Chapter 93
Chapter 93
da ya dunga yi musu, sam bazai ta6a yafe mishi akan abubuwan da ya aikata a gare su, don haka ya bud'e baki cikin rawar murya yace "Baba ni da k'anwata bama buk'atar sake ganin ka kamar yanda mu ma ka gudu ka barmu don haka kawai ka kyale mu zamu k'arasa rayuwar mu babu uba " Yana gama fad'in haka ya juya zai koma gida, yayin da Baba yake faman kuka yana furta "Ku yafe min Aliyu hakk'in ku ne yake bibiyata ku yafe min ko na ji dad'in rayuwata " Amman ina Aliyu bai saurare shi ba ya wuce gida tare da rufe k'ofar ya jingina bayan shi kan k'ofar duk dauriya irinta Aliyu sai da ya kasa rik'e kukan shi ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi har yanzu yana jin amon murya Baban nashi yana furta su yafe mishi. "Lafiya kake kuka? " Yaji saukar muryar Sabeer kusa dashi yana mai rik'e shi hankalin shi a tashe don a iya sanin shi Aliyu jarumi ne ba kamar shi ba dole akwai wani babban abu da ya d'aga mishi hankali. Girgiza kanshi yake kawai ya kasa magana, suna cikin haka Suhaima da Aunty Aliyah suka shigo zauren jin kamar sautin kuka, hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba ganin yanda Aliyu yake kuka, nan take suka fara kukan ita Aliyah zuciyar ta ce ta bata Baban ta ko Babaar tane wani daga cikin su ya rasu. Da sauri Suhaima ta k'arasa wajen Yah Aliyu ta shige jikin shi tana kuka tace "Yaya me.... me ya faru kake kuka? " Ganin yanda hankalin su ne ya tashi sosai ya sanya shi bud'e baki dakyar cikin muryar kuka a shak'e yace "Suhaima Bab..... Baban mu ne ya dawo " Awani firgice Suhaima ta d'ago kanta ta kalli Yah Aliyu cikin tsananin tashin hankali da rud'ani kafin ta rushe da kuka tace "Yaya don Allah kace ya tafi ina tsoran shi wallahi kada ya kashe mu kamar yanda ya fad'a, Yaya zai dawo yana dukan mu da zagin mu ina tsoran shi..... " Ganin abin nata ya had'ar mata da tsoro, firgici da kuma sumbatu har ta rasa me zata ce ya sanya Sabeer ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yana bubbuga bayan ta alamar rarrashi yayin da Aliyah ma ta k'arasa wajen mijinta tana bashi baki da ya bud'e k'ofar duk da kuwa da irin kallon da yake wurgata, gashi sai wani sauke huci yake kamar wani tsohon zaki. Suna tsaka da haka ne suka ji ana bubbuga k'ofar cikin sauri Aliyah ta sanya hannu zata bud'e k'ofar amman kafin ta bud'e Aliyu ya sakar mata wata harara bashiri ta hakura kawai ta zubawa mijin nata ido yanda ya rikid'a ya koma mata wani daban kamar ba Aliyun ta ba. "Aliyu, Aliyah, Suhaima, Sabeer ku bud'e k'ofar nan nasan kuna jin na" Suka jiyo amon muryar Baba Adamu yana kwalla musu kira, Sabeer ne yayi kok'arin janye Suhaima daga jikin shi ya samu ya bud'e k'ofar, yana bud'e wa Baba Adamu da Babaa Lantana suka shigo bayan su kuma mahaifin su Aliyu ne yana dogara sanda. Suna had'a ido da Suhaima ta wani saki k'ara mai rud'ewa wanda sauran kad'an ta wuntsila tsabar firgita da tsoran shi da sauri Sabeer ya taro ta ya rik'e ta k'am itama rik'eshi tashi sosai suka shige cikin gidan jikinta na 6ari don masifar tsoron shi take. Daman tabarmar da suka karya akanta tana nan a shimfid'e zama suka yi dukkanin su ban da Suhaima da ta gudu d'aki tana kuka sai Yah Aliyu da yake tsaye ya kasa zama. Tashi Sabeer yayi ya nufi d'akin ya tarar da Suhaima tana kwance a ruf da ciki tana kuka sosai, cikin sanyin jiki Sabeer ya k'arasa inda take ya zauna tare da janyota jikin shi ya d'orata saman k'afafun shi share mata hawayen face nata yake yi cikin sanyin murya yake rarrashin ta, dakyar ya samu tayi shiru sannan ya d'auko ruwa ya bata tasha, kad'an ta iya sha sannan yace "Baby nah ki nutsu mu je, amman na rok'e ki kada kiyi kuka ji yanda idanun ki da fuskar ki suka yi ja gashi sun kumbura saboda kukan da kika yi" Cikin sanyin jiki ta d'aga kanta alamar toh daga haka yaja hannunta suka fito zuwa tsakar gidan inda suke zaune jugum jugum kamar gidan makoki sautin kukan Baban su Suhaima ne kawai yake tashi, damk'e hannun Sabeer Suhaima tayi jikinta ya fara rawa don masifar tsoron Mahaifin ta take kallonta Sabeer yayi cikin zuciyar shi yana tunanin mai Mahaifin su yayi musu da har Suhaima take jin tsoron shi haka gashi ya karanto tsananin tsanar shi kan fuskar Aliyu da Suhaima. Gefe suka samu suka zauna sannan Baba Adamu yayi gyaran murya tare da cewa "Alhamdullilah dukkan godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da ya bamu aron rai har zuwa wannan lokacin da ya sanya ni ganin wai Umaru ne ya dawo gida" Baba Adamu ya k'arasa maganar tashi cikin tsananin mamaki da jimamin yanayin da suka ganshi aciki, cikin sanyin murya da tsantsar nadama Baban su Aliyu yace "Bani da bakin kare kaina a wajen ku don hak'ik'a na cika azzalumi mara imani kuma butulu a wajen iyalina, nayi nadama dana sani mara adadi nasan na cika mara tausayi wajen mata ta Fatima da yarana Aliyu da Suhaima, bansan ta inda zan fara neman gafarar ku ba ku tausaya min duk wani jin dad'i na rayuwa bana jin shi kuma nasan duk hakk'in ku ne ku yafe min 'ya'ya n........ " Bai k'arasa fad'in maganar ba saboda wani kuka da ya kubce mishi na nadama, duk wajen shiru akayi ana sauraren shi sai da ya tsayar da kukan dakyar yace "Ina Fatima ku kaini inda take na nemi yafiyar ta don Allah, Aliyu Suhaima ku yafe min ba don ni ba don girman Allah " Baba Adamu ne yace "Umaru sai dai kayi hak'uri amman Allah yayi wa Fatima rasuwa tun washegarin da ka tafi cikin ma dake jikinta shima ya rasu " Neman mik'ewa yake amman jikin shi babu k'arfi ya k'asa tashi sai kawai ya fashe da kuka yana cewa "Na shiga uku yanzu ya zanyi da d'unbin tarin hakk'in Fatima da yake kaina me yasa ma na tafi na barku Fatima ki yafe min " Babaa Lantana tana zubar da hawaye tace "Umaru ka godewa Allah kafin Fatima ta rasu ta yafe maka duk abin da kayi mata" Kallon Babaa Lantana yayi tare da kura mata ido kamar yau ya fara ganin ta yace "Da gaske kike Fatima ta yafe min? " "Tabbas Umman mu ta yafe maka don ita ba macuciya bace kuma ba azzaluma bace ta kasance mai hak'uri da yafe wa mutanen da suka zalunce ta komai girman laifin da suka yi mata " Cewar Aliyu kenan a fusace, matsowa kusa dashi yayi kan ya sanya hannun shi yana kok'arin rik'e Aliyu da sauri Aliyu yayi baya yana girgiza mishi kai tare da wurga mishi wani kallo yace "Kada ka sake ka ta6a ni " "Ka yafe min d'ana 'yata ki yafe ni " Ya k'arasa maganar yana kallon Suhaima kauda kanta tayi daga kallon shi sai dai zuciyar ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104