Chapter 13
Chapter 13
ankara ba taga sun d'auki wajen 25 minutes a wurin ai kuwa da sauri ta kallo inda Sabeer yake zaune yana danna wayar shi gefen shi kuma Fadilah ce ke faman yi mishi surutu tana wani karairaya da iyayi ita a dole so take ta birge Sabeer, k'arasa wa Mumy tayi wajen ta dafa kafad'ar shi cikin k'aramin sautin magana tace "Son kazo ka yanka cake " Daman gaba d'aya a takure yake da yabar wajen don haka ya mik'e tsaye Mumy taja hannun shi har zuwa inda aka ajiye cake, knife Mumy ta bashi suka rik'e tare tukunna suka yanka nan Mumy ta bashi a baki shima ya bata, nan kuma kowa ya fara bashi kyautar gift nashi da zai bashi Sabeer sai faman jan tsaki da 6ata rai yake ganin har ya k'ara 5 minute akan 30 minutes d'in da zai yi, sai kallon Mumy yake yana son sun had'a ido dashi yayi mata magana, amman tak'i yarda su had'a ido kwata kwata saboda tasan halin d'an nata gashi duk wanda zai bashi gift idan baisan shi ba sai ya tsaya gabatar da kanshi. D'ago kan da zaiyi ya kalli Mumy akayi sa'a ita ma ta kallo inda yake da ido yayi mata alamar ya gaji gashi time d'in da ya d'auka ya wuce yana nuna mata agogon hannun shi gashi kuma 'yammatan da suka bi suka dame shi Sabeer dai yaga ta kanshi tamkar zai fashe da kuka haka yake ji duk Mummy ce ta ja mishi, Mumy tamkar ta fashe da dariya haka taji lokacin da ta ga Sabeer yanda ya koma amman sai ta danne dariyar ta tare da marairaice mishi fuska da ya d'an yi hak'uri na d'an wasu minutes, daga nan kuma aka fara ciye ciyen abubuwan ci dana sha, a wannan lokacin Sabeer ya zame ya tafi abin shi gaba d'aya a wani gala6aice yake kanshi har ya fara ciwo. Shiga mota yayi driver yaja shi sai gida, yana parking ya fito daga motar ya nufi side d'in su, kai tsaye bedroom d'in shi ya nufa yana shiga ya fara cire kayan jikin shi yana wurgi dashi sai da ya cire komai sai iya dogon wandon shi ya bari tukunna ya shige toilet, shower ya sakarwa kanshi na tsayin 2 minute kafin ya fad'a cikin bath tub ya fara wanka bayan ya gama ne ya d'aura alwalar sallahr ishha tukunna ya fito daga toilet. Wata white jallabiya ya sanya cikin nutsuwa ya gabatar da sallahr ishha bayan ya idar ne bai wani tsaya yin wata addu'a ba ya mik'e tsaye tare da cire jallabiyar ya kwanta daga shi sai three-quarter a jikin shi kwanciya yayi saman bed yana mai runtse idanun shi hannun shi d'aya saman goshin shi ya dafe, a hankali ya wani bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi daman ya gaji sosai. Mumy koda ta duba bata ga Sabeer ba tasan ya tafi, don haka nan ta sallami friends nata da wad'anda suka zo, kowa ya tafi gida tukunna ta shiga mota zata rufe murfin motar taji an rik'e, cikin d'an mamaki ta jiyo don ganin wane, had'a ido tayi da Fadilah fuskar Mumy cike da mamaki tace "Fadilah daman baki tafi gida ba " Cikin marairaice fuska Fadilah tace "ni Mumy bin ki zanyi fah acan zan kwana " Murmishi kawai Mumy ta saki don tasan dalilin kwanan Fadilah a gidan nata, cikin kulawa Mumy tace "alright dgter shigo mu tafi " Fadilah jiki na rawa ta shige cikin motar ta zauna burin ta kawai a yanzu da tunanin ta shine yanda zata shawo kan Sabeer ya amince da ita ya aure ta ko suna hutawa da junan su, don ita Fadilah bata da ra'ayin aure a zuciyar ta sai da taga Sabeer, ita kawai 'yar aji dad'in rayuwa ce bata tunanin makomarta anan gaba matsayin ta na d'iya mace. Hira suke tsakanin Mumy da Fadilah har suka k'arasa gida driver yana yin parking suka fito a motar direct part d'in Mumy suka nufa, suna shiga cikin parlourn babu kowa amman a gyare yake tsaf dashi sai tashin k'amshin turaren wuta yake da air freshener, upstairs suka nufa nan Mumy ta nunawa Fadilah room d'in da zatayi amfani dashi, amman sai Fadilah tace "Mumy ina ne bedroom na Sabeer naje mu yi hira kinsan har yanzu yak'i sake min sosai " Murmishi Mumy ta saki tare da nuna mata wani d'an corridor da hannunta tace "kin ga bedroom d'in shi can nasan yanzu yana ciki " tana gama fad'in haka Mumy ta nufi hanyar da zai kai ta bedroom nata ta bar Fadilah anan. Wani dad'i ne ya kama Fadilah cikin rawar jiki ta juya zata nufi room d'in Sabeer sai ta kalli kayan jikin ta wani d'an Tunani tayi kad'an kafin ta juya kuma da sauri ta koma bedroom d'in da Mumy ta nuna mata. Da sauri ta shige bathroom ta fara yin wanka bata dad'e ba ta fito babu batun yin alwala balle sallah, cikin sauri ta gyara jikin ta sannan ta shirya cikin wata white d'in sleeping dress tsayin ta iyakar shi cinya mai siririn hannu sannan ta d'ora 'yar saman ta wadda take har k'asa sai dai gaban ta a bud'e yake sai 'yan igiyoyin rigar da ake d'aure wa, perfumes ta sanya masu matuk'ar k'amshi da tada hankali sannan ta fito zuwa room d'in Sabeer. Tura kofar room d'in tayi ta shiga tare da rufe kofar ta jingina bayan ta a jikin ta, shak'ar k'amshin turaren Sabeer tayi tare da lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta bud'e idanun ta a hankali ta zube su akan Sabeer da yake baccin shi hankali kwance, wani shu'umin murmishi ta saki tana mai k'arasa wa wajen bed d'in, hankalin ta kwance ta cire 'yar saman rigar ta tukunna ta haye kan bed d'in. Kallon Sabeer take tamkar wata kura taga nama, sai wani had'iyar yawu take musamman da takai eyes nata kan kirjin Sabeer a hankali ta d'ora hannun ta inda take Buk'atar ajiye shi a cikin jikin Sabeer ta fara shafawa cikin kwarewa da gwanin ta.... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey (saNaz) Where are U Bilkisu Bk this page is for U autan Exclusive thanks for luv and care, Allah ya bar zumunci thanks once again dear 👄 PAGE 19-20 Sabeer yana tsaka da yin sleeping nashi mai dad'i yaji tsikar jikin shi yana tashi, wani yanayi yana shigar shi a hankali mara fasaltuwa ya rasa tantanci shin mafarki ne ko ido biyu yake jin haka. Fitinannen k'amshin Fadilah ne ya cika kofofin hancin shi har takai da ya fara kok'arin bud'e idon shi, gaba d'aya Sabeer ya gama tsorota don yana tunanin ko aljanna ce ta zo mishi tun da a lokacin ya tabbatar da ba mafarki ba ne kuma yasan wace mace ce zata zo mishi a wannan daren idan ba aljanna ba, har jiki shi ya fara d'an rawa don Sabeer akwai tsoro dakyar ya iya yunk'urin bud'e idon shi ya zuba su akan Fadilah da take kok'arin kissing lips nashi, don ta had'a fuskar ta da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104