Chapter 45
Chapter 45
nayi miki da kike min kuka? " Cikin shagwa6a tace "Ba... Ba kai ne ba kace min baka sha kuma sai fushi kake dani bakason kula ni" Nan ta cigaba da kukan sosai ta bashi dariya hannun shi ya sanya ya rik'o hannunta don bazai jure ganin Suhaima a haka ba tana mishi kuka agaban shi, had'uwar hannun su waje d'aya shi ya saukar musu da wani yanayi a tsakanin su, sake runtse hannunta yayi da d'an k'arfi har sai da Suhaima tayi d'an k'ara kad'an. D'an sassauta rik'on yayi tare da cewa "Sorry! " Can k'asan mak'oshi yayi maganar. "Don Allah Sabeer kayi hak'uri bana jin dad'in baka min magana idan na duba ka " Girgiza kanshi yayi idanunshi cikin nata yace "Komai ya wuce Suhaima but zan tafi na bar muku gidan ku " D'an zaro ido tayi tare da cewa "Saboda me? " "Saboda wanda nazo domin ita bata sona gwara na hak'ura na koma inda na fito " D'an shiru tayi kafin ta d'ago kanta tace "Waya ce maka ba'a son ka " "Ke kika fad'a min " Ya k'arasa fad'i yana nunata da hannu. "Ni.... ni ba haka ba fah nake nufi ba kawai dai...... " Kasa k'arasa fad'a tayi don ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi...... Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/3, 9:27 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 63-64* Kasa k'arasa fad'in maganar tayi ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi, jin tayi shiru ne kuma ta sunkuyar da kai yasa shi sanya hannun shi ya d'ago face nata kafin yace "Uhm ina jin ki Baby kawai dai me ". Kasa jure kallon cikin idanun shi tayi sai ta lumshe idonta, kallon eye's lashes nata kawai yake cike da sha'awar kissing nasu sai dai ba yanzu yake son aikata hakan ba, d'an bud'e idonta tayi suka had'a eye's nasu kafin cikin d'an jin kunya Suhaima ta janye idanunta saboda ganin har idonshi ya fara canja launi tace "Ya wuce fah, yanzu ka hak'ura zaka sha kunun ? Kada kace min a'a please " Mak'e kafad'a yayi cikin shagwa6a da langa6e kai yace "Nak'i wayon sai kin fad'a min idan ba haka ba bazan sha ba yarinya " Sam Sabeer ya mance da duk wani shiri da yayi na share Suhaima, lallai ba k'aramin so yake mata ba, maganar tace ta katse mishi tunanin shi da yaji tana cewa "Haba Yaya nah na zuba maka " Dariya ta bashi sosai jin sunan da ta kirawo shi. "Yaya na koma yau kuma?, wannan ai sunan Babban Yaya ne ni miji ne ba Yaya ba " D'an rufe hannunta tayi da tafin hannunta sai ta d'an wara yatsun tana kallon shi ta haka kafin tace "Ai kaima kazama Yaya tunda Yayan Jiddah ne kuma ka girme ni" Tana gama fad'in haka ta janyo cup ta had'a mishi kunun ta ajiye mishi a gefen shi. "Koh! " Ya fad'in hakan yana kashe mata ido d'aya wani kunya ne ya sake kama Suhaima sai kawai ta mik'e zata gudu har zata fice daga d'akin taji yace "Suhaima har zuwa yaushe zaki furta min kina sona ne?, ki tausaya wa rayuwata Suhaima ki amshi soyayyata nayi alkawarin kasancewa dake cikin tsayin rayuwata bazan ta6a wulak'anta ki ba ko na guje miki ina yi miki wani so wanda baki bazai iya kwatanta miki ba " Cikin sanyin murya ya k'arasa fad'in haka fuskar shi d'auke da damuwa. Jikinta ne yayi sanyi sosai har ta gaza d'aga k'afanta sai kawai ta tsaya itama zuciyar ta yayi rauni sosai ga wani sabon son Sabeer da ya k'ara shiga cikin zuciyar ta, gashi yanda ya sadaukar da rayuwar shi don ya ceci nata lafiyar da rayuwar koda iya hakan tasan Sabeer ba k'aramin sonta yake ba don haka bazata bar wannan damar ta kubce mata, don haka batasan lokacin da bakin ta ya furta "Ina sonka Sabeer nima bazan iya rayuwa babu kai ba " Tana k'arasa fad'in haka ta juya da gudu tabar d'akin cikin jin kunya. Sabeer kuwa zaune yake kamar mutum mutumi saboda tsabar mamakin abin da ta furta mishi, anya ba mafarki yake ba kamar yanda ya saba tunanin shi da ne ya katse a lokacin da hannun shi ya dangwarar da cup d'in kunun gyadar har yayi nasarar zubo mishi a hannun shi wata 'yar k'ara ya saki kad'an, kafin kuma ya wuntsala kan katifar ya fara juyi na jin dad'i tabbas ba mafarkin da ya saba ba ne, da gaske ne Suhaima tace mishi tana son shi, sai da ya gama juyin murna sannan ya d'auki phone nashi num d'in Daddy ya lalubo ya kira. Daddy yana picking ko sallama Sabeer bai yi ba saboda tsabar zumud'i cikin murna yace "Daddy ka tayani murna Suhaima tace tana sona zata aure ni Daddy! " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Daddy fuskar shi cike da fara'a yace "Alhamdullilah congrats son, yaushe zaka dawo don muna kewar ka? " Yana dariya Sabeer yace "Very soon Daddy! " "Okay ya kamata ka dawo sai a fara maganar aure, uhm son za'a zama babba " "Kaiiii Dad! har da tsokana koh? " Ya fad'a cikin shagwa6a, dariya Daddy yayi kafin su cigaba da hira har zuwa lokacin da suka yi sallama, kwanciya Sabeer yayi ya lumshe idanun shi yana tuno lokacin da Suhaima take fad'a mishi tana son shi zata aure shi da wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi. Lokacin da Suhaima ta fito da gudu daga d'akin Sabeer sauran kad'an ta bige Aunty Aliya tayi saurin kaucewa tana cewa "Sorry Aunty nah" "Lafiyan ki kuwa Suhaima? " Fad'in Aliyah kenan. "Aunty lafiya qlau wallahi " tana gama fad'in haka ta wuce d'akin ta da sauri yayi da tabar Aliyah baki sake tana kallonta. Kan bed ta fad'a tana murginawa akai tana wani murmishi dagani murmishin farinciki ne take, jinta take sakayau kamar ta sauke wani babban abu akanta. "Ina son ka Sabeer, i luv U so much " Fad'in Suhaima a fili tana rufe fuskarta da hannunta kamar mai jin kunya wani na ganin ta. Tun daga wannan lokacin wata tsaftacacciyar soyayya ake gudanarwa tsakanin Sabeer da Suhaima, bawa junan su kulawa suke tare da tattalin juna, Yaya Aliyu, Aunty Aliya da su Babaa Lantana da Baba Adamu sun yi matuk'ar farinciki da kar6ar soyayyar Sabeer da Suhaima tayi. Yammaci ne irin na bayan sallahr la'asar Sabeer da Suhaima suna zaune a tsakar gidan saman wata babbar tabarma hira suke yi irin ta masoya. "Assalamu Alaikum " Suhaima ta tsinkayi sallama da muryar da bazata ta6a mance ta ba, don haka zumbur ta mik'e da sauri ta nufi k'ofa nan suka had'u da juna, wani ihun murna Suhaima ta saki tare da yin tsalle ta rungume Jiddah cikin tsananin farincikin ganin ta. Sai dai kuma jin abu ya tokare ta yasa ta sakinta tare da yin baya kad'an tana kallan d'an tudun da cikinta yayi, cikin dariya tace "Besty kaddai mun samu Baby " Dariya Jiddah tayi tare da kawo hannu ta d'an bugi kafad'ar Suhaima cikin k'asa k'asa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104