiga shine na bikin koh? " Aunty Aliyah ta tambaye ta tana mik'ewa tsaye, cikin d'an jin kunya Jiddah tace "Ehh Aunty haka ne, ina Yaya Aliyu? " "Ya zagaya cikin gona ne amman yanzu zaki ga ya shigo " Har Aunty Aliyah zata fita daga d'akin da sauri Jiddah ta tsayar da ita tare da sanya hannu cikin hang bag nata ta d'auko wani kyakkyawan invitation card guda biyar ta mik'awa Aunty Aliyah tare da cewa "Aunty wannan card d'in d'aurin aure ne na Yaya Aliyu da na Baba Adamu ne " "To shikenan zan bashi idan ya shigo " D'an marairaice fuska Jiddah tayi tare da cewa "Amman Aunty zaku je ai? " D'an murmishi tayi tare da cewa "Me zai hana Jiddah insha Allah zamu je, Allah ya kaimu dai lokacin da rai da lafiya " "Amin Aunty, sannan don Allah ki dad'a tunawa Yaya Aliyu sauran kwanaki 2 d'aurin aure zan zo na tafi da Suhaima " "Zan fad'a mishi Jiddah kuma zai barta insha Allah " 'Yar dariyar farinciki Jiddah tayi tare da cewa "Yawwa Auntyn mu ngde " Daidai lokacin Suhaima ta shigo d'akin hannun ta d'auke da k'aramin tire wanda ta sanya abinci aciki da kuma lemon so6o acikin k'aramin jug na roba sai cup d'in shi k'arami, ajiye wa tayi gaba Jiddah Aunty Aliyah kuma ta fita don ta barsu su yi hirar su. Bud'e plate d'in Jiddah tayi aikuwa ta had'a ido da wani lafiyayyen dambu wanda yasha zogale da gyad'a ga ainahin man k'uli da kuma yajin da aka daka da kayan k'amshi da tafarnuwa, muk'ut Jiddah ta had'iyi yawu saboda tana son dambu sosai, dariya ce ta kubce wa Suhaima ganin yanda Jiddah take had'iyar yawu don kawai taga dambu. Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa "Tun da dariya kike min na fasa baki cup cakes d'in da nayi miki Aunty Aliyah da Yaya Aliyu zan bawa " Danne dariyar ta Suhaima tayi tare da rik'o hannun Jiddah tana cewa "Haba tawan just kin ban dariya ne ganin yanda kike had'iyar yawu but na daina" Gid'a kai Jiddah tayi kawai saboda ta cika bakin ta da dambu ba damar tayi magana har wani lumshe ido take saboda dad'in da yayi mata, hannu Suhaima takai kan jug ta zuba mata so6on a cikin cup ta ajiye mata kusa da ita, sannan ta koma wajen wardrobe tana cigaba da gyaran kayan suna d'an hira da Jiddah jefe jefe har ta kammala cin abincin ta taya Suhaima k'arasa gyaran kayan, bayan sun gama suka fita zuwa tsakar gidan inda Aunty Aliyah da Yaya Aliyu suke zaune a saman tabarma shigowar shi kenan babu dad'e wa, nan suka gaisa da Jiddah tare da yi mata fatan alkhairin auren da zatayi tare da 'yar nasiha, sosai Jiddah taji dad'in haka tare da yi mishi godiya duk jikin ta yayi sanyi. Suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib nan Yaya Aliyu yayi alwala ya wuce masjid, yayin da Suhaima, Jiddah da Aunty Aliyah suka yi nasu alwalan tare da gabatar da tasu sallahn. Bayan sun idar ne da sallahr Jiddah tayi wa driver d'in ta waya, babu dad'e wa yayi sallama a kofar gidan Jiddah ta tashi taje inda yake tsaye kofar gida ta kar6i abin da ta buk'aci ya kawo mata wata 'yar bag ce black mai kyau madaidaiciya wadda zata cinye kayan mutum set 5 a ciki. Shigowa gidan tayi tare da ajiye bag d'in gaban Suhaima tace "Besty ga ankon ki fah ki duba ki ga yayi miki " Sakin baki Aunty Aliyah da Suhaima suka yi suna kallon ta cike da mamaki, bayan d'azu da safe Yaya Aliyu yace gobe zai bata kud'in ankon da na gifts d'in da zata siya mata sai gashi kuma Jiddah ta zo mata dasu. Murmishi Jiddah tayi ganin yanda suke kallon ta kafin tace "Aunty wannan kallon fah, ni ku duba kuga yayi? " Ta k'arasa magana cikin shagwa6a ganin sun k'i bud'e bag d'in tamkar masu jin tsoron akwai wani mugun abun aciki, ya sanya Jiddah ta janyo bag d'in kusa da ita ta bud'e, sai ga wasu tsadaddun kaya kala hud'u ta fito dasu masu matuk'ar kyau da tsada, swiss atampha, lace guda biyu da kuma wa wani material Light pink mai haske da abin nad'in kai pink shima amman mai duhu, anyi d'inkin gown ajiki yayi masifar yin kyau, sai shoes and hang bag set d'aya da su watch k'irar gucci na mata da kuma abin hannu, sark'a d'an kunne kai abubuwan kyalakyale sosai Jiddah ta zuba wa Suhaima. Rasa bakin godiya Suhaima da Aunty Aliyah suka yi har sun bud'e
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104