Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,189 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

6angaren Suhaima itama kusan haka al'amarin suke sai dai ita ta cigaba da zuwa makarantar islamia kullum da yamma duk da tayi saukar alqur'an but tana sake fad'ad'a karantun ta da sauran litattafai, gashi bata yi rama kamar yanda Sabeer yayi ba don ita sosai tana kok'arin yakice shi cikin ranta ga kuma yanda Yah Aliyu suke tsananin bata kulawa duk da har yanzu son Sabeer na mak'ale cikin zuciyar ta, kullum idan tayi sallah tana addu'ar Allah ya toni asirin wanda yayi mata wannan sharrin, har a makaranta tana fad'a wa Malamai su sanya ana mata addu'a Allah ya yaye mata abin da yake damunta, sai dai kuma tana shan zund'e akauyen shi don tasha surutai don ma Yah Aliyu yayi musu kyakkyawa warning duk wanda ya k'ara nuna k'anwar shi da hannu yana aibatata sai ya sanya an d'aure shi da wannan warning da yayi musu suka samun sauk'in abun don Yah Aliyu yana da arzik'i duk ta sanadiyyar noma da kiwon da ya rik'e hannu bibbiyu. Ko zancen Sabeer ba'a k'ara tayar dashi ba agidan ba kowa yabar abun cikin zuciyar shi, duk wani kyautata wa Yah Aliyu yana kok'arin yiwa Suhaima duk abin jin dad'i yana kok'arin bata shi. Ya sanya anyi gyaran gidan sosai ya kashe kud'i sosai agyaran, ginin zamani na dai dai talaka mai rufin asiri ya sanya akayi mishi, sai gidan Baba Adamu suka koma akayi gyaran, inda Suhaima ta samu yalwataccen d'aki babba guda d'aya har da toilet aciki ya sanya akayi mata, sai kuma palo babba da akayi da 2 bedrooms wanda ya kasance na Aunty Aliyah da nashi sai kitchen da toilet a waje, amman filin tsakar gidan ya ragu sosai gashi ko'ina yasha sumunti dak'unan tiles ya sanya aciki, hatta furnitures sababbin ya sanya na dai dai mai rufin asiri ban da kayan kallon da ya had'a musu duk wannan abin Yah Aliyu yayi shine don kawai faranta ran Suhaima saboda yana ganin tayi rayuwa ta cikin kud'i tsayin wasu watanni ta fara sabawa da jin dad'i shine dalilin da ya sanya yayi haka duk da ya san bai kai rabin rabin kyan da gidanta na da yake dashi. Suhaima taji dad'in abin da Yayan nata yayi mata kawai don ganin farincikin ta, nuna mishi farincikin ta da yayi ne a lokacin ya sanya shi cikin jin dad'i da walwala wanda rabon da ya kasance cikin haka tun kafin Suhaima ta dawo gida, acikin wannan lokacin ne yaje ya zana wec and neco a wata secondary ta gaba da kauyen su don makarantar ma ta shiga cikin gari sosai, Suhaima ba k'aramin jin dad'i tayi ba na komawar da Yayanta makaranta da zai yi, shima yace mata ta kwantar da hankalin ta zai nema mata wata university d'in ta d'ora karatun ta sai ya cikawa mahaifiyar su burinta insha Allah na ganin sun samu ilimi sosai, saboda jin dad'in wannan maganar Yah Aliyu sai da Suhaima tayi kuka ashe daman zata cikawa kanta buri na ganin tayi karatu mai zurfi. Bayan exam d'in su Yah Aliyu ta fito ne dakyar da sod'in goshi ya samu gurbin karatu a jami'ar Buk da taimakon wani Alhaji da yake kai mishi kwai da kaji duk karshen wata gidan shi a birni, duk da kyan da takardun Yah Aliyu sukayi inda zai yi karatun Mass com inda Allah ya taimake shi ma yana da machine d'in hawa sai dai cacar kud'in mai da haka ya fara karatun shi cikin nasara da kwanciyar hankali. *********** _*AFTER 7 MONTHS*_ Sabeer ne na hango yana fitowa daga side d'in shi duk yayi wani tamkar ba Sabeer d'an gayu d'an kwalisa ba yana sanye cikin wani jallabiya milk mai yankakken hannu, tafiya yake kamar zai fad'i saboda yanda jikin babu kwari, bedroom d'in Mumy ya nufa yana son fad'a mata yana son shan coffee a dafa mishi. Har ya d'ora hannun shi kan handle d'in bud'e k'ofar zai murd'a yaji muryar Mumy tana cewa "Ga wannan kud'in na sallame ki daga yau ki koma kauyen ku yanzu yanzun nan don na fahimci sosai Daddyn Sabeer ke zargin ki kuma naga yana sanya miki ido a duk wani motsin ki nasan idan ya cigaba da hakan asirin mu ne yake daf da tonuwa, tunda kinyi nasarar raba wannan shegiyar matsiyaciyar da d'ana aikin ki ya gama, idan kuwa kika yi kok'arin tona min asiri kinsan zan iya sanya wa a kulle ki har karshen rayuwar ki ko a 6atar min da ke " Cikin rawar jiki mai aikin tace "Wallahi Hajia bazan ta6a tona miki asiri ba baza ki k'ara ganina ba ma har abada " Wani murmishi Dr Faridah ta saki kafin tace "Good da ya fiye miki alkhairi kuwa tashi maza ki had'a kayan ki ina son yau kibar gidan nan " "Toh toh Hajia yanzu ma kuwa " Ta kwashe kud'in mai yawa da Dr Faridah ta bata ta fito zata fita daga d'akin. Jikin Sabeer wanda ke rawa kamar mai yin rawar sanyi yayi hanzarin barin bakin k'ofar ya 6uya a wani corridor yana kallon ta ta wuce can part d'in su na masu aiki. Cikin zafin nama Sabeer ya bita a baya da sauri aikuwa yayi nasarar ritsata zata shiga d'akin, kallon Sabeer take tuni cikinta ya d'auki k'ara yana hautsinawa ganin yanda ya rikid'a kamar wani zaki. Bata ankara ba ya dalla mata mari har guda biyu zata yi ihu yayi saurin sanya hannun shi d'aya a baki alamar tayi shiru yana zare mata ido wad'anda suka yi ja jikin shi yana rawa sosai, ba shiri ta mayar da bakin nata ta rufe shi k'am har da d'ora hannu ta damk'e bakin nata. Kafin ta ankara wani fitsari mai zafi ya kubce mata yana tsiyaya sai faman matse kafa take da sauri Sabeer yaja baya kafin yana yarfe hannu tare da duba jikin shi ko ta 6ata shi, belt d'in jikin shi ya cire ya fara zuba mata, sai rawar disco take gashi ba damar yin ihu, gani yayi belt d'in kamar bata shigarta sai kawai ya yar da ita ya nufe ta ya shak'e mata kamar zai kashe ta tuni idanun ta sun firfito kamar zasu zazzago ga dakyar take sauke numfashin ta, Allah ne ya kawo Daddy hanyar wajen zai tafi garden yaji kakari awajen ya nufo wajen, ganin abin da d'an nashi yake kok'arin aikatawa da sauri ya nufi wajen dakyar ya 6am6are ta daga hannun shi sai wani huci yake fuskar nan tashi tayi ja. Yana sakin ta ta zube tana jan numfashi cikin rud'ewa Daddy yake girgiza Sabeer yana cewa "Son me kake shirin aikatawa ne me tayi maka iyeeeee? "" Cikin rawar murya Sabeer yake nuna ta da hannu yana cewa "Dad.... Daddy kace ta tayi magana ita... itace ta... take zubar wa da Suhaima ciki " "What! " Cewar Daddy da sauri. "Keee fad'a mana uban da ya sanya ki aikata hakan? " Cewar Daddy a fusace, cikin rawar murya tace "Don Allah kuyi hak'uri wallahi sanya ni akayi " "Wane ya sanya ki? " Murya na rawa da jiki na 6ari ta kasa magana sai da Sabeer ya daka mata wata razananniyar tsawa sannan ta bud'e baki dakyar tace "Wallahi Hajiya ce ta

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});