Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 89

Chapter 89

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

buga k'ofar gidan tashi tayi taje tana tambayar wane sai taji muryar Yayanta Aliyu bud'e k'ofar tayi tana murmishi tace "Yayah sannu da dawowa? " Shima fuskar shi d'auke da murmishin yace "Yawwa Suhaima ya zaman gida ke kadai don nasan Aliyah ta tafi gidan suna koh? " "Eh Yaya ta tafi sai ni kadai duk tsoro ya kama ni " "Ai dama ke matsoraciya" Cewar Yah Aliyu yana dariya cikin shagwa6a tace "Kaiii Yayah aikuwa ni jaruma ce " Hannun ta ya kamo suka k'arasa cikin gidan yana biye mata, bayan yayi wanka ta zuba mishi abinci yana ci suna hira yana bata labari akan harkar karatun shi tana yi mishi addu'ar Allah ya taimaka, yana tsaka da cin abincin Sabeer ya shigo gidan bakin shi d'auke da sallama. Sanin muhimmancin sallamar ne ya sanya Yah Aliyu amsa mishi ko k'arasa shiga tsakar gidan bai yi ba ya juya zuwa cikin zaure ya shimfid'a tabarma ya zauna akai kawai, wani tausayin shine ya kama Suhaima wanda ya sanya ta binshi da kallon tausayi, ashe duk wannan kallon da take binshi dashi Yah Aliyu yana kallonta shima girgiza kanshi yayi kawa ya cigaba da cin abincin shi. "Ki zuba mishi abinci ki kai mishi " Ya furta hakan kamar bashi yayi maganar ba, aikuwa tsam ta mik'e da sauri taje kitchen ta zuba mishi tare da d'iban ruwa ta kai mishi, duk abin da take Yah Aliyu yana kallon ta yana kula da yanayin ta, bayan ta dawo daga kaiwa Sabeer abinci ta wuce d'akin ta kawai. Ahaka har aka kwashi tsayin sati biyu Sabeer na kwana a zaure har zuwa yanzu babu wata kyakkyawar fahimta tsakanin shi da Aliyu, ga wani irin tari da zazza6i mai zafin gaske da yake yi da cikin dare baya iyayin wani cikakken bacci duk yabi ya rame sosai yayi bak'i ga rashin aski duk gashi ya cika mishi fuska ko abincin kirki baya iya ci, gashi kirjin shi yayi mishi wani irin nauyi gashi tsakiyar damina akai ana samun ruwa akai akai sosai. Suhaima tana tausayin Sabeer ganin yanda ya koma har kuka take a 6uye, Aunty Aliyah tayi tayi dashi Ashiru ya rakashi chemist yak'i zuwa yayin da Yah Aliyu yake ce mishi ya tafi gidan su bazai iya zaman nan ba tunda shi ba d'an wahala bane kawai ya sakar mishi k'anwar shi, Sabeer idan yaji haka sai kawai yayi murmishi kawai shi ciwon da yake damunshi da k'in kulashi da Suhaima take yafi komai d'aga mishi hankali. Kamar yau tun kafin mangarib ake ruwa har zuwa bayan sallahr ishsha bai tsayaba sai dai idan lokacin sallah yayi ya d'an tsaya, Sabeer yana tukunkune a zaure yana rawar sanyi sosai ga tari da yake faman yi idanun shi sunyi ja sun k'ara fitowa sosai saboda tarin da yake yi zuwa can kuwa numfashin shi ya fara d'auke wa kafin daga bisani ya tuntsire a k'asa yana jan numfashi dakyar. Suhaima kuwa tana zaune a d'aki sai faman kukan zuci take tasan Sabeer yana can yana fama da dukan ruwan wani tausayin shine yake ratsa mata zuciya tana fitar da hawaye. Yah Aliyu kuwa da Aunty Aliyah sai fad'a suke tana fad'a mishi idan Sabeer ya mutu mai zai cewa iyayen shi wannan horan haka ya isa duk yaro yabi ya rame yayi bak'i ga rashin lafiyar da yake fama da ita nasan zuwa yanzu yayi horan da bazai sake maimaita abin da yayi ba. "Aliyah ana dole ne nace ya rabu da ita kuma bani na ce yazo ba fah ya zauna ra'ayin shine to ni mene ruwana " "Haba Yah Aliyu nasan ka da tausayi zuciyar ka mai kyau ce kayi hak'uri ka yafe mishi, baka ganin yanda Suhaima ma ta shiga damuwa kada ka shiga hakk'in su fah da yawa tana son mijinta shima yana son matar shi don me yasa baza ka hakura ka bashi matar shi ba kuma na tabbatar kana son Sabeer ya kasance da Suhaima har k'arshe rayuwar ta, bakasan abin da Allah ya 6oye ba kawai ni a shawara ta ka bashi matar shi don Allah Yah Aliyu " Cewar Aunty Aliyah tana kama hannun shi fuskar ta tab da hawaye, shiru Yah Aliyu yayi yau Aliyah ta tunasar dashi abubuwa da dama, take yaji zuciyar shi tayi sanyi ya kalli Aliyah yace "Naji na amince zan bashi matar shi " Wani dad'i ne ya ratsa zuciyar Aunty Aliyah tayi murmishi tana cewa "Ko kaifa Yah Aliyu naji dad'i sosai don Allah yanzu ka taso muje ka ce ya koma d'akin Suhaima " Hannun shi yasa ya ja hancin Aliyah yana cewa "Toh Mata tagari angama taso mu tafi " Ya mik'e tsaye yana murmishi tare da kamo hannun Aliyah suka fito zuwa zaure, sai dai suna shiga zauren hankalin su yayi masifar tashi ganin yanda Sabeer yake jan numfashi dakyar yana rik'e da kirjin shi ga kuma tarin da yake. Da sauri suka k'arasa inda yake Yah Aliyu ya tashe shi zaune tare da rik'e shi yace "Sabeer me yake damun ka? " Kallon Yah Aliyu yayi kafin yayi luuu da eyes nashi kamar wanda yasha kwaya bashi da k'arfin bud'e baki yayi magana ma, ganin haka ya sanya Yah Aliyu d'ago shi yana rik'e dashi suka k'arasa d'akin Suhaima. Da sauri Aunty Aliyah take buga k'ofar d'akin Suhaima tana kiran sunan ta, a firgice Suhaima ta duro daga saman gado tare da bud'e k'ofar nata. Kafin tayi magana Yah Aliyu ya shiga da Sabeer cikin d'akin tare da zaunar dashi ya juyo ya kalli Suhaima wadda sai rarraba ido take hanaklin ta atashe yace "Kiyi maza ki cire mishi kayan jikin shi ki canja mishi bari naje na samo mishi magani, Aliyah kije ki dafa mishi tea da kayan k'amshi ki dafa da lemon tsami a ciki " Yana gama fad'in haka ya wuce ya tafi da sauri yayi da Aunty Aliyah ma ta wuce zuwa kitchen da sauri duk da kuwa ana yin yayyafi, Suhaima kasa motsi tayi saboda ganin Yah Aliyu da kanshi ya kawo Sabeer har da cewa na cire mishi kayan jikin shi, ganin halin da Sabeer yake ciki ne ya sanya ta kok'arin cire mishi kayan shi dakyar ta iya cire mishi saboda gaba d'aya babu k'arfi ajikin shi balle ya mik'e tsaye, bayan ta gama cire mishi ta duba kayan nashi ta ciro dogon wandon jeans ta sanya mishi sai dai babu wata riga ta sanyi aciki wanda mutum zai sanya ya ji d'umi. Ahaka ta zura mishi T-shirt mai dogon hannu sannan ta lullu6e shi da blanket idanun shi har zuwa lokacin a lumshe yana jan numfashi dakyar gashi jikin shi yayi zafi sosai, jik'akk'un kayan ta d'iba ta fitar dasu waje ta ajiye sannan ta dawo dakin ta zauna kusa da Sabeer tare da rik'e mishi hannu tana kallon shi hawaye na fita a idanun ta........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/23, 9:24 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 108-109* Da sauri ta mik'e tsaye tare da matsawa can nesa da Sabeer saboda jin ana kok'arin shigowa d'akin, Yah Aliyu ne ya shigo hannun shi rik'e da

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});