Chapter 69
Chapter 69
rufe laptop d'in ya kallo ta cikin murmishi sannan ya sunkuya yace "Baby taho na gama " Cikin sauri ta taso tare da d'anewa bayan shi, yatsina fuska yayi sannan yace "Wash! Bayana Baby kin k'ara nauyi zaki karya min baya " Turo baki tayi cikin shagwa6a tace "Ni.... Ni Allah ban wani k'ara nauyi ba kai ne ka dad'a zama babba " "A'a Baby fad'i gaskiya " "Toh bakai ne kake d'ura min abinci ba da yawa " Dariya yayi yana cewa "a haba Baby fad'i gaskiya dai " Hannun ta ta sanya tare da d'an mintsinin shi a damtsen hannun shi, wata 'yar k'ara ya saki "Laaa Baby kika mintsine ne, aikuwa sai na rama " Kafin ta ankara ya kwantar da ita akan carpet ya bi jikinta ya kwanta gaba d'aya sai ya saukar mata da nauyin shi , dakyar take jan numfashi tace "Wayyo don Allah ka d'aga ni dear " Yana dariya yace "Nak'i wayon yarinya sai na rama ko kuma yau da dare na hanaki bacci kin yarda " Da sauri ta d'aga kanta dariya ya sake yi sannan ya d'aga ta, hannun ta ta zube su kan carpet tana sauke numfashi, janyo ta yayi kan k'afafun shi tare da had'e bakin su waje d'aya wani salo na daban yake nuna mata itama babu 6ata lokaci take mayar mishi da martani. Sunyi nisa cikin wannan yanayin ne yaji wayar shi na k'ara, ba don yaso ba ya d'auki wayar yana jan tsaki don an katse mishi jin dad'in shi. "Hello Yaya na haihu " "What! Da gaske kike? " Cewar Sabeer yana tambayar Jiddah, cikin dariya tace "Allah Yaya da gaske nake an samu Baby girl" "Masha Allah na tayaki murna 'yar kanwata Allah ya raya " "Yaya ka fad'awa Suhaima ita na fara kira wayan ba'a d'auka ba" "Okay babu damuwa " "Toh yaushe zaka kawo min Besty tun da kuka yi aure bata zo ba fah?" "Jiddah surutu huh, yanzu kina buk'atar hutu ne kije ki huta zan kawo ta ne" Cikin shagwa6a tace "Yaya ka kawo min ita gobe don Allah idan zaka fita office " "Okay naji " Nan ya kashe wayar tashi, kallon Suhaima yayi wadda take kallon shi tun fara wayar shi ya ce "Albishirin ki Baby " Matsowa kusa dashi tayi sosai tace "Goro fari k'al dear " "Mene tukuici na idan na fad'a " D'an dariya tayi kad'an sannan tace "Ka fad'i duk abin da kake so zanyi maka " "Jiddah ta haihu ansamu Baby girl " Wani ihun murna ta saki tare da rungume shi tana dariyar farinciki kallonta yake duk tabi ta birkitashi ta kashe mishi jiki. "Dear ka tashi mu tafi ganin Baby please " "No Baby yanzu mangarib ta kusa ki bari sai gobe don gaskiya yanzu kin gama birkita ni tashi mu tafi ciki before mangarib tayi " Sanin halin shi ya sanya ta biye mishi suka tafi, sai da suka sha soyayyar su tukunna sukayi wanka tare da yin alwala ya tafi masjid ita kuma ta shige bedroom nata don yin sallah, bayan ta idar da sallahr ne ta samu damar kiran Jiddah don yi mata barka kafin tazo sunsha hirarar su sosai kafin suyi sallama da juna. _*Washe gari*_ Tun asuba da tayi sallah take faman gyaran aikin gidan bayan ta gama ta had'a breakfast sannan ta jera saman dining table, bedroom ta wuce ta cire kayanta ta d'aura towel ta shige bathroom don yin wanka, acan Sabeer ya same ta suka sha soyayya then sukayi wanka suka fito shirya junan su suka yi, yana sanye cikin wata blue na suits sai necktie black da black shoes yayi matuk'ar yin kyau. Yayin da Suhaima kuma ta shirya cikin wani swiss lace brown da touch na red d'in flower's tayi kyau sosai, fita suka yi zuwa dinning table agurguje suka yi breakfast, sannan ta wuce d'aki ta d'auko mayafi babba red colour ta yafa sai flat shoes da handbag redred in colour perfumes masu sanyin k'amshi ta sanya sannan ta fito. "Wow! Baby na kinyi kyau sosai " Cewar Sabeer yana rungume ta ajikin shi. "Nagode Dear kai ma kayi min kyau " Kissing ya bata goshi sannan ya rik'o hannun ta suka fito zuwa compound. Suna zaune bayan mota driver nayin tuk'i suka fita daga gidan hanyar gidan Jiddah suka nufa. "Baby nima yaushe zaki haifa mana Baby? " Ya fad'a yana shafa flat tummy d'in ta, kunya ce ta kama Suhaima dakyar ta iyacewa "Duk lokacin da Allah ya bani sai na haifa mana " "Haba Baby ina kula fah dake tun daga kika zo gidan nan baki yi period ba yau 3 Month's har da 'yan kwanaki da auren mu, ai nasan da ajiyata anan shiru kawai nayi miki " D'an tunani ta fad'a yi tabbas rabon ta da yin period tun lokacin sauran 2 week's bikin su amman koda tana gida sai tayi 2 months bata ga period yazo mata shiyasa idan ta tashi yi take fama da menstruation pain mai tsananin zafi. "Kinyi shiru Baby ko ba haka bane? " Tana shirin yin magana suka shiga gidan Jiddah don haka sai ta mayar da bakin ta tayi shiru. Tare suka fito daga motar hannun su sark'e cikin na junan su, suna kok'arin shiga parlour ne aka bud'e kofa tare da fitowa, sai da gaban Suhaima yayi mugun fad'uwa ganin Mumyn Sabeer ce wadda ta jima da zuwa duba Jiddah da Babyn ta, idanun ta akan hannayen Sabeer da Suhaima fuskar ta sam babu alamar fara'a. Jikin Suhaima na rawa take kok'arin kwace hannun ta amman Sabeer ya rik'e k'am yak'i ya cikata don haka kawai ta tsugunna tana gaida Mumy, bata amsa ba sai kau da kai da tayi. Sakin hannun Suhaima yayi bugging d'in Mumy tare da bata peck a cheek nata, cikin sanyin jiki Suhaima ta mik'e daga tsugunnan da tayi. Kallon ta Mumy take yi sosai wanda ya sanya Suhaima k'ara rikicewa gabanta banda fad'uwa babu abin da yake, wani irin fad'uwa gaban Mumy yayi masifar yi a lokaci d'aya da ta hango wasu canji atattare da Suhaima wanda tasan tabbas sai mace mai ciki ne take canjawa irin haka abin ka da likita, wani mugun gumi taji ya karyo mata tun daga saman gashin kanta zuwa fuskarta da jikinta. Zame hannun ta tayi daga na Sabeer ta fara tafiya zuwa wajen motar ta hankalin ta a masifar tashe duk yanda zata yi sai tayi don ganin ba'a haifi wannan cikin ba, don bazata ta6a had'a zuri'a da 'yar kauye ba abin da bazai ta6a yiwuwa ba dole tasan yanda zatayi cikin ya fita idan yaso duk lokacin da ta samu ciki sai tana zubar dashi. Tasan halin Sabeer yanda yake masifar son yara dole ya rabu da ita daga lokacin da ya gane ita take zubar mishi da ciki duk da son da yake mata kuwa a wannan lokacin ne zata aura mishi yarinyar da take son ya aura wannan dabarar ta shine kawai zai kawo k'arshen zaman Sabeer da Suhaima, wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki tare da shiga mota tabar gidan zuciyar ta fes take jin ta gani take kamar ma Sabeer ya rabu da matsiyaciyar yarinyar nan..........
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104