Chapter 67
Chapter 67
aiko ya mayar dasu gida tare da kyautar kud'i da ya basu mai yawa, Suhaima tasha kukan rabuwa dasu sosai, har jikin ta ya fara d'umi alamar zazza6i ne zai rufe ta kwanciya tayi tana kuka musamman idan ta tuna family d'in Sabeer basa sonta sai Jiddah da Daddyn Sabeer kawai, rarrashin ta Jiddah tayi sannan ta gyara mata gidan tsaf, sai da tayi wanka Jiddah tayi mata kwalliya ta shirya cikin wata gown tayi kamata sosai duk wani sura na jikin ta ya fito da yake irin roba d'in nan ce, ita ma Jiddah shawarwari ta bata sosai sannan tayi mata sallama ta tafi. Kwanciya tayi kan kujera ga jikinta babu dad'i, ga abin da 'yan uwan Sabeer suka yi musu ga kewar gida da kad'aicin ita kad'ai agida sai kawai ta fashe da kuka aikuwa nan da nan zazza6i da ciwon kai suka tarar mata lokaci d'aya........ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/5, 9:47 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 82-83* Tana nan kwance ta kudundune cikin bargo tana rawar zazza6i ga hawayen da suke zuba a idanunta, kanta ciwo yake mata kamar ya cire duk eye's nata sunyi ja sun kumbura, tana cikin wannan halin Sabeer ya shigo bedroom d'in nata. "Baby baccin yamma kike me yasa Jiddah bata zauna da ke ba har na dawo? " Yana maganar yana hawa kan bed d'in, yaye blanket d'in yayi tare da sanya hannun shi zai d'ago ta jikin shi, sai yaji zafi sosai jikinta da ya ta6a jikinta, a rikice da kallo ta sai yaga hawayen da take nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi har ya rasa me zaice yana tsoron kada ya kasance ya illata 'yar mutane, jiki na rawa ya d'auke ta ya shimfid'e ta saman k'afafun shi cikin tashin hankali yace "Baby nah me ya same ki, ina ne yake miki ciwo, me yasa baki kirawo ni kin fad'a min na kirawo doctor ya duba ki ba, tun yaushe wannan zazza6in ya rufe ki haka? " Muryar shi da d'an rawa yake maganar, kasa magana Suhaima tayi sai hawayen da suke zuba kawai ita abin da yake sake firgitata da tsorata ta kada 'yan uwan Sabeer su rabasu, tabbas ta kamu da son Sabeer wanda tasan idan suka rabu su ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba. "Kiyi min magana Baby please, ki daina kuka kin ga yanda idanun ki suka koma kuwa? " Ganin yanda ya d'aga hankalin shi ya sanya bud'e idanun ta dakyar ta kalle shi kafin tace "Zazza6i da ciwon kai ne kawai suke damu na" "Sai me kuma? " "Shikenan " D'an kallon ta yayi sannan yace "Baby fad'a min gaskiya abin da su Mumy suka yi muku shi ya sanya ki kuka ko? " Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi cikin mamakin a inda yasan me akayi musu, d'an girgiza kai na takaici yayi then yace "Nasan komai Baby, idan don wannan kike damuwa don Allah ki daina sanya shi cikin zuciyar ki kada ya janyo miki wani ciwon please, sannan zan d'auki mataki " "Amman dai bai ka......." Hannun shi ya sanya saman bakin ta ya rufe tare da cewa "Baby kiyi shiru kawai, bari na kirawo doctor ya duba min ke " Langa6e kanta tayi cikin yanayin shagwa6a tace "Ni Allah bana son allura ne da shan magani, zan warke a hakan kawai " "Ke kinma isa amarya fah kike taya ciwo yazo bazan d'auki matakin gaggawa akanshi ba sai yayi k'arfi ya hanani cin amarci nah tabbb yarinya naki wasa ne " Sanya face nata tayi cikin kirjin shi tana d'an murmishi don ya bata kunya, tana ji ya kirawo Doctor Aishat wadda take babbar likitace ta gynecologist ce tana aiki a hospital d'in Dr Faridah wato Mumy. Tsayin 5 minutes suka d'auka suna waya kafin ya kashe ya kalli Suhaima wadda ta lafe ajikin shi dauriya kawai take amman kanta ciwo yake sosai, shafa kanta yayi da hannun shi yana cewa "Sannu Baby nah yanzu Doctor Aishat zata zo ta duba ki " "Amman bazata yi min allura ba koh? " "Eh zance kada tayi miki tunda bakya so" D'aga kanta tayi kawai. "Baby jikin ki yayi zafi sosai sannu dama zan iya dawo da ciwon jikina dana dawo dashi" Hannunta ta d'ora saman face d'in shi tana shafa kwantaccen gashin sajen shi zuwa gefen bakin shi, lumshe eyes nashi yayi yana jin wani abu na ratsa shi kai hannun ta yayi bakin shi yayi kissing d'in tsakiyar tafin hannun ta, wanda daga shi har ita da bata jin dad'i sai suka ji wani yanayi atattare dasu. "Kada ka damu zan samu sauk'i insha Allah" "Amin Baby nah " Sunan zaune suka ji door bell kafin ya tashi kuma ya bud'e yaji phone nashi na ringing, bayan ya d'auka ne Doctor Aishat take mishi bayanin gata a k'ofar parlour a tsaye. "Baby bari naje na bud'e mata door ta k'araso " Yana gama fad'in hakan ya fita daga bedroom d'in, yana shigo da ita ya koma bedroom ya d'auko Suhaima cak kamar wata Baby ya kawo ta parlour duk kunya ta kama Suhaima sosai sai wani sunkuyar da kai take shi kuwa gogan ko ajikin shi sai ma kok'arin had'a ta da jikin shi yake, yayi da Suhaima sai nok'ewa take. "Yalla6ai me yake damun amaryar taka? " Cewar Dr Aishat kenan ganin idan ta cigaba da shiru Sabeer zai bata kunya yanzu. "Uhm Dr Aishat zazza6i ne ke damunta da ciwon kai sai kuma..... Uhmmm kin dai gane bansani ba ko taji ciwo? " Ya k'arasa fad'a yana shafa bayan kanshi, kamar k'asa ta tsage ta shige ciki haka Suhaima taji a lokacin, yayin da Dr Aishat ta maze don tasan tatsuniyar gizo bazata wuce k'ok'i ba. "Yalla6ai na fahimta inason zan duba don nagane ko taji ciwo " "Okay ba damuwa " Kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta sai bedroom ya kwantar da ita saman bed yayi da Dr Aishat take binsu a baya, ganin ya tsaya bashi da alamar fita ya sanya tace "Yalla6ai ka taimaka ka d'an bamu waje kad'an" Ba dan yaso ba ya fita daga bedroom d'in, bayan ya fita ne Doctor Aishat ta duba Suhaima nan ta gane bata ji wani ciwo sosai ba idan tana amfani da ruwan d'umi ma zuwa nan da kwanaki biyu zata warke, nan ta fara kok'arin yi mata allura aikuwa Suhaima ta sanya kuka tare da rirrik'e hannun Doctor d'in, sai Sabeer ta kirawo dakyar ta yarda akayi mata da rarrashi da lalla6a tare da sanya ta ajikin shi aka samu akayi guda biyu sannan ta bata magungunan da zata sha, kuma ta basu shawarwari na yanda Suhaima zata kula da kanta har ta samu sauk'i. Tukunna tayi musu sallama ta tafi bayan Sabeer ya taka mata zuwa bakin k'ofar fita parlour, kitchen ya wuce ya bud'e frige fresh milk ya d'auko tare da cup ya dawo d'akin lalla6a ta yayi har tasha maganin da fresh milk d'in babu dad'e wa bacci ya d'auke ta da yake har da maganin sanya bacci aciki. Yana zaune kusa da kanta ya rik'e hannun ta yana aikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104