Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 49

Chapter 49

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,183 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amince ba don yaso ba sai don baya k'aunar 6acin ran d'an lelen shi, don haka ya kirawo 'ya'yanshi ya shaida musu gobe kowa ya tashi cikin shirin tafiya don zuwa neman wa Sabeer aure nan take suka amince da hakan. Sabeer ba k'aramin farinciki yayi ba da jin sun amince da abin da yake so, da dare Daddy yake sanarwa da Mummy yanda suka tsara shi da 'yan uwan shi ko uffan Mumy bata ce ba k'arshe sai juya mishi baya tayi ranta a k'untace batason Suhaima bazata ta6a son yarinyar da ta fito daga k'auye ba kuma 'yar talakawa ta had'a zuri'a da ita dole ta sami mafita ta tarwatsa auren kafin lokaci ya k'ure mata. *** *** *** Duk wasu shirye shirye sun kammala shi na saukar bak'in su, anyi musu lafiyayyen girki sannan Yah Aliyu ya siyo musu drinks na kwali da faro, d'akin da Sabeer ya zauna nan suka tsaftace shi aka sanya mishi turaren wuta aka shimfid'a tabarmi don nan zasu sauki bak'in su. Bayan Suhaima ta k'arasa gyaran gidan taje tayi wanka ta shirya cikin wani maroon less d'inkin riga da skirt sunyi mata kyau sannan ta zuba hijab agurguje ta fice daga gidan don tana kunyar su zo su sameta, ban da wani irin nishad'i da take ji a cikin zuciyar na daban a yau d'in nan gashi tana son ganin kyakkyawar fuskar Sabeer. Tana shiga gidan Babaa Lantana da sallama a bakin ta suna had'a ido da Babaa Lantana ta sanya dariya tare da cewa "Oh amarya Suhaima ai na d'auka bazaki bar gidan ma zama zaki yi da na ji ki shiru " Akunyace tayi 'yar dariya tare da zama a gefen ta tana cewa "Haba Babaa kinsan bazan iya zama ina jin kunya ne " "Ai na d'auka ku 'yan zamani babu wannan kunyar a wajen ku ashe da akwai masu ita " "Uhmmm" Kawai Suhaima tace kafin ta d'ora da cewa "Ni daga zuwa kin isheni da surutu ko ruwa baki ban balle ki kawo min abin dad'in da Baba ya kawo miki " "Lallai gidan bakon ki ne ko yau kika ta6a zuwa ai kinsan hanyar wajen ajiye ruwan" "Tabbb d'an tsohon nan naki yana kok'ari nasan shima idan ya dawo gida ko ruwan sha bakya kawo mishi " 'Yar hararar wasa Babaa Lantana tayi wa Suhaima kafim tace "Ku yanzu mai kuka iyama a yiwa miji hidima, wata ma miji ya dawo daga aiki ko sannu da zuwa babu balle aje batun kawo mishi ruwa mai sanyi ya jik'a mak'ogaran shi, wata ma ko kallon inda yake baza tayi ba balle yasa ran ayi mishi magana duk wata kulawar miji da hidimar shi ba'a fiye sauke mishi ba sai afkin kwalliya kamar ta aljanu da kyalakyalen da basu zu amfane su ba, wata ma ba don mijin nata zata yi kwalliya ba sai don zata fita anguwa gasu nan da yawa muna gani kuma muna jin labari, idan kika ga wata awaje ma fes da ita idan kika je gidan watak'il ko ruwan gidan baza ki iya sha ba sannan....." "Kaiii Babaa Lantana daga tsokana zaki d'auko dogon sharhi haka kamar wata ma'aikaciyar gidan redio sai zuba kike " Cewar Suhaima kenan bayan ta katse Babaa Lantana daga maganar da take. D'an hararar ta tayi kafin tace "Yo ai gaskiya nake fad'a da kin barni na cigaba sai ki d'auki abubuwa masu amfani ke da zaki tafi birni ga mijin ki kyakkyawa kamar balarabe don nasan baza ya rasa mata masu rububin son shi ba, don yanzu mun zo wani irin zamani da sam wasu matan basu da alkunya sai kaga mace har mace amman ta zubar da k'imar ta tana furta wa namiji so babu kunya wannan abin yana ban takaici " "Allah ya kyauta " Abin da Suhaima tace kenan tana jin wani abu yana mata tuk'uk'i cikin zuciyar ta da taji Babaa Lantana tace yanzu haka da akwai wasu matan da suke son Sabeer wad'anda suka fita kyau, wayewa da ilimi na boko tunda ita iyakar ta secondary kawai. "Yanzu me kika shirya mishi wanda zai ci idan yazo? " D'an yatsina fuska Suhaima tayi tare da cewa "Tabbb ni ban wani shirya mishi komai ba sai abubuwan da aka tanadarwa bak'in" Kama baki Babaa Lantana tayi sannan tace "Allah ya shirye ki Suhaima yanzu baki d'an yi mishi abu na musamman ba shi d'aya haka ake tar6ar saurayin" Cikin yanayin shagwa6a tace "Toh ni me zanyi mishi kawai yaci wannan na gaji tun safe nake aiki wallahi " "Ke tafi can tsaya sanyin jiki na kwace miki shi " Dariya Suhaima tayi kawai nan Babaa Lantana ta tashi ta fara kiciniyar aiki. "Babaa me zaki yi ne haka? " D'an hararar ta tayi kafin tace "Tsaya ki gani yarinya kiga yanda ake tar6ar bak'o " D'an ta6e baki Suhaima tayi tare da kwanciya tana ganin yanda Babaa Lantana take zirga zirga k'arshe ma fita tayi daga gidan, tayi mintuna goma da fita sai ga ta da kaji biyu yankakku ta cigaba da aikinta bata k'ara bi takan Suhaima ba. Phone nata ta d'auka ta bud'e data da yake tayi downloading what's app da Instagram sai fb da yake taga yanda Jiddah take charting shi yasa batasha wahala wajen iyawa ba, message's ne suka fara shigowa duk da iya Jiddah da Sabeer ne kawai take what's app dasu sai wani group na kitchen da na novels sai na make up wanda Jiddah ta sanya ta. Kan number d'in Jiddah ta shiga nan taga ta turo wani video tare a tsokanar ta amarya, bud'e videon tayi bayan ya gama bud'e wa sai ta fara kallo tun tana murmishi har ya sanya ta fara tuntsira dariya ganin irin shagwa6ar da Sabeer yake yiwa su Daddy sai kace wani d'an yayen yaro k'arami dariya tayi sosai har da hawaye, Babaa Lantana kuwa sakin baki tayi tana kallonta kafin kuma ta girgiza kanta tana cewa "Allah ya shirya " Ta wuce ta cigaba da aikinta. Bayan ta gama dariyar ta fad'a dogon tunani daman haka Sabeer yake duk da tasan daga yanayin shi zai yi shagwa6a bata zaci shagwa6ar zata yi haka wani murmishi kawai take saki wanda ita kadai tasan ma'anar shi. Wajen misalin karfe 2 na rana su Daddy suka k'araso tare da jagorantar Sabeer don yana son ganin Babyn shi, suna k'araso wa sun samu kyakkyawar tar6a daga wajen Yaya Aliyu, Baba Adamu da kuma wasu amintattun dattijai biyu abokanan Baba Adamu kuma mak'obtan su, su Daddy sunyi mamakin ganin irin wajen da Sabeer yaje neman aure duk da haka kuma k'auyen ya basu sha'awa gashi sun ji dad'in tar6ar karamcin da aka yi musu. Bayan sun yi sallahr azahar ne don a hanya ta riske su, sai aka yi zaman gaisawa kafin kuma a fara cin abinci, a d'an kyamace suka fara kai abincin bakin su amman da suka ji irin dad'in d'and'anon shi tuni suka zage suka fara ci. Ganin sun fara cin abincin ce yasa Sabeer zamewa zuwa cikin gidan suka gaisa da Aunty Aliyah sannan ta fad'a mishi a inda Suhaima take wani murmishi ya saki kafin ya fita kuma. "Wannan 'yar tsohuwar me kike girkawa ne duk kin cika

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});